HAUSA NOVELRASHIN SO Complete Hausa Novel

RASHIN SO Complete Hausa Novel

Harararsa ta dingayi sannan taja tsoki mtsssss tace”sakaran namiji kawai zai wani zo ya dameni akan inje inga jikin mahaifiyarsa, akan mi zanje tunda ba uwata bace idan ma son raina ne ta mutu mana babu abinda ya shafeni wannan maganar damuwarsa ce! Mutum ya girma amma baida tunani”.Tana rufe bakinta ta fara ayyukan da suke gabanta.
*** ***** ***** ******
Baffa Zakari da Anna suna zaune suna zancen Na’im Abdulhakeem wanda yakeson Naja’atu da aure, yayinda Naja’atu take zaune gefensu tana sauraren duk abinda suke fad’a.
Alokacin ne Baffa ya kalleta yace”Naja’atu kinsan keba budurwa bace mu iyayenki mune yafi dacewa mu zab’a miki mijin aure akaro na farko bana biyu ba, saboda haka kafin Na’im ya turo magabatansa inason ki gayamin gaskiya tsakani da Allah kina sonshi ko bak’ya sonshi?”.

Naja’atu ta duk’ar da kanta ak’asa cikin kunya murmushi ne shimfid’e afuskarta can k’asan mak’oshi tace”Baffa ina sonshi na amince da aurensa”.

Baffa da Anna suka saki murmushin farin ciki da annashuwa tsantsar nishad’i ne kwance afuskarsu, Baffa Zakari sai washe baki yakeyi yace”alhmdulillahi dama burina inji ta bakinki kina sonshi tsakani da Allah, saboda shi aure baya yiyuwa saida soyayya, yarda, amincewa tsakanin saurayi da budurwa, tunda kin amince zansa musu ranar da zasu zo asaka ranar aurenki saboda banason ad’auki dogon lokaci bakida aure”.
Anna tayi murmushi tace”haka ne maigida Naja’atu kinga ribar hak’urin da kikayi agidan Basheer sai gashi ubangiji ya baki miji nagari mai tsananin k’aunarki, ya kuma cire miki bak’in ciki zuwa farin ciki domin haka tun yanzu kin fahimci cewa aduniya babu abinda yake dawwama talauci ko arzik’i, bak’in ciki ko farin ciki tsanani ko sauk’i shiyasa akeson kowane musulmi ya kasance mai tawakkali da rungumar k’addararsa hannu bibbiyu”.

Naja’atu ta natsu tana sauraren nasihar da mahaifiyarta keyi mata, kwallar zallar farinciki sai shatata sukeyi asaman k’yakk’yawar fuskarta tana sharewa, hak’ik’a tasan duk abinda Anna ta fad’a gaskiya ne komai ya faru da ita *K’ADDARA CE* babu makawa sai ya sameta _(Ni kaina Mugirat rayuwar Naja’atu ta bani matuk’ar tausayi da zubar kwallar zallar takaici da bak’in cikin rayuwa, kodayake nima da irin taskun rayuwar da nake fuskanta masoyana tabbas da zakuji labarin rayuwata dasai kun tausaya min saboda nima na fuskanci k’alubalen rayuwa da *RASHIN SO* hmmm Allah ubangiji ya fitar damu daga cikin k’angin rayuwa)_.

Baffa ya girgiza kansa cikin gamsuwa da maganar Anna yace”alal hak’ik’a kinyi zance mai ma’ana da muhimmanci gaskiya, Naja’atu zanyi magana da Na’im ya turo magabatansa Allah ubangiji yayi miki albarka”.

“amin Baffa”.Inji Naja’atu.

Naja’atu ta mik’e tsaye daga baya ta shige cikin d’akin Anna tana sharar d’akin tareda jaye kayayyaki tana mayarwa agefen d’akin, haka dai ta gyara room d’in tsab zad sha’awa kunna turaren kara tayi room d’in ya gauraye da k’amshi mai k’amsashe d’akin gaba d’aya.
___________________

Yah Basheer yazo ganin jikin hajiya Hannatu dake kwance saman gado jikinta yayi matuk’ar tsanani sosai, sai wani irin farin ruwa ke fitowa daga cikin marurun dake jikinta akan yadda jikinta yayi matuk’ar zafi da tsanani yasa Alhaji Tasi’u bai fita zuwa ko’ina ba saboda ko ya fita baxai tab’a samun natsuwa da kwanciyar hankali ba, awaya ya kira Basheer yazo jikin mahaifiyarsa yayi tsanani Alhaji Tasi’u ya kalli Basheer da tun d’azu yake kukan takaici da bak’in cikin rayuwa babansa sai lallashinsa yakeyi yana cewa”kayi hak’uri ka daina kuka yanzu dai bari inyi mata wanka sai in shiryata mu kaita asibiti”.

