HAUSA NOVELRASHIN SO Complete Hausa Novel

RASHIN SO Complete Hausa Novel

__________________

Mai keke napep yana isa k’ofar gidan Baffa ya ajesu fitowa sukayi daga cikin napep d’in, suna fitowa mai napep d’in ya tadda napep d’insa yabar cikin unguwar, jan hannun ‘ya’yanta tayi suka fad’a cikin gidan ko sallama babu akan babu dad’in rai azuciyarsu suna isa tsakiyar gidan suka hango Anna tana sharar tutun awaki, jin tafiyar mutane yasa Anna ta d’ago idanunta da sauri suka fad’a akansu Naja’atu ganinsu yasa wani irin rikitaccen fad’uwar gaba ya ziryaceta zuciyarta ta tsinke, aje tsintsiyar dake hannunta tayi ak’asa ta nufo wurinsu Naja’atu da sukayi zazzaune saman tabarma sukayi shiru.
Tana isowa ta cire takalminta ta zauna gab da Naja’atu tace”Naja’atu mi yake faruwa na ganku kadaran majaran ayamutse kamar wad’anda aka koro!?”.
Hawayen dake mak’ale cikin idanunta suka zubo afuskar Naja’atu wani irin d’aci da tururin bak’in ciki ke yawo acikin ilahirin jikinta dak’yar ta bud’a baki tace”Anna yah Basheer ya sakeni!”.
Wani irin d’aci da k’ololon bak’in ciki ya shimfid’u afuskar Anna muryarta tana rawa tace”shi…Basheer…d’in… ne.. ya.. sake…ki…!? “.
Hawaye suna kwaranya afuskar Naja’atu ta girgiza kanta alamar eh mana, azuciyar Anna taji wani irin mahaukacin zafi ya gauraye sassan jikinta da k’wak’walwarta cikin kad’uwa da rad’ad’in ciwo tace”ina lillahi wa inna ilaihirraji’un!Amma Basheer ya cutar da rayuwarki mi kikayi masa ne ya sakeki!?”.
Naja’atu ta d’ago idanunta da sukayi jajir kamar gauta tarin bak’in ciki ne ya sark’eta ta dingayi kamar numfashinta zai d’auke, Anna ta tashi tsaye tana mata sannu dak’yar ta samu tarin ya tsagaita ta dainayi.
Bayan tarin ya lafa Anna ta d’ebo mata ruwa ta bata tasha,bayan tasha Anna ta zauna saman tabarma tace mata”ina saurarenki ki gayamin sanadiyar mutuwar aurenki!?”.
Naja’atu ta share hawayenta ta kawo labarin duk abinda ya faru ta sanarwa mahaifiyarta, tana gaya mata tana kuka cikin d’aci da rad’ad’in bak’in ciki aranta Anna sai lallashinta take tana bata magana,saida takai k’arshen labarinta taja bakinta tayi shiru.
Kwallar zallar takaici ne ya cika k’wayar idanun Anna taf hannunta ta sanya ta share cikin takaici da nadamar had’a aurenta da Basheer tace”ba komai Naja’atu duk zaluncin da Basheer yayi miki akwai Allah shi zaiyi miki sakayya tun anan duniya!Sannan ya yassuwa kare ya d’auka babu ke babu shi har abada koda saki d’aya yayi miki bazaki tab’a komawa gidansa ba!”.

Naja’atu ta share hawayenta tace”zan shiga cikin d’aki banida lafiya sosai!”.

Anna ta sanya hannu ta tab’a jikinta jaye hannunta tayi da sauri domin jikinta yayi raurau da tururin zazzab’i, cikin tausayawa da tsantsar damuwa ta kalleta tace”Ayyah Allah ya baki lafiya bari in kira yayanki Hamid yazo da likita yayi miki allura da magunguna”.
Naja’atu tana runtse idanunta alamar zazzab’in yana damunta sosai,Anna ta tashi tsaye ta d’auko pillow ta azawa Naja’atu saman kanta domin ta d’an kishingid’a saman pillow.

Sannan Anna ta tashi tsaye ta shige cikin d’akinta phone d’inta ta d’auko ta kira nombar yah Hamid, phone d’in tana shiga ta fara ringing d’id’id’id’i alamar wayar ta shiga tana shiga yah Hamid yayi receiving call d’inta yace”Assalamu Alaiki Anna”.
“Amin wa’alaikas salam Hamid ya iyalinka?”.
“lafiya k’alau Anna ya kuke?”.
“to lafiya k’alau ba lau ba! “.
Hamid yaji fad’uwar gaba ya ziryacesa zuciyarsa ta tsinke! Cikin tsinkewar zuciya yace”Anna mi yake faruwa!?”.
Anna tayi huci mai tattare da d’acin rai tace”kazo da likita yayiwa Naja’atu allura ta dawo daga gidan mijinta batada lafiya”.
Cikin tausayi da tsananin k’aunar k’anwarsa yace”subahanillah!Allah ya bata lafiya ganin nan zuwa da likitan”.

“OK ina jiranka kayi sauri”.

“to Anna karki damu muna nan zuwa yanzu yanzun nan da yardar Allah”.
“to Hamidu”.Tana kai k’arshen maganarta ta katse wayarta tana fitar da numfashin takaici da bak’in cikin rayuwa, kwallar zallar d’acin rai ne ya zubo afuskar Anna ta share aje wayar tayi saman gado, tana ajiyewa ta fito daga cikin d’akinta ta nufi wurin Naja’atu.

