HAUSA NOVELRASHIN SO Complete Hausa Novel

RASHIN SO Complete Hausa Novel

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sis Najer’art*

*PAGE 28*

 

Suna isa cikin tsakiyar d’akin marigayiya hajiya Hannatu suka iskota kwance ayadda Alhaji ya barta, maigadi ya mayarda kallonsa wurin Basheer dake kwance asome cikin mayuwacin hali tattaro dauriya da k’arfin hali yayi ya fad’a bathroom ya d’ebo ruwan sanyi akofi, yana zuwa bai tsaya b’ata lokaci ba ya watsa ruwan ajikin Basheer Alhaji yana tsaye yana kallo ya kasa aiwatar da komai akan d’imaucewa!.
Ruwan suna sauka ajikinsa rayuwarsa ta dawo cikin jikinsa wani irin numfashi ya saukar, ya farfad’o daga doguwar suman da yayi yana ajiyar numfashi sannu sannu, Dila maigadi ya dubi Alhaji yace”ya farfad’o mi yasa mi hajiya dake kwance bata motsi!? “.
Alhaji ya bud’a baki yace”Allah yayi mata rasuwa!”.
Maigadi ya dafe goshinsa cikin yanayin damuwa yace”ina lillahi wa inna ilaihirraji’un!Rai bak’on duniya duniya ba matabbata bace ubangiji ya jik’an hajiya k’yakk’yawan halayenta su bita har cikin kabarinta”.
“hmm Amin amin Dila”.
Dila ya musk’uta yace”yanzu bari inje in sanarda mutane abinda yake faruwa”.
Alhaji ya kasa k’ara cewa komai yayi yana kallon maigadi har ya fice daga cikin room d’in, Alhaji ya mayarda da hankalinsa wurin Basheer dake zaune yana risgar kuka kamar zuciyarsa zata tarwatse ya mutu! Kuka yakeyi kamar zai shid’e,shima Alhaji kukan yakeyi amma sai ya daure bai nunawa d’ansa ba dafa kafad’arsa yayi yace”ka daina kuka bata buk’atar kuka sai addu’a”.
Basheer ya fad’a ak’irjin mahaifinsa ko damuwa da bak’in cikin da yake ciki zai ragu sosai, kwallar zallar bak’in ciki sai shatata yakeyi afuskarsa wani irin d’aci da tururin bak’in ciki ke taso masa a k’irji da zuciya.

Bada jimawa ba saiga Dila maigadi ya dawo da mutane kusan su hud’u, sauran mutane masu yawa ‘yan uwa da abokan arzik’i duk suna waje suna jiran ayiwa gawa wanka afito da ita, dak’yar da lallashi suka samu Alhaji ya daure yayiwa hajiya Hannatu wanka, sannan aka lullub’eta cikin likkafani makarar da maigadi ya siyo aka ciccib’eta aka sanyata cikin makara, suka fitar da ita wurin mutane dandazon mutane suka taru akayi mata sallar gawa,ana gama yi mata sallah aka d’auketa aka kaita gidanta na gaskiya inda ko munk’i ko munso dole wata rana sai munje can.
_Allahuakbar duniya kenan ba matabbata bace,tabbas duk abinda mutum ya shuka shi zai girbi abinsa da hannunsa, duniya gidan aro ce duk abinda mutum zaiyi arayuwarsa ya dinga saka tausayi da tsoron Allah azuciya ubangiji yasa muyi k’yakk’yawan k’arshe wad’anda suka rigamu zuwa gidan gaskiya ubangiji ya jik’ansu da rahama yasa sun huta._ ????????

Haka dai gidan Alhaji Tasi’u suka kasance cikin tsananin damuwa na rashin hajiya Hannatu ,cikin yini guda duk sun zabge sun rame akan kuka da rashin cin abinci da yawa dukkansu zuciyarsu cunkushe take akan rashin hajiya! Ganin babu mace cikin gidan yasa k’anwar Alhaji Tasi’u ta dawo gidan da zama har akammala zaman makoki Zinaru itace k’anwarsa uba d’aya uwa d’aya.
Itace ta zamo kamar uwa agaresu domin tana k’ok’ari wurin basu hak’uri da kalamai masu sanyaya zuciya, wata rana da kanta take tusa Basheer agaba akan sai yaci abinci haka zai tsakuri abincin cikin rashin dad’in zuciya da jimamin mutuwar mahaifiyarsa, idan ya sanya abincin cikin bakinsa shi yakeyi kamar yana tauna mad’aci a mak’oshinsa haka dai yake daurewa yana cusa abincin abakinsa har ya d’an ci, Mama Zinaru zata kallesa cikin tsananin tausayi tana zubar kwalla afaikace domin mutuwar Hannatu ta girgiza zuk’atan danginta matuk’a da mak’wabta, kowa kaji yana maganarta saidai kaji yana yabon halayenta babu mai cewa tir da halinta!Haka akayi zaman makoki harna tsawon kwana uku ‘yan uwa da mak’wabta sai zuwa gaisuwar rasuwa sukeyi babu k’ak’k’autawa, haka sukayi ta zuwa tururururu har akayi sadak’ar bakwai kowa ya kama gabansa sukabar Alhaji, Zinaru, da Basheer suna jimamin mutuwar hajiya Hannatu hak’ik’a sunsan suyi babbar rashi na har abada rashin da bazasu tab’a mantawa dashi ba arayuwarsu saboda hajiya Hannatu ta zamo jigo da ginshik’in rayuwar gidan, gidan ya zamo babu wani haske da farin ciki acikinsa domin babu wanda zaka kalla daga Alhaji har Basheer ka hango walwala afuskarsa.

