RASHIN SO Complete Hausa Novel
Naja’atu ta musk’uta tace”tabbas amana dangin guba ce kowa ya cita saita k’abe masa ciki”.
“Allah baya ban bashi akan duk wanda ya cutar da wani ranar sakayya tana zuwa”.
Anna dake cikin awaki ta fito daga cikin awakin ta iso wurinsu tace”a’aaaa yau Saliha ce agidanmu?”.
“nice Anna mun wuni lafiya ya hak’uri?”.
“lafiya k’alau Saliha ya maigidanki?”.
“k’alau yake”.
“ki mik’a sak’on gaisuwata garesa sannan kice masa mun gode da d’awainiya da taimakon da yakeyiwa Naja’atu lokacin da tana gidan wannan azzalumin mijinta mara tsoron Allah!”.
Saliha ta noce kanta a k’asa cikin kunya da tsananin tausayi tace”zan gaya masa karkiji komai Anna ai duk abinda mukayi mata yiwa kaine sannan addinmu ya nufemu da tausayi da taimakon wanda yake cikin wani hali”.
Anna ta gyad’a kanta alamar gamsuwa tace”alal hak’ik’a maganarki gaskiya ne ubangiji yasa ku gama da duniya lafiya”.
“Amin amin Anna”.
Anna tana k’arasa maganarta ta shige cikin d’akinta yayinda tabar Naja’atu da Saliha suka cigaba da firarsu cikin natsuwa da shak’uwa da k’aunar juna”.
*********************
Yah Hamid ya fito daga wanka ya shirya cikin shaddarsa blue tareda sanya takalmin fata da feshe jikinsa da performs masu k’amshi, Bilkisu sai k’ara gyara masa kwalliyarsa takeyi tana kod’ashi yayi k’yau kayan sun amshi jikinsa, shi kuma sai washe baki yakeyi yana jin dad’i sosai azuciyarsa, yana kammala shiryawa Bilkisu ta d’auko masa k’aramin mirror tace”kalli fuskarka kaga yadda kayi masifar k’yawo mijina”.
Murmushinsa mai k’yau yayi tareda kallon kansa cikin madubi yayi yace”eh gaskiya nayi matuk’ar k’yau duk da yake ni bak’i ne”.
“hmmm Baban Hassan ai bak’ar fata bata hana k’yawo saidai idan Allah bai hallaci mutun da k’yawon ba”.
“kuma fa haka ne”.
Kallonta yayi ya sake cewa”ni zan wuce zuwa gari saina dawo”.
“adawo lafiya”.
“Allah ya yarda”.
Yana kai k’arshen kalamansa yaja k’afafunsa ya fice daga cikin gidan yabar Bilkisu tana aikace-aikacenta.
Yah Hamid bai zarce ko’ina ba sai wurin gyaran mashin d’insa daya samu wata matsala, yana kai wurin mai gyara ya ajiye mashin d’insa tareda yin magana akan matsalar mashin d’in yakeda, maigyaran ya dubi mashin yaga ba wata doguwar matsala bace kud’in gyara ya gaya masa nan take ya zare ya biya kud’in, nuna masa yayi zai shiga kasuwa ya siyowani abu maigyaran ya jijjiga kansa alamar babu damuwa.
Yah Hamid ya fice daga cikin wurin yana tafiya sannu ahankali daidai zai shiga cikin kasuwar, saiga Basheer shima ya kawo kusa gareshi yana tafiya da k’afa suna kawowa gab da juna suka bangaji juna batare da sun ankara ba, d’agowar da zasuyi idanunsu ya fad’a cikin juna murtuk’e fuskarsa Basheer yayi cikin d’acin rai da tafasar zuciya yace”Hamid kai wane irin jakin makaho ne! Baka gani ne daka bangajeni !?”.
Hak’ik’a yah Hamid yaji zafi da zogin maganarsa tsantsar b’acin rai ne da tafasar zuciya kwance afuskarsa nunashi da yatsa yayi yace”karka k’ara zagina Basheer domin babban kuskuren da zakayi arayuwarka shine k’ara zagina! Tun mushaidar juna ka daina shiga sabgata”.
Basheer yace”idan na zageka mi zakayi d’an matsiyaci jikan talakawa!”.
Hamid yayi murmushin takaici yace”naji d’an masu kud’i jikan k’aruna bari in wuce inada abinyi”.