Tana fitowa ta iske Naja’atu tana kwance tana saukar da numfashi sannu sannu cikin yanayin rashin lafiya,su Rufaida kuwa suna zaune ga k’asa suna wasar guje guje cikin jin dad’i da walwala sosai, Anna ta shafa goshin Naja’atu tana tofa mata addu’a agoshi tace”kiyi hak’uri ki daure gasunan tafe kinji”.

Naja’atu ta gyad’a kanta alamar to amma har azuciyarta bata jin wani dad’i sosai,ba’a jima sosai ba saigasu yah Hamid yana gaba likita abokinsa yana biye abayansa da sallama suka shigo cikin gidan Anna ta amsa musu cikin sakin fuska,isowa sukayi har wurin da Naja’atu ke kwance tana hucin zafin zazzab’i dak’yar take bud’e idanunta,yah Hamid ya kalli Anna yace”ya jikin nata?”.

Anna ta marairaice fuskarta tace”jikinta dai ya game da zafi sosai Hamidu”.
“ai daga gani tana jin jiki gaskiya”.Juyawa yayi ya kalli abokinsa yace”Faisal matso kusa gareta kayi mata allura”.
Faisal yace”ina zuwa bari in saka maganin cikin syringe”.Magani da syringe ya zaro cikin k’aramar jikkarsa yana zarosu ya fasa kwalbar maganin tareda sanya bakin allura cikin kwalbar, zuk’e ruwan maganin yayi suka shige cikin syringe d’in sannan ya k’araso wurin Naja’atu, hannu ta mik’a masa ya dubi inda ya kamata ya soka mata allura runtse idanunta tayi tana cize baki alamar taji zafin allurar, yana gama yi mata allurar ya tashi tsaye sanya hannunsa yayi cikin jikkarsa ya ciro mata magungunan zazzab’i yaba Anna kallon yah Hamid yayi yace”zata samu lafiya da yardar Allah amma tana buk’atar kulawarku”.

Yah Hamid yace”zamu dinga bata kulawa Faisal”.

Faisal yayi murmushin dake bayyana asirin k’yawonsa yace”Allah ya tashi kafad’unta nizan wuce zuwa gidana”.
” Amin mun gode ka gaida matarka”.Inji Anna.
“zataji da yardar Allah”.
Faisal ya nufi hanyar fita daga cikin gidan yayinda yah Hamid ke biye abayansa suna isa waje yah Hamid ya dubesa yace”likita mun gode Allah ya k’ara d’aukaka”.Faisal yace”amin ni zan tafi sai gani na biyu”.
“to ba damuwa Allah ya kaika gida lafiya”.Faisal ya isa wurin motarsa dake parker a k’ofar gidan ya bud’e gaban motar ya shiga ya zauna, tadda motarsa yayi ya nufi hanyar zuwa hospital d’in da yake aiki yah Hamid yana tsaye sai can ya juya ya shiga cikin gidan yana sak’a da warwara azuciyarsa……..
[11/27, 3:25 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sis Najer’art*

“`Wannan littafi na siyarwa ne ga mai buk’ata ya turo kud’i 200 ta account number
6020308418 Keystone bank Mugira Musa, idan ka biya saika turo evidence of payment ta wannan nombar 08163650557“`.

_Ko katin MTN na 200 ta wannan nombar 08163650557_.

*PAGE 22*

Yah Hamid yana isowa wurin Anna ya zauna kusa gareta yana ajiyar zuciya yace”Anna wai ina mijin Naja’atu miye musabbabin dawowarta gidan nan ayau!?”.Anna ta kallesa da jajayen idanunta b’acin rai k’arara akan fuskarta tace”babu komai Hamidu kawai dai batada lafiya shiyasa tazo gida”.Hamid ya girgiza kansa yana cewa”haba Anna ki taimaka ki gayamin gaskiya karkiji komai nifa jikina ya bani akwai mummunan abinda ya faru da Naja’atu,sannan idan baki sanardani matsalarku ba waye kuke dashi da zaku gayawa matsalarku?”.
Anna ta duk’ar kanta k’asa tace”Basheer ne ya saketa ya korata cikin ruwan saman da akayita tsugawa yau”.Yah Hamid ya kalleta afirgice cikin kad’uwa cikin mamaki yace”ya saketa fa Anna!?”.
“eh mana ya saketa Hamidu batare da wani k’wakk’waran dalili ko hujja ba!”.
Hamid ya rik’e goshinsa cikin damuwa domin maganar ta soki k’ahon zuciyarsa tsantsar damuwa da bak’in ciki ne ya shimfid’u afuskarsa dak’yar ya iya furta kalmar cewa”ina lillahi wa inna ilaihirraji’un!Lallai Basheer ya tafka *BABBAN KUSKUREN* da har abada bazan tab’a daina nadamarsa ba yayi *SAKEN* da Naja’atu ta kufce masa arayuwa, babu damuwa duk abinda mutum yayi yana gani ga rabonsa”.
Anna ta bintsire baki tace”kaidai bari Hamidu lamarin babu dad’in saurare tabbas Naja’atu taga tasku da k’angin rayuwa!Ina mata fatar Allah ubangiji ya musanya mata da rayuwar farin ciki anan gaba”.
“Amin Anna nizan tafi kasuwa in siyo mata wani abu taci saboda kinsan mara lafiya sai an kula dashi”.
“haka ne gaskiya Allah yayi albarka”.
Yah Hamid yaja k’afafunsa ya fice daga cikin gidan da saurinsa.
____________________

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button