RASHIN SO Complete Hausa Novel

Kasuwa yah Hamid ya tafi ya siyo mata yoghurt da tsire cikin bak’ar leda, leda d’aya ya siyo lemu, abarba, ayaba, kankana, da dai sauransu kayan marmari.
Yana siyowa ya biya gidansa ya iske bilkisu zaune tana suyar awara cikin tukunya k’amshin awarar duk ya game gidan gaba d’aya, hango yah Hamid da tayi ne yasa ta tsame awarar daga cikin man gyad’a ta fad’ad’a murmushi afuskarta tace”a’a Baban Hassan har ka dawo ne daga gidansu Anna?”.
Yah Hamid ya k’araso wurinta yace”kedai bari daga kasuwa nake nazo ne in d’aukeki muje kiga yadda jikin Naja’atu yayi, ina fatar kin kammala suyar awara?”.
Bilkisu tace”eh na gama jikin nata yayi tsanani sosai ne?”.
“da sauk’i shiga cikin d’aki ki d’auko hijabinki mu wuce”.
“to Baban Hassan”.Inji Bilkisu.
Bilkisu ta d’auki kwanon awararta ta shige cikin d’akinta hijabinta ta sanya tareda feshe jikinta da turare, jawo k’ofar d’akin tayi ta kulle da padlock tana kullewa ta isa wurinsa tace”gani na shirya muje”.
Yah Hamid ya shiga gaba tana biye abayansa har suka fito bakin garka, wurin daya parker mashin d’insa ya sanya key ya kunna mashin d’in hawa ya farayi saman mashin d’in sannan Bilkisu tahau bayansa, ya tadda mashin d’insa suka nufi hanyar zuwa gidan Baffa.
**********************
Yah Hamid da Bilkisu sunje ganin jikin Naja’atu to taji sauk’i sosai sun dad’e agidan sannan daga baya suka wuce gidansu, Baffa Zakari daya dawo daga kasuwa ya samu labarin cewa yah Basheer ya saki Naja’atu yaji zafi da k’ololon bak’in ciki azuciyarsa idanunsa sunyi jajir b’acin rai da tsantsar damuwa suka bayyana k’arara afuskarsa, har kwallar tausayi saida ya zubar akan Naja’atu domin abin yaci masa rai tareda sanya zuciyarsa cikin k’unci da tsananin takaici babu yadda ya iya ne saboda abin k’addararren al’amari ne tun ranar gini ranar zane, amma har a k’ark’ashin zuciyarsa yayi nadamar had’a zuri’a da Basheer domin yaron baida mutunci baisan darajar d’an Adam ba.
Shi da kansa ya lallashi zuciyarsa tareda sanya dangana da juriya akan k’addarar data sami Naja’atu, ko afuskarsa bai nunawa Anna b’acin ransa ba saidai ya dangana hakan da *K’ADDARA CE* tana rubuce alittafin kowane irin mahaluki a cikin duniya!.Ya lallashi Anna tareda yi mata nuni da hak’uri da juriya akan lamarin rayuwar duniya.
Haka dai rayuwar ta cigaba da gudana cikin rashin walwala da kwanciyar hankali, saboda Naja’atu jikinta ya k’ara tashi sosai wanda asanadiyar haka saida yah Hamid yazo da mota aka kwasheta aka kwantar agadon asibiti, kallo d’aya zakayi mata ka gane tana cikin matsananciyar damuwa da tsananin rashin lafiya domin kuwa duk ta fice cikin kamanninta tayi bak’i ta rame, abinciken da likitoti sukayi sun gano ta kamu da cutar hawan jini da ciwon zuciya adalilin irin takurawa da bak’in cikin da yah Basheer yake k’unsa mata lokacin da tana gidansa.
Da doctor ya sanardasu Anna mummunan ciwon daya kama d’iyarsu saida suka zauce da rud’ewa, tsantsar damuwa da tsananin tashin hankali ne bayyane afuskokinsu saboda kowa yasan Basheer shine silar faruwar hakan duk dayake komai ya samu bawa muk’addari ne daga Allah, kuka Anna ta fashe dashi wiwiwi cikin asibitin kowa yana kallonta cikin tausayawa da tsantsar damuwa dak’yar yah Hamid ya lallasheta ya samu tayi shiru ta daina kuka, Bilkisu itama sai sharar kwallar tausayinta takeyi tana ajiyar zuciya kowanensu ka kalla fuskar nan amurtuk’e take kamar an gaya musu mutuwa Naja’atun zatayi ne, haka dai suka cigaba da zama asibiti suna jinyar Naja’atu wadda bata cikin hayyacinta batasan a inda take rayuwa ba.
