HAUSA NOVELRASHIN SO Complete Hausa Novel

RASHIN SO Complete Hausa Novel

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sis Najer’art*

*PAGE 25*

 

Ganin sun wuce mutumen ya shige cikin motarsa yana binsu abaya sannu ahankali kamar basu yake bi ba,tafiya sukeyi har suka iso bakin k’ofar gidan Baffa Zakari fitowa tayi ta shige cikin gidan mai keke napep d’in ya tadda napep d’in ya fice daga cikin unguwar, mutumen yana cikin motar yana kallon gidan da Naja’atu ta shige zaune yayi zugum yana wani sak’e sak’e cikin zuciyarsa, can dai ya lumshe k’yakk’yawan idanunsa ya bud’esu tareda yin doguwar ajiyar zuciya yace”yes thank God naga gidansu i will come back next time”.Yana gama fad’ar maganarsa ya tadda motarsa yabar cikin unguwar.
____________________

Naja’atu tana shigowa cikin gidan ta hango Anna zaune tana cin alala itadasu Rufaida, hangota da sukayi ne yasa suka mik’e tsaye suka shek’o da gudu suna cewa”Ummi oyoyo oyoyo sannu da zuwa”.
Suna isowa wurinta suka fad’a ajikinta tareda rungumeta cikin tsananin farin ciki da k’aunar ‘ya’yanta Naja’atu ta k’ank’amesu ajikinta tace”yauwa yaran albarka”.
Daga baya ta jayesu ajikinta tareda sanya hannu cikin handbag ta d’auko chocolates guda goma, taba kowanensu biyar-biyar ledodin dake rik’e ahannunta Rufaida ta amshi guda d’aya k’arasowa sukayi wurin Anna suka zazzauna saman tabarma, suna zaunawa Anna ta dubeta tace”sannu Naja’atu kin d’auko rana sosai”.
Naja’atu ta yamutsa fuska cikin yanayin gajiya tace”yauwa Anna hmmm kasuwa akwai d’aukar lokaci fa idan mutum ya shigeta da niyar sayen abu d’aya to sai ya jima kafin ya fito daga cikin kasuwa”.
Anna tace”ai haka kasuwa take yanzu dai idan kin huta kije ki d’auki alala tana nan cikin kwano kici”.
“to Anna washhhh k’afafuna duk sunyi ciwo Rufaida tashi ki d’aukomin pillow in kwanta”.
“to Ummi”.Rufaida ta mik’e tsaye ta shige cikin d’aki ba’a jima sosai ba saigata ta fito d’auke da pillow ahannunta, mik’awa Naja’atu pillown tayi ta amsa sannan ta zauna suka cigaba da cin alalarsu suna shed’anci da rashin jin magana.

*********************
Haseena suna gama masha’arsu itada Nasir ya kaita har cikin unguwar da suke sun dad’e suna tattauna maganganu masu muhimmanci, sannan daga k’arshe Haseena ta fito daga cikin motar Nasir yaja motarsa yabar unguwar, dayake daga inda ya ajiyeta zuwa gidan Basheer akwai d’an tazara shiyasa ta tako da k’afafunta ahankali harta iso bakin k’ofar gidan Basheer, tana isowa ta bud’e k’ofar gidan ta shiga cikin tsakiyar gidan anan suka ci karo da Basheer yaja k’afafunsa yayi tsaye yana kallonta yace”har kin dawo ya jikin mara lafiya?”.
Haseena ta langwab’e kanta cikin marairaicewa kamar zatayi kuka tace”hmmmm kaidai ba’a cewa komai saidai ace ubangiji ya bata lafiya jikin nata yayi tsanani sosai”.
Basheer yace cikin jimami”ayyah Allah ubangiji ya bata lafiya nizan wuce can wurin ginin gidana”.
“Allah ya kiyaye hanya mijina”.
“amin”.Yana k’arasa maganarsa ya nufi hanyar dazai fita daga cikin gidan, Haseena ta fad’a cikin d’akinta kai tsaye tana shiga ta cire tufafinta ta fad’a bathroom tayi wanka, bayan ta fito daga cikin toilet d’in ta nufi wurin gado ta zauna jawo mayukanta tayi ta shafa ajikinta sannan ta ciro doguwar riga bak’a ta sanya ajikinta, tana kammala duk abinda takeyi ta kwanta saman gado tareda rungume pillow ajikinta tunanin yadda Nasir ya nuna mata zallar soyayya da k’auna ta dingayi, murmushin farin ciki tayi tana juye juye tana k’udurta abubuwa cikin ranta wanda ita kad’ai tasan abinda yake zuciyarta.