Basheer yana kuka yace”a’a basai anyi mata wanka ba bari dai in gyara mata jikinta sai mu wuce asibitin”.
Alhaji Tasi’u yace”ba matsala bari in koma parlour in jiraka”.Yana rufe bakinsa ya juya baya zai wuce kenan hajiya Hannatu ta chapko hannunsa dole Alhaji Tasi’u ya waigo ya dawo kusa gareta cikin tsananin tausayi yace”mi kike buk’ata inyi miki Hannatu?”.

Cikin jimami da rad’ad’in ciwo ta bud’i baki hawaye masu d’auke da rad’ad’in ciwo sai zubowa sukeyi daga idanunta saboda ciwon yana matuk’ar damunta dak’yar tace”karka tafi Alhaji ku barni gida in cigaba da zama, ji nakeyi kamar bazanyi doguwar rayuwa aduniya ba duk abinda nayi muku ku yafemin”.Dak’yar ta k’arasa maganarta tana lumshe idanu da cize labb’anta.
Hankalinsu Basheer yayi k’ololuwar tashi sosai zuciyarsu ta girgiza cikin tsinkewar zuciya yah Basheer ya fashe da rikitaccen kuka wiwiwi kamar k’aramin yaro yace”dan Allah ki daina fad’ar kalmar mutuwa hajiya idan kika tafi kika barni bansan yadda rayuwata zata iya kasancewa ba”.

Alhaji Tasi’u kwallar zallar takaici ne ya zubo afuskarsa yasa hannunsa ya share cikin yanayin damuwa yace”kayi hak’uri Basheer da yardar Allah zata samu lafiya bata cikin hayyacinta ne shiyasa takeyin sabbatun magana”.

Basheer yana kuka yace”Alhaji na tsinke tuntuni da ciwon hajiya babu irin maganin da bata sha ba amma duk da haka ciwon yak’i ci yak’i cinyewa, sannan ace bazan damu ba wannan wace irin *RAYUWA CE* mai tattare da k’addarori da bak’in cikin rayuwa!?”.

Alhaji Tasi’u ya jawosa ajikinsa ya rungumesa cikin tausayawa da tsantsar damuwa yace”ya isa haka kada kayi sab’o duk abinda kaga ya samu bawa tabbas rubutacce ne awurin ubangiji, sannan kowane irin mutum da kake gani da irin k’alubalen rayuwar da yake fuskanta saboda haka ka sanya juriya da hak’uri acikin zuciyarka,komai zai zama tarihin rayuwa “.

Basheer da idanunsa suka kumbura akan yawan kuka ya bud’i baki dak’yar yace”naji Alhaji……. “.Kafin ya k’arasa maganarsa tari ne ya sark’e hajiya Hannatu ta dingayi kamar zata mutu! Da sauri suka isa wurinta suna jero mata sannu numfashinta dak’yar yake fitowa bakinta sai zubar da ruwa ruwa yakeyi,dak’yar ta samu tarin ya tsagaita cikin yanayin rashin lafiya tace”Tasi’u ga amanar Basheer nan na baka ka kula dashi nasan zaka bashi ingantacciyar rayu……… “.Kafi ta kammala maganarta jini yayi mata suk’ut daga cikin baki ta fara aman jini kamar zata amayarda kayan cikinta, ganin yadda take gudanawar jini yasa zuciyarsu ta tsinke gabansu ya bada dummmmm! Rirrik’e mata hannunwa sukayi suna zubar da hawayen tausayin kansu da mutuwar jiki, saida tayi aman jini mai yawa sannan jikinta ya saki idanunta suka firfito awaje numfashinta ya d’auke cak rai yayi halinsa!.
Ganin bata motsi da numfashi yasa Alhaji Tasi’u ya tab’i jikinta yaji shiru kara kunnensa adaidai saitin bakinta yayi yaji bata numfashi, sanya hannu yayi ya shafe mata idanu tareda fad’ar kalmar ina lillahi wa inna ilaihirraji’un! Allah ubangiji ya jik’anki Hannatu yasa kin huta! “.Cikin kad’uwa Basheer ya d’imauce yace”mi kake cewa Alhaji!?.”Hajiya ta rasu!”.”Ba gaskiya bane sake dibawa ka gani! “.Alhaji ya girgiza kansa hawaye masu zafi suna gangarowa afuskarsa yace “karka haukace d’ana ka yarda da cewa Allah ubangiji yayiwa mahaifiyarka rasuwa!”.Jin maganar Alhaji yasa Basheer yayi wani irin kwatantanwa ya fad’i k’asa biffffff ya some, k’ara rud’ewa da d’imaucewa Alhaji yayi alokaci guda shek’awa da gudu yayi ya nufi bakin get kamar zararre,tun kafin ya iso wurin getman ya hango ubangidansa yana kwasar gudu kamar zautacce gabansa ne ya buga da k’arfi rassssss! Hankalinsa ya d’unguma sosai Alhaji yana kawowa wurinsa yana haki yace”ka taimakeni Dila yarona ya sume k’asa zai mutu !”.Maigadi yace”subahanillah!Muje in gani”.Yana kai k’arshen kalamansa yaja hannun Alhaji Tasi’u suka rankaya zuwa cikin gidan…………
[11/27, 9:24 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button