HAUSA NOVELRASHIN SO Complete Hausa Novel

RASHIN SO Complete Hausa Novel

Yah Basheer da Haseena suka kalli juna sannan suka kauda idanunsu daga barin kallon juna, yah Basheer yasa hannu cikin aljihunsa ya zaro takarda ya wurgawa Naja’atu ajiki cikin tsinkewar zuciya tace”takardar miye ka bani yah Basheer?”.

Kallon tsana da tsananin rashin so yakeyi yi mata cikin zafin rai yace mata”takardar saki ce na baki ki tashi yanzu ki ficemin daga cikin gida na sakeki saki uku har abada babuni babu ke! “.

Jin ya furta kalmar saki saida yasa Naja’atu ta zabura da k’arfi tareda k’amewa wuri guda hawaye masu zafi suka cigaba da sintiri afuskarta tsananin b’acin rai da tafasar zuciya suka bayyana k’arara afuskarta d’aci da k’ololon bak’in ciki sai yawo sukeyi cikin jinin jikinta bud’a baki tayi tace”nagode da irin sakayyar da kayimini Basheer tabbas ka nunamin halinku na zama, kuma inason ka sani komai daren dad’ewa sai hak’k’ina ya fita akanka domin baxan tab’a yafe maka akan cutar da rayuwata da kayi ba!”.

Yah Basheer yace”banason jin wata maganar banza ki ficemin daga cikin gida yanzun nan!”.

Naja’atu tayi murmushin takaici tace”zan fice daga cikin gidanka amma ya xama dole kayimin uzuri har a d’auke ruwa!”.

“bazanyi miki wani uzuri ba yanzu nake buk’ata ki barmin gidana!”.

“kayi hak’uri bazan iya fita cikin ruwan nan ba!”.
Basheer ya iso wurinta baiyi wata wata ba ya sunkuceta ya fitar da ita daga cikin d’akin, ya kaita cikin ruwan sama yanata dukanta ganin abinda Basheer ya aikata yasa Haseena taja hannunsu Rufaida ta fitar dasu waje takai su wurin mahaifiyarsu.

Suna fitar dasu waje bakin k’ofar gidan suka sakata suka kulle gidansu, juyawa kawai su Haseena sukayi suka koma d’akinsu suka lab’e domin kada ruwan sama ya jik’asu,su Naja’atu dake cikin ruwa yanata dukansu kamar bulala jawo su Rufaida tayi ta rungume ajikinta sai karkarwa da makarkatar sanyi sukeyi, cikin wata k’aramar baranda dake k’ofar gidan Basheer suka shige amma duk da hakan saida ruwan sama ya jik’a musu jiki sharkaf da ruwa rawa da makarkatar sanyi kawai suka cigaba dayi,alokacin ne Suhail ya fashe da rikitaccen kuka yace”Ummi sanyi nakeji kizo mu shiga cikin gidan Abba”.Hawaye suna kwaranya afuskar Naja’atu ta k’ara rungumeshi tace”yi hak’uri ka daina kuka sun kulle gidansu idan aka d’auke ruwan zamu tafi gidansu Baffa”.

Suhail yana kuka yace”sanyi nakeji sosai”.

Bargon dake lullub’e ajikinta ta lullub’awa Suhail ajiki tace “daina kuka d’ana komai na duniya yanada iyaka”.Itama Rufaida k’ara matsowa tayi ta shige cikin bargon sai ya zamana ya zamar musu kamar rumfa, an dad’e anata tsuga ruwa kamar ba za’a d’auke ruwan saman ba can aka d’auke ruwan cak gari ya waye yayi haske garau zad sha’awa da burgewa…

Suna zaune gari yayi haske wurare da ramuka duk suka cika da ruwa k’asa tayi chab’o babu k’yawon kallo, ganin an d’auke ruwan yasa Naja’atu ta yaye musu bargon dake lullub’e ajikinsu suna zaune saiga Salisu ya gifto saman mashin d’insa har zai wuce yayi ribas ya dawo baya, saboda ya hango Naja’atu cikin madubi yana isowa wurinta ya kalleta cikin tausayawa yace”Naja’atu lafiya na ganki waje cikin ruwan sama!?”.

Naja’atu tayi hucin zafin zazzab’i dak’yar tace”Basheer ne ya sakeni ya koroni daga cikin gidansa! “.Tana k’arasa maganarta hawayen bak’in ciki suka cigaba da gangarowa daga cikin idanunta.

Salisu yaji gabansa ya bada rasssss zuciyarsa tayi bak’ik’irin cikin damuwa yace”Ina lillahi wa inna ilaihirraji’un! Lallai kinga jarabawar rayuwa Naja’atu kiyi hak’uri kinji dukan tsanani yana tareda sauk’i”.

