HAUSA NOVELRASHIN SO Complete Hausa Novel

RASHIN SO Complete Hausa Novel

Zaune Basheer yake zaune yana lissafin kud’in dazai cigaba da aikin gina yayinda Haseena take zaune kusa kujerar dake fuskantarsa, sai kallonsa takeyi aranta tana k’ulla abubuwa cikin ranta wanda ita d’ai tasan abinda take shiryawa, kansa yana duk’e ak’asa yace”wallahi baby rashin lafiyar hajiya tana yawan tayarmin da hankali idan ciwonta ya tashi sai naga kamar baza tayi rai ba”.
Haseena ta bintsire baki alamar ko ajikinta tace”hak’uri zakayi ka dinga yi mata addu’ar samun sauk’i ai cuta ba mutuwa bace kowa kaga ya mutu to lokacinsa ne yayi”.

“maganarki gaskiya ce amma bakisan wani abin mamaki ba duk rashin lafiyar da takeyi har kwantar da ita asibiti anyi amma still doctors sun kasa gano ko mike damunta, Alhaji da kansa ya d’auko malam Kallamu mai maganin gargajiya ya dubata shima ya kasa gano abinda yake damunta, yadai bayar da magunguna dana sha dana wanka”.

Haseena tace”lallai kace abin babba ne ubangiji shi kad’ai yasan abinda yake damunta Allah ya bata lafiya”.

“Amin amin babyna”.
Cigaba da lissafe-lissafensa yakeyi alokacin ne Haseena ta tashi tsaye tsam ta shige cikin d’akinta, taga shiga ta sanya key abakin k’ofar d’akin phone d’inta ta d’auko tayi dialling nombar Nasir wayar tana shiga ya d’auka, bayan sun gaisa yace mata su had’u wani wuri akwai maganar da yakeson ya sanar da ita, nuna masa tayi babu damuwa gatanan tafe, sharp sharp ta sake chanza tufafinta lace ta sanya red colour sannan ta sanya gyalenta cikin handbag d’inta hijabinta ta d’auko ta sanya, fitowa tayi daga cikin d’akin yayinda ta iske yah Basheer ya kishingid’a saman kujera murmushi ta sakar masa tace”baby an kirani gidan k’anen Babana matarsa babu lafiya”.

Kallonta yayi yace”subahanillah!Yaushe aka kiraki baby Hasee Allah ubangiji ya bata lafiya”.

“amin ya rabbi yanzu aka kirani shine nake neman izninka inje in gano yadda jikin nata yake”.

Basheer ya girgiza kansa alamar gamsuwa yace”na baki iznin kije babu komai bari in samu abinda na baki”.
Sanya hannu yayi cikin aljihunsa ya zaro bandir d’in kud’i naira dubu ishirin ya mik’a mata yace”kiyi hak’uri da wannan ba yawa kinsan harakar gina gida akwai cin kud’i sosai “.

Haseena ta amsa cikin farin ciki tace”ba damuwa nagode sosai mijina Allah ubangiji ya k’ara bud’i”.
Tana rufe bakinta taja k’afafunta tayi tafiyarta tana girgiza k’ugu da karkad’a jikinta cikin salo, yayinda Basheer ya bita da kallo yana had’iyar miyau kamar tsohon k’warto ????.

Haseena tana fita ta tari keke napep ta kaita har inda Nasir yace su had’u, mai keke napep yana ajiyeta ta hango motar Nasir parker agefen hanya d’ari biyar ta zaro cikin handbag d’inta ta bashi,amsa yayi zai bata chanjinta ta d’aga masa hannu alamar ya barsu godiya yayi mata yana wak’e hak’ora nan ya tadda napep d’insa ya k’ara gaba.
Haseena ta nufi wurin motar Nasir da yake zaune cikin motarsa yana jiranta tafiya takeyi guda guda kamar batason taka k’asa, shi kuma ya tsura mata idanu ko k’iftawa ba yayi wani irin kibiyar sonta da k’aunarta sai fisgarsa sukeyi, idan kuma ya tuna tanada wani lusarin miji sai yaji wani irin tururin bak’in ciki da mashin tsagwaron kishi ya game masa sassan jikinsa da zuciyarsa, tattaro dauriya da hak’uri yayi ya sanya aransa k’amshin turarenta ne yayi masa iso domin harta k’araso cikin motarsa ta bud’e k’ofa ta shigo, tana zama idanunsu suka sark’e cikin na juna sun dad’e suna aikawa junansu zazzafan sak’onni ta cikin idanunsu can suka saukar da numfashi sannu ahankali Haseena tayi murmushin dake k’ayartar da fuskarta tace”Nas ka kiraki gani nazo inji dalilin kiran da kakeyimin?”.