Basheer ya zaburo da k’arfi kamar zai daki Hamid cikin son fitina da tijara yace”bazan baka hanya ka wuce ba duk abinda zakayi kayi!”.Hamid bai sake cewa komai ba ya rab’e ta gefensa zai wuce kenan yah Basheer yasa hannu ya jawo masa bayan rigarsa ta yage b’arrrrr kamar ansa rezor an yaga, dak’yar Hamid ya samu ya juyo da baya yana fuskantarsa cikin zafin rai da haushi ya d’auke Basheer da gigitattun maruka guda biyu masu k’yau tass tass kawai kaji ya tashi, akan k’arfi da rad’ad’in marin saida yah Basheer yayi taga taga ya fad’i k’asa d’immmmm hannunsa ya bugi dutsi wani irin rikitaccen zafi da rad’ad’in marin ne ya ziyarci sassan jikinsa da zuciyarsa jinsa da ganinsa suka d’auke na wucin gadi akan marin ya gigita rayuwarsa, ya dad’e kwance a k’asa baya cikin hayyacinsa yah Hamid yayi tsaye k’yam yana hucin tsanar walak’anci da rainin wayo can Basheer ya dawo cikin hayyacinsa yace”Hamid ka mareni !?”.”An mareka ko zaka rama ne?”.Basheer ya girgiza kansa cikin tsananin bak’in ciki da b’acin rai yace”zan rama amma ba yanzu ba tabbas zakayi nadamar marina da kayi arayuwarka! “.Tsoki yah Hamid yaja yace”ashe k’aryar tak’amar iskanci kakeyi duk abinda zakayi ina jiraye dakai banza mahaukaci! “.Yana kai k’arshen kalamansa yaja k’afafunsa yayi cikin tsakiyar kasuwa yabar Basheer kwance ak’asa……….
[11/27, 3:25 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????
*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sis Najer’art*
*PAGE 24*
Hamid yana shigewa cikin kasuwa yah Basheer ya mik’e tsaye yana kakkab’e tufafinsa da k’asa, waige waige ya dingayi saboda kada Hamid ya iskeshi wurin nan ya sake marinsa, yana gama kakkab’e jikinsa yayi matuk’ar sauri yabar wurin domin wani irin masifar tsoron Hamid ne ya d’arsu azuciyarsa alokaci guda, inda ya parker mashin d’insa ya nufa yaje yahau saman mashin d’in yabar kusaga kasuwa saboda ya tabbatar da cewa Hamid zai iya halakashi idan baibi sannu ahankali ba saboda a d’azu yana hango tsanarsa da tsagwaron k’iyayya ak’wayar idanunsa, jikinsa yana rawar tsoro ya tadda mashin d’insa yabar wurin da masifaffen gudu harna tashin hankali.
___________________
Hajiya Hannatu suna cikin d’akinta itada Alhaji Tasi’u suna maganar marurun daya fito mata ajiki, rigarta ta d’aga ta nuna masa marurun tace”Alhaji nifa wannan marurun yana bani mamaki sosai ji yadda suke k’ara girma da yimin k’aik’ayi”.Alhaji Tasi’u yayi duba ga marurun yace”abin akwai mamaki wai mi kikaci har ya zamo sanadiyyar fitowarsu?”.
Hajiya Hannatu ta gyara rigarta tace”babu abinda naci tun ranar da mukayi kwana bayan mu gama cin soyen kazar daka kawo mana da dare”.Alhaji ya d’aga kansa sama alamar tunani can ya saukar da wani numfashi yace”ohhh na tuna ranar littinin ce dana siyo kaza yanzu dai abinda za’ayi tunda maganin asibiti baiyi ba, ki bari zanzo miki da malam Kallamu mai maganin gargajiya ya baki magani mu gani ko ubangiji zaisa adace”.
Hajiya Hannatu tace”ba matsala Alhaji sai yazo”.
“uhmmmm hajiya”.Cewar Alhaji Tasi’u.
**** ***** ***** *****
*BAYAN WATANNI UKU*
Marurun dake jikin hajiya Hannatu suka k’ara yawaita bayan Alhaji Tasi’u ya d’auko malam Kallamu mai maganin gargajiya ya bata magunguna na gargajiya, ta fara amfani dasu tunda dad’ewa amma ciwon yak’i ja da baya sai k’ara anzama yakeyi ciwo da tsananin k’aik’ayi ya saka mata ajiki, wani lokacin zakaji jikinta yayi matuk’ar zafi garau kamar mai ciwon zazzab’i ganin yadda hajiya Hannatu ta koma farat d’aya yasa hankalin Alhaji yayi k’ololuwar tashi sosai zuciyarsa ta tsinke! Akan haka ne ya kaita asibiti domin abinciki ko wane irin ciwo ne ke damunta an bata gado tayi kwanaki acan asibitin, yah Basheer shida kansa yake jinyarta saboda ba k’aramin so yakeyiwa mahaifiyarsa ba, duk abinda ake buk’ata shi yake nemowa ya kawo asibitin.
Haka dai ya cigaba da jinyar hajiya Hannatu har taji sauk’i sosai doctor ya sallamesu suka dawo gida, tun lokacin da hajiya ta kwanta saman gadon asibiti Haseena bata tab’a tako k’afarta koda wasa ba tazo taga ya jikinta ko tayo abinci ta kawowa hajiya Hannatu, babu ruwanta saboda ba mahaifiyarta bace ciwonta ko ajikinta bata nuna damuwa afili ba bale azuciyarta, suna dawowa gida Alhaji Tasi’u ya cigaba da bata kulawa tareda kwantar mata da hankali shima Basheer yana yawan zuwa wurinta akai akai domin yaga yadda ta k’arasa da jikinta.