RASHIN SO Complete Hausa Novel
Haseena ta langwab’e kai tareda sanya hannunta cikin nasa tace”hak’uri zakayi tunda ta riga ta dawo darling”.
Basheer ya dubeta yace”haka zakice mini?”.
Haseena tace”idan bance maka kayi hak’uri ba so kake ince kaje ka saki matarka? Bayan kasan tun kafin in aureka nasha gaya maka bazan iya rainon ‘ya’yan kishiya ba ka kuma sani bawai don baka sani ba”.
Basheer yayi k’asa k’asa da murya don ganin yayi kamar ta hasala dashi cikin sanyin jiki yace mata”kiyi hak’uri babyna nasan da haka gaskiya amma ban sanardake wannan maganar ba domin in b’ata miki rai ba, sai dai domin Naja’atu tayi matuk’ar b’ata mini rai dad’ewar da tayi agidansu”.
Haseena ta chanza fuskarta zuwa yanayin walwala tace”ai nasan bakason b’acin raina ko kad’an darling saboda haka ka kwantar da hankalinka banyi fushi ba”.
Murmushin farin ciki yah Basheer yayi tareda marairaicewa kamar mace yace”har kinsa naji sanyi araina na ganin farin cikin zuciyata batayi fushi dani ba, domin fushinki gareki yana iya haifar mini da illah arayuwata”.
“banida hujjar yin fushi dakai mijina domin banida tamkarka afad’in duniyar nan, kuma kana bani tsantsar kulawa da nunamin *SOYAYYAR GASKIYA* wadda babu algussu acikinta”.
Hak’ik’a Basheer yaji dad’in kalamanta har cikin jini da sassan jikinsa wani irin shauk’in sonta da kibiyar k’aunarta ke yawo acikin ilahirin jikinsa babu abinda yakeso da muradi illa ya jishi gashi gata suna manne da juna.
Cikin murmushi yace”Hasee baby agaskiya banda abinda nakeso sama dake saboda kin iya tafiyar da rayuwata yadda ya kamata”.
Haseena tayi fari da idanunta cikin kissa tace”bakada damuwa muddin muna rayuwa acikin inwa d’aya mijina”.
“ashe zanyita jin dad’ina kenan?”.
“sosai ma kuwa darling”.
Hannunsu suna mak’ale da juna suka fara kissing d’in juna ta ko’ina ajikinsu yayinda sukayi nisa da fara kissing,Basheer yasa hannunsa yana mammatsa boobs d’inta cikin shauk’in buk’atuwa ita kuma sai langwab’ewa takeyi ajikinsa tana nishin dad’i kawai sai naga ya cire mata riga boobs d’inta suka bayyana afili, ai kuwa nan da nan ya k’ara rikicewa da rud’ewa akan bayyanar na fulaninta kan nipples d’inta ya sanya cikin bakinsa yana tsotsa, sai naga Haseena ta saki numfashi tana nishin dad’i hmhmhmhm hmhmhmhm hmhmhmhm kawai kakeji k’ara manna bakinsa kawai takeyi akan nonuwanta, sun jima suna yamutsa junansu ta ko’ina nishinsu kawai kakeji sannan suka fad’a cikin duniyar ma’aurata mai cikeda tarin ni’ima.
**********************
Naja’atu tana shiga cikin d’akinta ta banye zanen goyon Suhail ta zaunar dashi saman gado, Rufaida itama ta zauna kusaga Suhail direct Naja’atu ta shiga cikin bathroom ta had’a musu ruwan wanka masu d’umi Rufaida ta fara yiwa wanka sannan ta shiga da Suhail ta wanke masa jiki tsab ta nad’osa cikin zane domin kada yaji sanyi, wurin mirror ta nufa da Rufaida kayan kwalliya ta kwaso ta shafe mata jiki da mayuka sannan tayi mata kwalliya mai k’yau, ciro mata fitted gown tayi ta sanya mata sannan ta d’auko Suhail ta shafa masa mai tareda saka masa tufafinsa masu dama.
Tana kammala shirya Suhail ta shimfid’esa saman gado tace “Rufaida ki kulada Suhail kafin in fito da wanka”.
Rufaida ta shagwab’e fuskarta tace “to Ummi idan yayi kuka fa ya zanyi masa? “.
Naja’atu ta waigo ta kalleta tace”ki lallashesa har sai ya daina kuka”.Tana k’arashe maganarta ta fad’a cikin toilet ta fara wanka ta jima tana wanka daga k’arshe ta fito d’aure da d’aurin k’irji ,koda ta fito daga toilet ta iso cikin d’akin taga har Suhail yayi barci tuntuni yayinda Rufaida take zaune tana gadinsa, kallon Rufaida tayi alokacin da tayiwa kanta masauki asaman kujerun dake gefen gadonta tace”Rufaida har yayi barci ne?”.
