HAUSA NOVELRASHIN SO Complete Hausa Novel

RASHIN SO Complete Hausa Novel

Bak’in siririn hasken yana gama jujjuyawa cikin matuk’ar tsafi da gunguma akan sihiri ya girgiza tareda rikid’a ya zamo jibgegen halitta mai matuk’ar muni da ban tsoro, girman halittar ya wuce tunaninku ko tsammaninku saboda akan fad’inta da girmanta harta kusa cinye fiyeda rabin filin d’akin, kammanin halittar idan mutum ya kalleta tabbas bazai k’ara tab’a iya numfashi adoron k’asa batare da ya mutu ba! Gashi ne lullub’e zaro zaro ajikinta sannan tanada tsini saman kanta mai kamar kibiya farantan hannaye da k’afafuwanta zago zago ne masu kamar mashi girman idonta d’aya yakai fad’in ball idanunta har canza colour sukeyi suna fitar da wuk’ak’e da bak’ar wuta, bakinta wargajeje gudan k’ato wanda zama guda zata iya tura giwa goma acikinsu ta lak’umesu batare da wata matsala ba, hannunta ta d’aga sama tana wasu sambatu masu ban tsoro can wani irin kore koren haske ya bayyana atafin hannunta, yana bayyana ta kalli hasken da k’wayar idonta da kanshi hasken ya tashi sama suuu suuuu suuu ya nufi kusa ga hajiya Hannatu dake kwance tana barci yana isa wurinta baiyi wata wata ba ya zurara cikin jikinta ya shige tsab, yana gama shigewa halittar ta kece da wata irin mahaukaciyar dariya wadda asanadiyar haka saida ya haifar da girgizar d’akin da tartsatsin wuta kaji fass fass fass yana tashi can ta tsagaita dariyarta cikin muryarta mara dad’in saurare tace”nazo d’aukar *FANSA* daga yanzu fansar zata fara !”.Hhhhhhhh d’akin ya gume da muguwar dariyarta wani irin siddabaru tayi saita b’ace b’at cikin bangon d’akin kamar babu abinda ya tab’a wanzuwa, tana b’acewa komai ya tsaya cak girgiza da hasken suka b’ace daga cikin d’akin………
[11/27, 3:25 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sis Najer’art*

*PAGE 23*

 

Washe gari da safe misalin k’arfe tara 9:00am na safe bayan hajiya Hannatu ta gyara bedroom da palournta tsab tayiwa Alhaji breaskfast yaci ya fita, ta fad’a bathroom tayi wanka fitowa tayi d’aure da towel ajikinta ta shafa mayukanta tana gama shafawa taji yanayin jikinta ya chanza gaba d’aya, dubawar da zatayi idanunta ya sauka akan wasu irin ramukan maruru rud’un rud’un manya, bata kawo komai cikin zuciyarta ba ta sanya atamfarta ash clour ta sanya ta koma parlour tana karkad’a k’afa tareda kallon tashar Aljazeera.
___________________

*BAYAN SATI D’AYA*

Marurun dake jikin hajiya Hannatu suka fara yi mata k’aik’ayi da ciwo sosai tun tana b’oyewa Alhaji Tasi’u tana nuna dauriya, harta gaji ta fito fili ta sanar masa batada lafiya sannu yayi mata tareda bata kud’i masu yawa yace taje asibiti likita ya dubata, yana bata kud’in ya fice daga cikin gidan ya nufi wurin sana’arsa yana fita hajiya Hannatu ta shirya ta nufi babbar asibiti mai zaman kanta, ta samu ganin likita yayi mata awo da gwaje-gwajen jini sannan ya rubuta mata magunguna atakarda ya bata ta biya kud’in gwaje-gwaje sannan ta fito daga cikin asibitin.
Direct chemist d’in dake gefen asibitin ta shiga ciki ta mik’a masa takarda, amsa yayi ya karanta abinda takardar ta k’unsa sannan ya dinga d’auko magungunan da suke arubuce yana bata, haka ya dingayi har ya kammala zaro magungunanta calculating d’in kud’in duka maganin yayi ya gaya mata, babu gardama ta ciro kud’i daga cikin handbag d’inta ta biyashi,tana biyansa ya sanya mata magungunan cikin leda mai d’auke da sunan shagon bata yayi ta amsa ta wuce daga cikin chemist d’in direct hanyar da zata samu keke napep ta nufi.

Naja’atu ta warke garau ganin ta samu lafiya ne yasa ta fara yin sana’arta na saida kayan miya, ganin tana samun riba sosai yasa ta siyo injimin markad’e ta fara nik’an kud’i, da fara nik’anta sai ubangiji ya bud’e musu falalar arzik’i kud’i masu kauri suka dinga shigo mata ta kowace sana’a, ya zamana gwargwado sunfi k’arfin komai agidan Baffa Zakari duk abinda suke ra’ayin ci shi sukeci, zamansu sukeyi cikin rufin asiri kuma yah Hamid kodayaushe cikin taimakawa iyayensa yakeyi, komai kawo musu yake na dangance kayan abinci irinsu wake, buhun shinkafa,gero,doya da sauran kayayyakin da ake sarrafa abinci kala kala.