*BAYAN WATA D’AYA*
Tuni aka sallamo Naja’atu daga asibiti likita ya rubuta mata magunguna atakarda wad’anda zata rik’a sha domin taji sauk’in jikinta, su yaya Hamid suka nemi hayar mota suka rankayo suka dawo gida cigaba da bata kulawa na musamman sukayi tareda gujewa duk abinda suka san zai iya sakata damuwa, suna matuk’ar k’ok’ari wurin ganin bata shiga cikin kad’aici ba ‘ya’yanta ma Baffa Zakari ya d’aukesu kamar ‘ya’yan daya haifa acikinsa ba jikokinsa ba.
Haka dai sauk’i ya dinga shiga da sannu sannu harta warke garau kamar bata tab’a yin wani ciwo ba, ganin ta samu lafiya yasa iyayenta suka samu natsuwa da kwanciyar hankali azuciyarsu cigaba sukayi da tafiyar da rayuwarsu yadda ya kamata cikin sauk’in lamari da rufin asirin Allah.
Agidan iyayen Basheer da sukaji hukuncin da d’ansu ya zartarwa Naja’atu kwata kwata basuji dad’i aransu ba, sunzo takanas ta kano da kansu sun bawa Baffa Zakari hak’urin abinda ya faru Baffa ya nuna musu babu komai duk abinda ya faru k’addara ce dama tun farko Allah ya riga ya k’addari ko Naja’atu ta auri Basheer sai sun rabu, haka dai sukayi magana ta mutunci da karamci atsakaninsu kowane ya fahimci d’an uwansa daga k’arshe sukayi musu sallama suka wuce gidansu suna yabon kirki da halayyar Baffa na k’warai.
Da suka koma gida Alhaji Tasi’u ya d’aga waya ya kira Basheer bayan wayar ta shiga suka gaisa suna gaisawa, alokacin ne yake sanar masa da yazo gida yana nemansa yah Basheer yace masa gashinan tafe tareda katse wayar, bai tsaya wani dogon nazari ba ya sanya tufafinsa sharp sharp ya nufi gidan mahaifinsa yana shiga ya taraddasu zaune suna zaman jiransa,gaishesu yayi babu wanda ya amsa alokacin ne Alhaji ya tambayesa dalilin dayasa ya saki Naja’atu?Basheer shiru yayi ya rasa abin fad’a saida Alhaji ya daka masa tsawa da hargowa! Sannan jikinsa ya dinga rawa alokacin ne ya bud’i baki yana wani kakkaucewa da kame kamen banza, Alhaji da hajiya ganin yah Basheer baida wata k’wakk’waran hujjar dazai gaya musu nan da nan suka rufeshi da fad’a ta inda suke shiga batanan suke fita, saida sukayi masa wankin babban bargo tass suka fed’eshi daga daga bindi har kan wutsiya, tsantsar takaicin fad’an da suka rufesa dashi yasa yah Basheer yaji gaba d’aya rayuwarsa ta b’ace duniyar ta fice masa arai ,tattaro dauriya yayi idanunsa sunyi jajir akan b’acin rai basu hak’uri yayi yana magiya akan yayi kuskure su yafe masa, cigaba da basu hak’uri yayi har ya samu suka sassauta zuciyarsu dak’yar suka yafe masa saboda babu yadda suka iya domin mai afkuwa ta riga ta afku kuma k’addara ta riga fata.
Ganin sun sauko daga fushin da sukeyi dashi alokacin ne Alhaji Tasi’u ya dubesa atsanake cikin ruwan sanyi yace”ba komai zaka iya tafiya tunda ka zartar da hukuncin dake cikin zuciyarka”.
Tashi tsaye yayi yace cikin sanyin murya “ku gafarceni Alhaji komai yake faruwa haka Allah ya k’addara”.
Hajiya Hannatu ta hararesa kamar idanunta zasu fad’o ak’asa tace”mun ji ya zaka iya tafiya duk abinda mutum dai yayi kansa yayiwa”.
“tabbas maganarki gaskiya ce Hannatu”.Cewar Alhaji Tasi’u.
Basheer yaja k’afafunsa ya fice daga cikin gidan yayinda yabarsu Alhaji Tasi’u suna mayarda zancen sakin da yayiwa Naja’atu.
Da tsakar dare misalin k’arfe goma dai-dai su Alhaji Tasi’u da Hannatu suna kwance saman gado suna barci sai minshari suke fitarwa alamun sunajin dad’in barcinsu, hajiya Hannatu harda k’ara gyara kwanciyarta tayi cikin gigin barci bata sani ba, kwatsam! Sai naga d’akin ya gauraye da bak’in hayak’i rawa da tanbal tanbal kawai yakeyi kamar zai kife cikin k’asa, wata irin fitinanniyar iska mai k’arfi ta bayyana daga k’ark’ashin k’asa huhuhuhu kawai kakejin ya game cikin d’akin gaba d’aya, d’akin ya cigaba girgiza da rawa na tsawon lokaci can naga siririn bak’in haske ya fito adunk’ule daga cikin bangon d’akin suu suu suu yana jujjuyawa cikin matuk’ar tsafi da gunguma akan sihiri.