Rufaida tace”eh tun d’azu yayi barci Ummi”.
Naja’atu ta jawo powder ta shafa afuskarta sannan ta mayarda kayan kwalliyarta a ma’ajinsu, wurin jikkar tufafinta ta nufa ta ciro doguwar rigarta atamfa ta saka ajikinta Rufaida sai kallon mahaifiyarta takeyi tana murmushinta mai k’yau da gani,bayan Naja’atu ta gama sanya tufafinta ta juyo ta kalli Rufaida tace”kinajin yunwa ne in dafa miki wani abu kici?”.
Rufaida ta langwab’e kanta cikin sagarci tace”banason cin komai sai fura”.
Naja’atu ta mik’e tsaye tace”bari inje bakin garka ko zan samu yaron dazai siyo miki”.
Rufaida ta kwanta shame shame saman gadon tace”zakima samu yaron aike Ummi”.
Naja’atu ta ciro kud’i cikin handbag d’inta ta nufi tsakiyar filin gidan tana tafiya sannu ahankali kanta noce ak’asa domin batason idanunta suyi tozali da abinda zai hana mata kwana, tana cikin tafiya taji taci karo da mutum taja ta tsaya turus d’agowar da zatayi idanunta suka fad’a cikin na Haseena dake rik’e da bucket ahannunta ta fito daga wanka, kowace daga cikinsu ta tsaya tana kallon ‘yar uwarta na mintuna kad’an Naja’atu ta fara jaye idanunta ta daina kallonta ta bud’i baki cikin sanyin murya tace”kiyi hak’uri na bangajeki bada sani ba”.
Haseena tayi murmushin da baikai zuci ba tareda yi mata wani irin kallo mai d’auke da tarin ma’anoni maganarta sannu ahankali tace”ni ya dace in baki hak’uri Ummin Suhail bake saboda haka kiyi hak’uri ina sauri ne in shiga d’aki in shafa manshafi na bangajeki ban sani ba”.
Murmushi Naja’atu ta sakar mata tace”babu komai ai Amarya”.
Haseena tace”toni zan shige cikin d’aki in shafa mai”.
“ba matsala ‘yar uwa”.
Haseena ta shige cikin d’akinta yayinda Naja’atu ta isa bakin k’ofar gidan tana lek’awa ko zata hango yaro ta aikesa ya siyo mata fura da nono, bata wani jima sosai da tsayuwa ba saiga wani yaro d’an mak’wabciyarta Saliha ya gifto kiransa Naja’atu tayi ta mik’a masa kud’i domin ya siyo mata fura d’in, yaron mai suna Rayyanu ya amshi kud’inta ya nufi hanyar zuwa kasuwa………
[11/15, 1:04 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????
*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sis Najer’art*
_Wannan littafi na siyarwa ne ga mai buk’ata ya turo kud’i 200 ta account number 6020308418,idan ka biya saika turo evidence of payment ta wannan number 08163650557._
_Ko katin 200 na MTN ta wannan nomba 08163650557._
*PAGE 3*
Rayyanu bai jima sosai ba ya dawo daga wurin aiken da Naja’atu tayi masa cikin gidan ya shiga har cikin d’akinta hannunsa rik’e da ledar fura, yayi sallama abakin k’ofar d’akin yayinda ya hangota zaune saman cushion ta kishigid’a tashi zaune tayi da murmushi afuskarta tace”Rayyanu har ka siyo furar?”.
Rayyanu yayi murmushi yace”eh na siyo”.
“k’araso cikin d’akin mana ka ajemin saman mirror”.
Rayyanu ya cire takalminsa abakin k’ofa ya shiga cikin d’akin ya aje mata ledar saman mirror, fita zaiyi daga cikin room d’in Naja’atu ta ciro hamshin ahandbag ta bashi yak’i amsa kallonsa tayi tace”ka amsa mana”.
Rayyanu ya girgiza kansa alamar a’a yace mata”kibar kud’inki Ummin Suhail ni don Allah na siyo miki”.
Naja’atu ta mayarda kud’inta cikin handbag tace”nagode Rayyanu ka gaidamin Saliha”.
“zataji idan naje gida zan sanar mata”.
