HAUSA NOVELRASHIN SO Complete Hausa Novel

RASHIN SO Complete Hausa Novel

“tabbas k’anwata kinga k’angin rayuwa amma da kikayi hak’uri kika amshi k’addararki hannu bibbiyu to gashi nan take ubangiji ya musanya miki da wanda yafi Basheer nesa ba kusa ba”.
“haka ne gaskiya yaya bari in bud’e inga abinda ya kawo mini”.
Sanya hannu tayi ta bud’e ledar farko kayan cosmetics ne da dogayen riguna masu shegen k’yau matuk’a, leda ta biyu mayuka da turarurka masu shegen k’amshi akwai kwalin iphone 7 acikin ledar sannan ga hijabbai kusan kala hud’u hannu ta sanya ta d’auko kwalin wayar, ciro phone d’in tayi daga cikin kwalinta numfashin farin ciki da murna sosai yah Hamid ya sauke yace”huhhh!K’anwata agaskiya wannan phone d’in ta had’u sosai lallai Na’im ba k’aramin so yake miki ba”.

Mik’a masa wayar tayi ahannunsa tace”tsadaddiyar waya ce da sai d’iyan masu kud’i ke rik’onta yah Hamid”.

“gaskiyarki na tayaki murna Naja’atu ubangiji yasa kiyi amfani da ita lafiya”.

“amin yayana”.

“yanzu kije ki sakata achaji ta samu ta dad’e idan ta cika zaki fara amfani da wayarki ni zan tafi gidana”.

Naja’atu ta b’ata fuska cikin sagarci tace”haba yaya tun yanzu zaka tafi baka fa wani dad’e ba fa”.

Mik’ewa tsaye yayi yace”aganinki ban dad’e ba bari inyiwa Baffa sai anjima”.Nufar d’akin yayi yaga yadda jikin Anna yayi sauk’i sosai sannan yayiwa mahaifinsa sai anjima ya fito ya wuce zuwa gida, Naja’atu ganin yayanta ya tafi yasa ta mik’e tsaye ta shige cikin d’akin Anna rik’e da ledodin ahannunta.

____________________

*BAYAN KWANA BIYU*
Jikin Anna yayi sauk’i sosai domin ayanzu tana iyayin komai da kanta, Naja’atu ta nuna mata kayayyakin da Na’im ya kawo mata itada Baffa sunyi matuk’ar farin ciki da murna sosai akan samun miji nagari da d’iyarsu tayi, cikin kayan ne taba mahaifiyarta hijabi da turare sannan taba yah Hamid turare k’yauta dak’yar ya amsa sabodashi har yanzu tausayi Naja’atun ke bashi, Baffa Zakari ta bashi turare yace tabar kayanta babu abinda zaiyi da turare, to aranar data saka chaji saida Na’im ya kirata da daddare suka sha firar soyayyarsu kamar sun jima da sanin juna.

Ayanzu ma azaune take bayan ta gama girka abincin rana wayarta tana kusa gareta saiga kiran Na’im ya shigo cikin wayar, Naja’atu batayi saurin receiving call d’insa ba saida taga ta kusa katsewa ta d’auka tace”hello my life”.Tana wani kashe murya ayangace dariyar dole na saki ni Mugirat nace ashe Naja’atu an iya soyayya samu ne kawai batayi ba ????.

Yaji dad’in sunan data kirashi dashi wani irin farin ciki da sanyi ne ya tsirgar masa cikin zuciyarsa murmushi ya kubce masa afuska kamar yana ganinta yace”Angel ina fatar kina cikin farin ciki da walwala sosai?”.

“kamar yadda kake”.
Na’im ya lumshe idanu yace”har naji dad’i matuk’a azuciyata Angel bansan wace irin soyayya ce nakeyi miki ba arayuwata, tun lokacin da idanuna sukayi tozali da fuskarki na kamu da matsananciyar soyayyarki banda sukuni da walwala saina tunaninki dare da rana, tabbas ina cikin jarabtar sonki banda tamkarki arayuwata”.