Yah Basheer yana zaune saman kujerar dake fuskantar Haseena kallon k’auna yayi mata yace”babyna”.

Murmushi ta sakar masa tace”na’am darling”.
“filin dana siya watanni uku da suka wuce har an fara gini”.
Firfito da idanunta awaje tayi fuskarta d’auke da annuri tace”kayyy amma naji dad’i matuk’a ubangiji ya sanya alkhairi kace mun kusa shiga sabon gida kenan”.
“da yardar Allah bada dad’ewa ba nakeson mu koma sabon gida”.
“Allah ubangiji ya gwada mana lokacin lafiya gaskiyar zance nayi matuk’ar farin ciki da wannan maganar taka”.
“Amin babyna”.
Zancensu suka cigaba dayi har saida lokacin sallar la’asar tayi sannan yah Basheer ya mik’e zumbur ya shiga cikin toilet ya d’auro alwala, yana gama alwala ya nufi hanyar masallacin dake unguwarsu Haseena ta fad’a bathroom itama domin tayi wanka.
********************
Naja’atu tana nik’ar kayan miyar gidansu yayinda Anna take zaune wurin awakinta tana basu ruwa da dussa, saiga sallamar Saliha ta shigo cikin gidan hannunta rik’e dana d’iyarta Shamsiya tana isa tsakiyar gidan ta zauna saman tabarmar dake shimfid’e ak’asa, Naja’atu taga shigowarta dak’yar ta daure ta k’arasa nik’ar kayan miyan, tana gamawa ta kashe injimin nik’an tareda mik’ewa tsaye murmushi ta sakarwa Saliha daga inda take tsaye tace”a’aaaa kice munada manyan bak’i”.
Saliha tayi murmushi tace”bak’ya rabo da zolaya nice kuma bak’uwa?”.
“bak’uwata kike mana”.
“OK”.
Naja’atu ta isowa wurinta suka gaisa sannan ta shige cikin d’aki alokacin ne ta d’ebo ruwa aranda masu sanyi ta kawo agaban Saliha ta aje, juyawa zatayi nufin ta d’ebo mata abinci Saliha ta gano nufinta saboda haka da sauri ta katse mata hanzari tace”ina zakije ki barni kuma?”.
Naja’atu tace”abinci zan kawo miki Aminiyata”.
Saliha ta girgiza kanta alamar a’a tace”ki barshi kawai ruwan ya isa wallahi ak’oshe nake”.
Naja’atu ta dawo ta zauna kusa ga Saliha tace”to na dawo”.
Saliha tayi kalar tausayi sosai cikin yanayin rashin walwala tace”ashe Basheer sakinki yayi tareda yi miki walak’anci da k’ask’anci iri iri abin babu dad’in ji balantana gani, agaskiya Basheer bai k’yautawa rayuwarki ba ya cutardake”.
“hmmmm babu komai *RAYUWA CE* Aminiyata haka ubangiji ya k’addaro mini tun kafin nazo duniya, sannan rubutacce ne acikin kundin k’addararta babu makawa sai ya sameni!”.
Saliha ta jijjiga kanta alamar gamsuwa da maganarta tace”wannan maganartaki tabbas haka ne gaskiya komai ya faru dake k’addara ce”.

“wato Saliha munyi auren soyayya nida Basheer tun bansan miye duniya ba tun bansan dad’i ko d’acin soyayya ba,da akayi aurenmu ya nunamin k’auna da tsantsar *SOYAYYAR GASKIYA* kamar ya had’iyeni akan so bayason ganin b’acin raina ko damuwata, duk abinda nake ra’ayi da muradi shi yake k’ok’arin nemomin aduk inda yake zamanmu zama ne da amana da fahimtar juna shiyasa alokacin na chanza na k’ara k’yawo kamar ba ni ba, bansan rayuwar bak’in ciki da k’uncin rayuwa ba saida Haseena ta shigo cikin rayuwarmu ta hargitsa mana gida tareda tarwatsa farin cikinmu! Tsananin soyayyar da yakeyimin ta juye ta koma *RASHIN SO* zallar k’iyayya yake nunamin wadda saida na gwammace kid’a da karatu, to tunda Basheer yayi aure ban huta ba cin karo kawai nakeyi da abubuwa marasa dad’i tareda k’unsamin bak’in cikin rayuwa”.
Saliha ta nutsu tana saurarenta har takai k’arshen maganarta numfashi tayi mai tattare da d’acin rai da bak’in ciki arayuwa sannan tace”lallai kinga taskun rayuwa da jarabawa arayuwarki Naja’atu amma babu komai duk abinda mutum yayi zai girbi abinsa,sannan wata sakayyar tun anan duniya Allah ke zartar da ita!”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button