********************
Washe gari da rana Naja’atu ta dafa musu jallof rice taji kayan lambu da maggi k’amshin girkinta duk ya gauraye gidan gaba d’aya, Anna tana kwance cikin d’aki tana jin jiki domin yau ta tashi da zazzab’i mai tsanani saida Baffa Zakari ya kira mai chemist yayi mata allurorin zazzab’i ya bata magunguna aka biyasa bayan ya tafi, yah Hamid yazo gidan domin ya gaida iyayensa ya taras da Anna babu lafiya.
Kujera ya d’auko yana zauna cikin d’akin yana yiwa mahaifiyarsa sannu da jiki, da Naja’atu ta kammala girkin ta sanyawa kowa cikin plate d’insa ta d’auko ta rurrufe da murfi,tana ajiyewa ta gaida yayanta Hamid cikin girmamawa ya amsa mata cikin sakin fuska yace”k’anwata ya hak’uri?”.
Naja’atu ta duk’ar da kanta ak’asa tace”sai godiya yaya yasu Aunty Bilkisu”.
“k’alau suke k’anwata Allah ubangiji ya baki miji nagari muja galari”.
“Amin”.Cewar Naja’atu.
Maida hankalinta tayi wurin Anna tace”Anna daure ki tashi kici abinci”.Tace cikin sanyin murya da tsananin tausayi.

Anna ta fitar da numfashin ciwo tana cije baki dak’yar ta bud’a baki tace”bana iya cin komai”.
matsowa Naja’atu tayi kusa gareta ta taimaka mata ta d’auko pillow ta jingina bayanta da pillow, abincin ta d’auko ta fara d’iba tana sanya mata cikin baki dak’yar ta had’iye abincin tana b’ata fuska kamar zatayi kuka Naja’atu sai sannu takeyi mata cikin kulawa tace”dan Allah kiyi hak’uri ki daure kici ko kad’an ne “.
Yah Hamid ya musk’uta yace”bari in tafi kasuwa in siyo mata abu mai sauk’i wanda zata iya ci, Anna mi kike iya ci mai sauk’i sauk’in had’iya?”.

Anna ta langwab’e kanta cikin rad’ad’in ciwo tace”taliyar hausa nakeso”.

Yah Hamid da Naja’atu suka kalli juna atare cikin mamaki sukace”taliyar hausa kikeso Anna!?”.
Ta gyad’a musu kai alamar eh mana yah Hamid ya kalli Naja’atu yace”akwai taliyar hausa agidan nan ki dafa mata?”.
“eh amma cikin kayayyakin miyan da nake sayarwa”.
Yah Hamid ya zaro naira dubu daga cikin aljihunsa ya mik’awa Naja’atu yace”ki bata ta d’ari uku sauran chanjin ki rik’e”.
Naja’atu tak’i amsa tace”haba yaya da kabar kud’inka koni mai iya siyowa Anna ce duk abinda take buk’ata basai ka biyani ba”.

Yah Hamid ya girgiza kansa yace”nasan da haka k’anwata ki amsa mana idan baki amsa ba zan iya yin fushi dake”.
“bazanso kayi fushi dani ba yaya amma tunda ka nace ba komai Allah ya sanya alkhairi ya bata lafiya”.Ta amshi kud’in dake cikin hannunsa.
“amin karki damu kunfi k’arfin komai awajena ku d’in kunada muhimmanci arayuwata”.
Tabbas taji dad’in kalaman yayanta har cikin b’argon zuciyarta murmushi kwance afuskarta tace”muna alfahari dakai yayanmu ubangiji ya k’ara d’aukakaka bari inje in dafa mata taliyar hausan”.

“OK ba damuwa”.Naja’atu ta tashi tsaye ta nufi kitchen d’auko taliyar tayi sannan ta jajjaga kayan miya ta soya tana gama soyawa, ta zuba ruwa tareda sanya kayan had’i zaman jira tayi har saida ruwan miyar suka tafasa sosai sannan ta zuba taliyar hausar cikin miyar, zama tayi ta cigaba da kula da taliyar harta dahu sannan ta juye cikin kula ta rufe.

Tana juyewa ta d’auko kular taliya ta kaiwa Anna agabanta plate ta d’auko ta d’iba mata abincin sauran ta rufe da murfin kular, d’ibar abincin ta dingayi da spoon tana ba Anna tana ci ahankali yah Hamid yana kallonsu yana murmushi, haka dai ta cigaba da ciyar da Anna har aka samu taci fiyeda rabin plate sannan ta kauda kanta gefe alamar ta k’oshi, tana ganin haka ta mik’e tsaye tareda aje plate ruwa masu sanyi ta d’ebo tareda d’auko magungunan Anna ta bata tasha tana yamutsar fuskarta kamar zatayi kuka, bayan tasha magani ta kwanta ta lumshe idanunta nannauyar barci ya saceta batare data ankara ba, ganin haka ne yasa yah Hamid da Naja’atu suka dawo bakin k’ofar da fira domin kada su dameta da surutu firarsu sukeyi cikin nishad’i da k’aunar juna.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button