Yana gama maganarsa yasa kai ya fice daga cikin d’akin yayinda Naja’atu ta koma ta zauna saman kujerarta, ruwa ta d’ebo aroba ta fara dama furar tana tsaka ga damawa saiga Basheer ya shigo cikin d’akin kai tsaye babu sallama, takun tafiyarsa Naja’atu ta gane shiyasa ta waigo tana kallonsa cikin mamakin shigo mata d’aki da yayi, saboda rabon da ya shigo cikin d’akinta tun lokacin da ya auri Haseena ya d’auke k’afafunsa daga shiga cikin d’akinta, nata hak’k’i dana Haseena duk ya had’e ya bawa matarsa Haseena, tun abin yana ci mata tuwo ak’warya har tazo ta saba da rashin adalcin da Basheer keyi atsakaninta da Haseena idanu ta kawo ta saka musu wad’anda basa ji basa gani, shi kuma ganin abinda yakeyi dai-dai ne shiyasa abin nashi ya zarce.
Yana shigowa ya isa wurinta ya dubeta yace”Naja’atu muryar wa nakeji kina magana dashi cikin d’akinki yanzu?”.
Naja’atu ta dubesa tace”kamar ya muryar wa kakeji?”.
Jan numfashi yayi yace”banason raini fa ya ina tambayarki kina tambayata!”.
“to idan kaji ina magana cikin d’akina saika tuhumeni”.
Basheer yaja tsoki mtsssss yace”kada ki d’auka ina sonki ne shiyasa nake tambayarki a’a bana sonki ko kad’an azuciyata,banaso ne ki dinga jawomin k’attin banza har gida shiyasa nayi miki magana domin baxan d’auki wannan sakarcin ba”.
“bana jawo k’atti cikin gidanka yah Basheer saboda niba mazinaciya bace! Rayyanu yaron Saliha ne na aikeshi akasuwa ya siyomin fura da nono to muryarsa ce kaji muna magana”.
Basheer yace”ai Rayyanu shida k’ato basuda wani banbamci saboda haka ki gayawa munafikin yaron nan kada ya kuskura ya sake shigomin cikin gidana, idan ba haka zanyi masa dukan tsiya saina barshi kwance!”.
“bazan iya gaya masa wannan maganar ba kaje da kanka ka gaya masa mana”.
“haka zaki fad’a?Zanyiwa yaron mutane shegen duka kuwa asanadinki kuma duk abinda ya sameshi ke kikaja masa”.
“babu ruwana idan ka jiwa yaron mutane ciwo kai za’a d’aure ba niba”.
“hardake za’a d’aure saboda bak’ya jin magana kullum anayi miki magana abu guda amma bak’ya ji, saboda kinason jamin zagi shine zaki ba Rayyanu kud’i ya siyo miki fura akasuwa”.
Naja’atu tace”babu b’ata suna da kana bani hak’k’ina na ciyarwa da hakan bai faru ba, amma tunda kayi aure ka daina d’aukar nauyinmu nida yarana to ya kakeson inyi so kake mu zauna da yunwa mu halaka!?”.
“bana baki hak’k’inki d’in jeki gayawa duk wanda zaki gayawa bak’ar munafuka! “.
Naja’atu jin yana kirata da munafuka dole taja bakinta ta tsuke bata sake cewa uffan ba, Basheer ganin bata sake kulashi ba yasa yaji haushi yace”ina miki magana kin k’yaleni”.
Naja’atu ta juyar da kanta gefe tareda aje furar ak’asa yah Basheer yana ganin ta aje robar furar, ya kawowa robar wawura da nufin ya kifar da furar Naja’atu dayake tana hankalce dashi ta suri robar furar ta ajeta gefenta tace”mi kake nufi nufinka so kake ka kifar mini da fura ko?”.
Basheer yace”k’warai da gaske naso in zubar da furar ak’asa inga ta tsiya! “.
“bakada sa’a ka k’ara gaba to wata k’ila ka samu sa’a agaba”.
Basheer yayi tsaye yana k’are mata kallo yayi shiru na tsawon lokaci ganin yayi bayada abinda zaiyi mata, dole yaja k’afafunsa ya fice daga cikin room d’inta yana fita daga cikin d’akin Naja’atu ta d’auki furar ta isa wurin da Rufaida ke kwance tana barci, kamar ta k’yaleta sai taga bazata iya barinta ta kwana da yunwa ba tayar da ita tayi zaune ta mik’a mata furar, amsa Rufaida tayi tasha rabin robar ta mik’awa Naja’atu sauran ta koma ta cigaba da yin barcinta.
Amsa Naja’atu tayi ta rufe robar da wani murfi fad’awa bathroom tayi ta watso ruwa masu sanyi domin taji dad’in barci, tana fitowa ta d’aura zanenta ta kawo k’aramar riga ta sanya addu’ar barci da sauran addu’o’i na neman tsari tayi ta kwanta jawo bargo tayi ta lullub’e jikinta ta rufe idanunta ta fara barci.