Ya k’ara da cewa”yanzu dai bari in samo miki keke napep ta kaiku gida”.

Naja’atu tace “to mun gode Allah ya k’ara bud’i”.Amin amin Naja’atu”.Kud’i ya zaro masu yawa daga aljihunsa ya bata tak’i amsa dak’yar ya lallasheta ta amsa, sannan ya tadda mashin d’insa ya nufi inda zai samo musu mai keke napep ya kaisu har gida………
[11/27, 1:59 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sis Najer’art*

_Free page._

*PAGE 21*

 

Yana wucewa bada jimawa ba saiga Salisu ya dawo da mai keke napep har gabansu Naja’atu dake tsungune cikin baranda,a idanunsu Salisu ya zaro kud’i d’ari biyar yaba mai keke napep domin yakaisu gidan Baffa, bayan ya gama biyansa ya umurcesu dasu shiga cikin napep d’in ya kaisu gida, kai tsaye ta mik’e taja hannun ‘ya’yanta suka shiga cikin napep d’in suka zazzauna saman kujera.
Suna zama mai napep ya tadda napep d’insa tareda saitata saman kwalta Salisu yana zaune saman mashin d’insa saida yaga b’acewar keke napep d’in sannan ya sauka saman mashin d’in yana zubar da kwallar tausayin rayuwar Naja’atu.
Direct gidansa ya shiga cikin yanayin damuwa da mutuwar jiki da sallama ya shiga cikin gidan, hango Saliha yayi tana wankin kayansu Rayyanu ganin mijinta ya dawo yasa ta mik’e tsaye tsam tabar wankin, wurinsa ta isa ta kallesa tana nazarinsa na tsawon lokaci hango damuwa da b’acin rai tayi kwance cikin idanunsa nan taji bataji dad’in yanayin da taga mijinta cikinsa ba, kujera ta d’auko ta bashi ya zauna sannan ta ciko ruwa masu sanyi akofi ta mik’a masa yasha yayi gyashi, zaunawa tayi gab dashi tayi kalar tausayi tace”wa nene ya b’atawa mijina rai shin baka bashi labarin yadda kakeda matsayi da muhimmanci azuciyata ba?”.
Salisu ya saukar da numfashi cikin jimami da damuwa yace”Saliha ayau naga abinda ya bani tausayi da sanyani zubar kwalla ko alabari ban tab’a jin wanda ya walak’anta rayuwar iyalinsa ba fiyeda Basheer! Bansan ko wace irin dakakkiyar zuciya ce dashi ba ace mutum bayada imani da tausayi ko kad’an arayuwarsa”.

Cikin tsinkewar zuciya Saliha ta firfito da idanunta awaje tace”mi Basheer d’in yayiwa su Naja’atu kuma!?”.

Jijjiga kansa yayi cikin zafi da rad’ad’in abinda ya gani da idanunsa yace”Basheer ya saki Naja’atu tareda yi mata korar kare kinsan Allah duk ruwan saman da akayita tsugawa duk ajikin Naja’atu da ‘ya’yanta ya k’are!”.
Gaban Saliha ya fad’i cikin mamaki tace”kardai kacemin cikin ruwan ya koreta!?”.
“k’warai kuwa cikin ruwan ya korota ya kulle gidansa”.
“ina lillahi wa inna ilaihirraji’un!! Alal hak’ik’a Naja’atu taga jarabawa da k’angin rayuwa wannan wace irin *RAYUWA CE* mara tabbas mai cikeda matuk’ar tashin hankali da bak’in cikin rayuwa!?Allah ubangiji ya juyawa Naja’atu da mafi alkhairi arayuwarta yasa taji dad’in rayuwarta nan gaba”.
“hmm Amin abin dai babu dad’in gani bale ji ubangiji ya bata miji nagari wanda zai share kukanta”.
Saliha ta duk’ar da kanta ak’asa hawayen tausayin aminiyarta sai shatata sukeyi afuskarta, ganin haka ne yasa Salisu ya matso kusa gareta yasa hannunsa ya rungumeta cikin jikinsa yace”ki daina kuka domin dukkan mai rai sai Allah ya jarabcesa Saliha abinda kawai zakiyi mata shine ki tayata da addu’ar samun sauk’i da sassauci arayuwarta, shi kad’ai ne abinda zakiyi mata tasan ke masoyiyarta ce”.
“zan dinga tayata da addu’ar samun sauk’i cikin lamurranta amma abin ne da tausayi Baban Rayyanu”.
“akwai tausayi kam gaskiya amma ya muka iya tunda komai rubutacce ne awurin ubangiji”.
“tabbas haka ne k’addara ta riga fata”.
Zugum sukayi suna jimami da tsananin tausayin rayuwar Naja’atu saboda ba k’arya taga *TASKU* da k’uncin rayuwa azamantakewar rayuwar aurenta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button