Har bayan sati d’aya da rasuwar hajiya Hannatu Basheer bai koma gidansa ba ita kuma ab’angaren Haseena bata wani damu ba akan rashin jin d’uriyar mijinta, hankalinta kwance ta cigaba da harakokinta aranar da hajiya ta rasu da taga bai dawo ba bata kirasa awaya ba d’aga wayarta tayi ta kira Nasiru tsohon saurayinta suka kwana tare kamar mata da mijinta, aranar sun biya buk’atar juna son ransu haka ya zamana kullum sai Nasiru yazo gidanta suna aikata masha’arsu cikin jin dad’i da nishad’i sosai, tuni ta mance da wani Basheer azuciyarta taji dama ya tabbata acan gidan iyayensa inda shegiyar uwarsa ta mutu! Alal hak’ik’a Haseena ta samu labarin cewa mahaifiyar Basheer ta rasu amma dayake ba uwarta bace nuna halin ko inkula tayi ta cigaba da gudanar da rayuwarta yadda take so da ra’ayi.

Mama Zinaru ganin yadda Basheer ya d’auki damuwa da bak’in ciki ya sanya azuciyarsa yasa ta lallashesa tace”haba Basheer ka daure ka sanya dangana da hak’uri azuciyarka wanda ya mutu fa ya riga ya mutu saidai mu bita da addu’ar samun rahamar ubangiji”.

Basheer ya d’ago jajayen idanunsa yace”bawai banyi imani da k’addarar da Allah ya jarabceni dashi bane a’a nayi imani da cewa lokacinta ne yayi Mana, amma kinsan nayi babban rashin jigon rayuwata mantawa da ita alokaci guda abu ne mai matuk’ar wahala azuciyata”.

Mama Zinaru tayi huci mai tattare da d’acin rai tace”nasan kana cikin rad’ad’i da zafin rashin mahaifiya amma hak’uri zakayi ka cire komai aranka tabbas komai zai wuce kamar amafarki, yanzu kaje kayi wanka kaci abinci idan kaci abinci ka tafi gidanka wurin iyalinka saboda tanada hak’k’i akanka kuma tana buk’atarka”.Basheer yace”babu inda zanje Mama ki barni inji da damuwata “.Hak’uri zakayi ka tafi wurin iyalinka domin banason ka shiga cikin hak’k’inta “.Basheer ya girgiza kansa hawaye suna kwaranya afuskarsa yace”babu inda zanje! “.

“karkayi haka d’ana kenan baka yarda da k’addararka ba bakayi imani da cewa Hannatu lokacinta ne yayi harta rasu ba, bakayi imani da cewa ba kowane mahaluki adoron duniya baya tsallake wa’adinsa ba!? “.
“nayi imani dasu mana”.

Numfashi ta sauke tareda b’oye damuwarta tace”to idan kayi imani da duka wad’annan abubuwan dana ambata to kayi abinda nace please”.

Basheer ya mik’e tsaye zumbur cikin sanyin jiki ya fad’a cikin bathroom yayi wanka, sannan ya d’ibi abinci kad’an yaci ba domin dad’in rai ba, bayan yaci iya abinda zai iya ci sannan ya mik’e tsaye ya sanya shaddarsa sky blue, wucewa yayi daga cikin gidan batare da yacewa kowa k’ala ba mashin d’insa yahau ya nufi hanyar zuwa gidansa.

____________________

Basheer yana isa gidansa ya sanya mashin d’insa cikin tsakiyar gidan ya sauka k’asa ya nufi hanyar room d’in Haseena, Haseena taji motsin mashin d’insa ta lek’o ta tagar d’akin tana kallon ramewarsa tana mamaki sannan babu annuri afuskarsa murtuk’e take, ganin ya kusa shigowa cikin d’akin yasa ta saki labule ta zauna saman kujera tana karkad’a k’afafunta, yana shigowa babu sallama Haseena ta yamutsa fuska babu ko tausayi tace “sai yanzu kaga damar dawowa cikin gidan nan ka duba ka gani satinka guda rabonka da gidan nan! “.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button