HAUSA NOVELRASHIN SO Complete Hausa Novel

RASHIN SO Complete Hausa Novel

Baffa Zakari ne na hango tafe yana fuskantar zuwa gidansa tafe yake shi kad’ai yana zullumi akan rashin lafiyar matarsa, hannunsa rik’e da leda ya iso bakin k’ofar gidansa yana zance zuci bai ankara da motar mutum ba abakin k’ofar gidansa daga sama yaji angaidashi, waigowa yayi afirgice domin baiyi tsammanin mutum bane yana waigowa idanunsa suka fad’a cikin na magidancin saurayi wanda ak’alla shekarunsa zasu kai talatin da shida,ganin mutum ne tsaye agabansa yasa hankalin Baffa ya kwanta hannu ya mik’a masa sukayi musabaha da juna, sannan matashin magidancin yace”da farko dai nasan baka sanni ba”.
“ban sanka ba gaskiya yaro”.

K’yakk’yawan magidancin yace”ni sunana Na’im Abdulhakeem naga ‘yarka naji ubangiji ya d’oramin matsananciyar soyayyarta farat d’aya tun lokacin da idanuna sukayi tozali da fuskarta, babana Alhaji Abdulhakeem Abbas ma’aikacin gwamnati ne yana aiki ak’ark’ashin ma’aikatar ilmi mu biyu ne iyayenmu suka haifa nida k’anena Nazir………”.Baffa Zakari ya katse masa hanzari yace”ba dogon tarihi nace ka sanardani ba yanzu dai da gaske kake kana son Naja’atu? Dama tuntuni yaro nasan mahaifinka Abdulhakeem mutumen kirki bayada wata matsala arayuwarsa saboda haka indai da gaske kanason Naja’atu ka turo magabatanka asa muku ranar aure”.
Cikin zuciyarsa yace wow nice name! Ashe sunanta yana dad’i afili yace cikin ladabi”ba komai Baba zan turo magabatana asaka rana ko zan iya ganinta yanzu?”.Baffa Zakari yace”yanzu zan kira maka ita”.Yana rufe bakinsa ya shige cikin gidan azaune yaga Naja’atu da yah Hamid suna fira suna hangosa ya k’araso wurinsu, su yah Hamid sukayi masa sannu da zuwa tareda gaidashi amsa musu yayi fuska asake kallon Najaatu yace”kije ki shirya ki tafi waje kinyi bak’o sannan ki saurareshi da k’yau saboda yaron d’an mutanen kirki ne”.

“to Baffa”.Inji Naja’atu alokacin ne ta mik’e tsaye ta shiga cikin d’akin sanya hijabinta tayi ta fito ta nufi hanyar zuwa waje.

Tana isa bakin k’ofar gidan ta hango magidancin mutumen nan daya tab’a yi mata horn da tana tsaye agefen titi ,sak’e sak’e ta dingayi azuciyarta saboda tayi matuk’ar mamakin yadda yayi saurin gano gidansu kauda komai tayi cikin ranta ta k’araso wurinsa tareda gaidashi cikin sanyin muryarta mai dad’in gaske, amsa mata yayi cikin sakin fuska da shauk’in soyayyar Naja’atu kallonta kawai yakeyi ita kuma ta noce kanta ak’asa cikin kunya, sunyi shiru na tsawon lokaci kowanensu da abinda yake sak’awa azuciyarsa sannan ya bud’i baki yace”sunana Na’im Abdulhakeem inada mata d’aya da yara uku biyu maza d’aya mace ina aiki a asibiti, wato Naja’atu tun lokacin da idanuna sukayi tozali da k’yakk’yawar fuskarki Allah ya d’oramin soyayyarki ina fatar zaki fahimceni sosai ki soni ki amshi k’ok’on barar soyayyata”.

Naja’atu ta d’ago idanunta tana k’are masa kallo tsab ba k’arya Na’im ya had’u iya had’uwa bayada wata makusa ajikinsa farat d’aya taji hankalinta ya kwanta dashi, kuma zuciyarta ta amince dashi cikin yanayin sanyin hali tace”tunda har Baffa ya ganka ya aminta dakai yaji ka kuma kwantar masa azuciya, ni ta gefena babu matsala na amince zan aureka Allah ubangiji ya tabbatar mana da abinda yafi zama alkhairi “.Tabbas yaji matuk’ar dad’in kalamanta murmushi ya sakar mata yace”nagode nagode da amsar soyayyata da kikayi hannu bibbiyu cikin yarda da aminci, ni kuma da yardar Allah idan mukayi aure zan baki kulawa da tsantsar *SOYAYYAR GAKSIYA* zan baki farin ciki na har abada “Naja’atu batasan lokacin da murmushi ya kubce mata afuskarta ba tace”babu damuwa ubangiji ya gwada mana lokacin lafiya ya kauda duk wata fitina atsakaninmu”.Amin my Najerty”.Ya fad’a yana jifarta da kallon k’auna, sunan daya kirata dashi yasa Naja’atu ta rufe fuskarta alamar taji kunya sosai tabbas taji dad’in sunan daya kirata dashi wani irin sanyi da soyayyar Na’im ke kwaranya cikin jini da sassan jikinta ayanzu ta sadak’ar tayi dace da *MASOYIN GASKIYA* burinta ubangiji yasa ya rik’eta amana tareda bata tsantsar kulawa……..
[11/27, 9:24 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sis Najer’art*