Nasiru yace”Haseena kenan kwana biyu banji muryarki ba shiyasa nace bari in kiraki kizo in ganki ko rad’ad’i da zugin da zuciyata keyi zai ragu, ina masifar sonki da k’aunarki shiyasa na matsu baki kashe aurenki ba! Sai yaushe zamu kasance atareda juna kowane lokaci sai yaushe zan dinga jin d’umin jikinki akodayaushe!?”.
Jikin Haseena yayi matuk’ar sanyi idanunta suka cicciko da kwallar takaici kallonsa tayi cikin damuwa tace”nima ina jin rad’ad’in da kakeji azuciyarka ina sonka Nas nayi maka alk’awarin zan aureka, amma so nake sai burina ya cika na samu abinda nakeso!”.

Nasir ya ciro handkchief d’insa mai k’amshi cikin aljihunsa ya mik’a mata yace”karki kuskura ki zubarmin da tsadaddin hawayenki abanza, karki damu muddin ina numfashi adoron k’asa zan taimaka miki tareda jajircewa wurin ganin burinki ya cika nasan kina sona Haseena amma wannan wawan mijin naki ya nisantar dake daga gareni! “.

Haseena ta amshi handkchief d’in ta share hawayenta tace”bakada matsala indai akan Basheer ne bai isa ya datse mu’amalar dake tsakaninmu ba har abada”.

“bai isa kam domin sani ne kawai baiyi ba muna tare da juna har abada”.

Haseena ta jawo hannunsa ta d’aura saman boobs d’inta tace”tabbas haka yake”.
Ganin haka yasa Nasir ya had’e bakinsu wuri d’aya tareda rungumeta ajikinsa yana aika mata kisses da romance d’inta, itama ta dinga mayar masa martanin abinda yakeyi mata nishinsu kawai kakeji hmhmhmhm hmhmhmhm hmhmhmhm yana tashi cikin motar, suna yamutsa junansu cikin shauk’in buk’atuwa da salon soyayya nan naja k’afafuna nayi gaba domin kada in makauce.
___________________

Naja’atu ce tayi wanka ta sanya atamfarta light green da red sanya hijabinta tayi light green ta kawo turarenta ta feshe jikinta dashi, sannan ta fito daga cikin d’aki ta isko Anna zaune saman tabarma itadasu Rufaida sun kewayeta sunata damunta da surutu, sai kallonsu takeyi tana cewa “ku tashi ku tafi wasa kun dameni”.
Rufaida ta mak’e kafad’a alamar batayi tace”babu inda zamuje Anna muna kusa gareki”.
Anna ganin sunk’i tashi dole yasa ta tsuke bakinta Naja’atu tana fitowa ta duk’a har k’asa tace”Anna ni zan tafi sayayya kasuwa ko akwai abinda kike buk’ata?”.
Anna ta kalleta cikin tausayawa tace”eh ki d’an siyomin d’anyen naman miya idan chanji ya rage”.

“OK ba matsala zan siyo nina tafi saina dawo”.
“Allah ya dawo dake lafiya”.
“Amin Anna”.Tana k’arasa maganarta ta fice daga cikin gidan ta nufi hanyar zuwa waje, tana isa bakin k’ofar keke napep d’in ta gifto gaba gareta, tsayar dashi tayi ta shiga cikin keke napep d’in sukayi jinga bayan ta biyashi kud’insa ya tadda napep d’in suka nufi kasuwa.

Suna isa bakin kasuwa mai keke napep ya ajeta gefen hanya yana ajeta yaja napep d’insa ya wuce, shiga cikin tsakiyar kasuwa Naja’atu tayi ta fara sayayyar kayayyakin abinci ,saida ta kewaye kasuwar da yawon sayayya shago shago ta dinga shiga tana sayen abinda ya dace, haka dai ta cigaba da zagayar kasuwar harta kawo wurin mai saida nama ta siya tana siye ta fito daga cikin kasuwar ta nufi bakin titi tayi tsaye tana jiran keke napep .
Tana tsaye bakin titi wani mai mota zai wuce kenan yaja ribas ya dawo baya daidai wurinta danna horn yayi fifififi, Naja’atu tana jinsa tak’i waigowa ta kallesa cikin halin ko inkula ta k’ara matsawa gefe mutumen ya k’araso da motarsa wurinta yace”Assalamu alaiki”.Sanin darajar sallama ne yasa Naja’atu ta amsa masa adak’ile tace”wa’alaikas salam”.Mutumen yayi murmushin dake k’ara bayyana da tsantsar k’yawonsa yace”shigo in rage miki hanya ‘yan mata .Nagode daka barshi yanzu zan tari napep “.OK dan Allah ko zaki taimaka ki gayamin sunanki “.Banida suna”.Tana rufe bakinta saiga keke napep ya iso gabanta taronsa tayi ya tsaya shiga tayi ta sanar masa sunan unguwar dazai kaita, ciro kud’i tayi cikin handbag d’inta ta biyasa tadda napep d’in yayi suka hau saman kwalta………
[11/27, 9:24 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button