Taji dad’in maganarsa sosai har cikin zuciyarta da gangar jikinta cikin shauk’in so da k’aunarsa tace”nagode matuk’a da soyayyarka gareni my life ka sani Naja’atu tana sonka fiyeda tunaninka,hak’ik’a ka nunamin tsantsar kulawa da soyayyar gaskiya”.

“wannan kulawar da nake baki bata kai kwatan wadda zan nuna miki ba idan mukayi aure ba,saboda haka ki kwantar da hankalinki babu ke babu kuka muddin ina numfashi aduniya”.

Naja’atu tayi siririn murmushi tace”ni kuma idan mukayi aure zan kasance mai biyayya agareka har bayan numfashina”.

“naji dad’i matuk’a da kalamanki gareni Allah ubangiji ya gwada mana lokacin bikinmu lafiya”.

“Amin hasken rayuwata”.

Haka dai suka cigaba da firarsu cikin shauk’in soyayya da k’aunar junansu fiye da misali, ji sukeyi kamar su lashe junansu akan so da tsantsar k’auna.

*********************
Yah Basheer naga ya fito daga cikin gidansa yahau saman mashin d’insa kai tsaye ya nufi hanyar filin da akeyi masa gini,binshi abaya nayi domin in ganowa idanuna sabon gidansa gudu yakeyi da sauri saman kwalta har ya iso wata unguwar da ake gina sabbin gidaje, ko’ina ka duba gidaje ne sabbi fil na masu kud’i gasunan birjik ako’ina jera ga juna.
Basheer yana isowa bakin wani gida fankacece da ba’a gama gyarashi ba ya parker mashin d’insa agefen gidan,sauka yayi saman mashin d’in yayi ya bud’e get d’in gidan ya shiga cikin gidan kai tsaye ya iske masu yi masa aiki har sun fara plaster ,sallama yayi musu suka amsa masa shugabansu mai suna Isiyaku yace”yallab’ai har ka shigo”.

Basheer yace”eh Isiyaku sannunku da aiki”.

Suka amsa kusan tare sukace”yauwa”.

Basheer ya dubi plaster da sukeyi yaga yayi k’yau matuk’a jijjiga kansa yayi alamar gamsuwa da aikinsu ya juyo ya kallesu yace”aikin naku yayi k’yawo Isiyaku”.

“eh yallab’ai”.

“yanzu bari in samu abinda na baku kuci abinci”.Cewar Basheer sanya hannu cikin aljihunsa yayi ya ciro dubu goma ya basu suka amsa.

Godiya sukayi masa d’aya daga cikinsu ya nufi shagon sayar da abinci domin ya siyo suci da ‘yan uwansa, yah Basheer ya fito daga cikin gidan ya nufi gidan mahaifinsa Alhaji Tasi’u domin yaga yadda jikin hajiya Hannatu yake.

Awaje ya parker mashin d’insa ya shiga cikin gidan da k’afafunsa yana shiga cikin tsakiyar parlourn ya hango hajiya Hannatu kwance saman cushion sai nishin ciwo take fitarwa kad’an kad’an,isowa wurinta yayi da sassarfa jikinsa yana rawar tsoro yace”a’aaaa jikin ne hajiya!?”.

Hajiya Hannatu tana wani langwab’ewa akan rad’ad’in ciwo tace”jikin ne Basheer yaushe ka shigo cikin gidan nan?”.

Basheer ya kalleta yace”yanzun nan na shigo domin inga yadda kika k’arasa da jikinki”.

Tana wani lumshe idanunta tace”naji sauk’i marurun ne kawai suke yimin ciwo”.Basheer yayi tagumi cikin yanayin damuwa da b’acin rai akan rashin lafiyar mahaifiyarsa yace”ayyah ubangiji ya baki lafiya kin gama shanye magungunanki ne?”.