*PAGE 26*

Cigaba da firarsu sukayi cikin walwala da annashuwa yayinda ak’arshe Na’im Abdulhakeem yace mata zai wuce gidansa, Naja’atu ta langwab’e kanta ta nuna masa ba matsala ubangiji ya kiyaye hanya yace mata amin, bud’e bayan boot d’in motarsa yayi ya ciro manyan manyan ledodi guda biyu shak’e da kaya mik’a mata yayi bayan ya rufe boot d’in, Naja’atu ta duk’ar da kanta ak’asa ta nok’e tak’i amsa yayi yayi da ita dak’yar da sud’in goshi ta amshi ledodinsa, nombarsa ya rubuta mata atakarda tareda sanar mata akwai waya acikin leda d’aya da sim d’inta da komai idan ya koma gidansa zai kirata, itadai sai kallonsa takeyi murmushi shimfid’e afuskarta daga baya ya shige cikin motarsa ya fice daga cikin unguwar, tsaye tayi k’yam tana godiya ga Allah mad’aukakin sarki daya bata miji batare data sha wahala ba, d’aga k’afafunta tayi ta fad’a cikin gidansu rik’e da ledodin ahannunta.

Tana isowa wurin yah Hamid ta zauna yayinda yake binta da kallo bakinsa yana motsi alamar akwai magana azuciyarsa, Naja’atu tana lura da motsin bakinsa dariya ta sakar masa tace”yaya fad’i abinda yake cikin ranka kada maganar ta kasheka”.
Yah Hamid ya harareta da wasa yace”hmm Naja’atu akwaiki dasa idanu”.
Naja’atu tace”ba wani sa ido sai gaskiya ina fa hankalce dakai yayana”.
Murmushin dake bayyana hak’ora yah Hamid yayi yace”naji kin ganoni miye acikin ledodin dake cikin hannunki?”.
Naja’atu tayi fari da idanunta cikin nishad’i tace”albishirinka yayana”.
“goro k’anwata”.
“fari ko ja?”.
Hamid ya harareta da wasa yace”kee ki gayamin idan zaki gayamin sirrin dake cikin zuciyarki fari dai ba domin halinki ba”.
“kaiiii yaya ka cika saurin fushi fa”.
“ba fushi nayi kece kikeda jan rai wlh”.
Naja’atu ta saukar da numfashi tace”yi hak’uri kana jina yanzu da Baffa ya shigo kirana tareda sanardani nayi bak’o, to ba kowa bane illa Na’im Abdulhakeem d’an hamshak’in shahararren ma’aikacin gwamnatin nan ne wanda ake yawan fira dashi cikin TV, shine yazo takanas ta kano domin ya aureni”.
Maganar ta daki zuciyar yah Hamid cikin mamaki da firgici! Ya kalleta cikin kad’uwa yace”are you sure shine d’an Abdulhakeem shahararren ma’aikacin gwamnati?”.
Naja’atu tace”i’m very sure yayana nima lokacin daya gayamin shi d’an Alhaji Abdulhakeem ne saida nayi kwankwanto amma da nayi nazari da yi masa kallon k’walelecewa saina hango tsananin kammaninsa da Alhaji Abdulhakeem, hmmm bro Allah ubangiji shike halitta d’a ya biyo mahaifinsa sak”.
Yah Hamid ya jijjiga kansa alamar gamsuwa yace”ikon Allah yafi gaban mamaki tabbas Naja’atu kinyi dacen mijin aure idan har ya biyo halin mahaifinsa, domin Alhaji Abdulhakeem mutumen kirki ne yanada girmama mutane da sanin darajar d’an Adam, sannan kokai waye k’arya ne ka fad’i sharrinsa saidai alkhairinsa alal hak’ik’a kinyi dace da masoyin gaskiya”.

Naja’atu tace”ai Allah abin godiya ne”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button