“a’a ban ida shanyewa ba”.”To ki bari idan kin shanye bakiji sauk’i ba saimu sake komawa asibiti kinji hajiya dan Allah ki dinga daurewa kina cin abinci ji yadda kinka rame lokaci guda”.Hajiya Hannatu ta gyad’a kanta alamar to tana runtse idanunta daga k’arshe yah Basheer ya d’auko faifai yana mata firfita, juyawa b’angaren jikinta tayi ta gyara kwanciyarta alamun firfitar tana yi mata dad’i sosai matuk’a,kallon mahaifiyarsa yakeyi cikin karayar zuciya da fargabar ciwonta shi ya rasa wane irin ciwo ne yake damunta, maganganu marasa kan gado ya cigaba da sak’awa aransa yana warwarewa ya rasa mafita, ya rasa mi yake damun mahaifiyarsa hawayen tausayinta ne ya zubo afuskarsa yasa hannunsa da sauri ya share hawayensa afaikace domin kada hajiyarsa ta gani hankalinsa ya tashi sosai………..
[11/27, 9:24 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sis Najer’art*

*PAGE 27*

 

Basheer ranar gidan mahaifinsa ya yini yana kula da mahaifiyarsa duk abinda take buk’ata shi yakeyi mata da sauri babu b’ata lokaci,bai bar gidan nan ba saida marece da Alhaji Tasi’u ya dawo gidan yi musu sallama yayi ya fice daga cikin gidan ya nufi hanyar gidansa.
Yana isa cikin tsakiyar gidan ya iske Haseena tana soyen naman rago k’amshi tashi kawai yakeyi, shigowa yayi wurinta babu ko sallama Haseena tana ganinsa tace”sannu da dawowa darling”.
“yauwa”.Yace mata cikin yanayin damuwa da b’acin rai.
Kallon k’walelecewa Haseena tayi masa tana hango damuwa da rashin walwala cikin k’wayar idonsa ajiyar zuciya tayi tace”mi yake damunka naga rayuwarka a b’ace?”.
Basheer yayi huci mai tattare da damuwa da bak’in ciki idanunsa sunyi jajir yace”hajiya ce babu lafiya ajikinta Haseena tun lokacin dana sanardake batada lafiya baki tab’a cewa ba koda wasa bari kije ki gaidata da jiki ba”.
Haseena taji haushin maganarsa cikin ranta kallon baka isa ba tayi masa tace”dakata Basheer!Karkaga laifina ka tab’a cewa inje in gaisheta banyi ba? Nifa banason ganin laifin tsiya kaji na gaya maka”.
“ke yanzu idan kinada tunani har sai nace miki kije ki gaidata,wannan ai rashin tunani ne gaskiya”.
Haseena ta d’aga murya da k’arfi tace”eh banida tunani d’in sai mi? Kaifa Basheer bari in gaya maka niba irin Naja’atu bace da idan ka kwaso shararka sai akanta, bazan je in gaidata ba kahau mumbari ka d’au landspeaker ka gayawa duniya ai mahaifiyarka ce ba tawa ba ehehhh!”.
“haka kika fad’a!?”.
“na fad’a asanyani cikin kabari da raina tun kafin in mutu!”.Haseena ta fad’a cikin masifa atsawace kamar mai fad’a da tsaranta.
Wani irin kallo Basheer ya jefeta dashi yace”bakiji ance ina kashe mutane bale kiyi tsammanin zan iya kasheki da ranki “.
Rik’e k’ugunta tayi tana cize baki alamar son fitina tace”bani iya sani abu cikin duhu cikin bak’ar leda ina na sani ko ka gaji kashe d’iyan mutane!”.Hak’ik’a maganarta tayi masa zafi da rad’ad’i azuciyarsa jin wani abu yayi ya soki k’ahon zuciyarsa cikin yanayin b’acin rai yace”nina gaji kashe d’iyan mutane!?”.
Haseena tayi masa kallon banza tace”eh na fad’a”.Tace cikin masifa.
Kallon cikin k’wayar idonta yayi ya hango masifa da bala’i ne kwance cikin idanunta, sassauta muryarsa yayi cikin sanyin hali yace”kiyi hak’uri Haseena abar maganar ta wuce shikenan”.
“bayan ka b’atamin rai sannan zaka ce inyi hak’uri”.
Yah Basheer yace”eh banason wani tashin hankali domin ciwon mahaifiyata kawai ya dameni”.
Haseena ta yamutsa fuska cikin yanga tace”naji na hak’ura ubangiji ya bata lafiya”.
“amin baby”.Yana kai k’arshen kalamansa yaja k’afafunsa fuuuuu ya fad’a cikin bathroom domin yayi wanka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button