RASHIN SO Complete Hausa Novel
Maganarta ta matuk’ar yi masa ciwo azuciya da rad’ad’in zafi amma saiya wayance bai nuna mata komai afuska ba ya zauna yace”kiyi hak’uri nasan ban k’yautawa rayuwarki ba amma kiyimin uzuri ba laifi bane mahaifiyata ce ta rasu shiyasa na tsaya har aka gama zaman makoki”.
Cikin zuciyarta tace ina ruwana inda ma harda ubanka ya gangara babu abinda ya shafeni! Shege wahalallen banza, amma azahiri kalar tausayi tayi afuskarta tace”ayyah na tausaya maka ubangiji yasa ta huta kayi hak’uri lokacinta ne yayi dukkan mai rai saiya d’and’ani zafin mutuwa da rashi arayuwa”.
“uhmmmm haka ne gaskiya”.
Haseena ta langwab’e kanta cikin damuwa afuskarta tace”yanzu bari in kawo maka abincinka”.
Girgiza kansa yayi cikin rashin walwala yace”ki barshi kawai naci abinci gidan Alhaji”.
“to ko zaka watsa ruwa kaji sanyi ajikinka?”.
“a’a nayi wanka acan”.”To babu damuwa bari inje parlour in goge tufafina dana wankesu d’azu”.”OK zaki iya tafiya”.Yana rufe bakinsa Haseena ta fice daga cikin d’akin ta nufi parlour domin tayi gugar kayanta, cikin zuciyarta sai dad’i da farin ciki takeji akan mutuwar hajiya Hannatu saboda ita fa gaskiyar zance ba wani so takeyiwa Basheer ba, sallaya biyu ta shimfid’a awurin socket ta d’auko iron ta fara goge tufafinta masu yawa tana goga tana sak’e sak’e cikin ranta.
Baffa Zakari ya amshi nombar Na’im awayar Naja’atu ya kirasa sukayi magana akan ya turo magabatansa asa rana aure, Na’im yayi matuk’ar farin ciki da zancen Baffa tareda alk’awarin zai turo magabatansa bada jimawa ba, bayan gama tattaunawa ne Baffa Zakari ya mik’awa Naja’atu wayarta tareda sanar mata abinda suka zanta, Naja’atu tayi matuk’ar farin ciki da wannnan auren da zatayi na so da k’auna, Baffa ya sanarwa Anna da yah Hamid abinda ake ciki suma sunyi na’am da maganarsa tareda bayyana tsantsar farin cikinsu.
Bayan kwanaki kad’an da maganarsa da Na’im sai ya turo magabatansa aka saka rana sati biyu adaura aure, anyiwa bak’in tarba ta mutunci da karamci kuma anyi musu shimfid’ar fuska wadda tafi ta tabarma,sannan an karramasu da kayan mak’ulashe da gorunan lemun sanyi haka suka ci suka sha har suka biya sadakin Naja’atu dubu ishirin suka fice daga cikin gidan Baffa Zakari yayi musu rakiya har wurin motocinsu da suka parker ak’ofar gidansa, saida yaga tashin motarsu da wucewarsu sannan ya juyo ya koma cikin gidansa fuskarsa k’unshe da tsananin farin ciki da nishad’i sosai, yana shiga cikin tsakiyar d’akin ya iske Anna da Naja’atu zaune suna fira ganin Baffa ne yasa sukayi shiru basu ce komai ba…………
[11/27, 9:24 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????
*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sis Najer’art*
*PAGE 29*
Baffa Zakari ya zauna wurinsu tareda fitar kud’in sadakin Naja’atu aljihunsa yace”Anna ga sadakin Naja’atu dubu ishirin har sun biya”.Anna tayi murmushi farin ciki k’unshe afuskarta tace”kai madallah da wannan ranar farin ciki ubangiji ya nuna mana lokacin biki lafiya”.Naja’atu ta duk’ar da kanta ak’asa cikin kunya sannu ahankali tace”amin”.
Baffa Zakari cikin walwala da annashuwa yace”mun saka ranar d’aurin aure sati biyu masu zuwa ranar juma’a ta sama ya kama kenan”.Anna ta aza hannu saman hanci tayi gud’a tace”ayyiruhhhh Allah abin godiya ne tabbas komai yayi farko k’arshensa yana nan tafe Naja’atu kinyi goshi Allah ubangiji yasa ayi bikin cikin yawancin rai”.
Baffa Zakari yace”amin ubangiji ya share mana kukanmu yaba Naja’atu miji nagari abin alfahari ga kowace d’iya mace”.
Anna tace”ai dama haka rayuwa ta gada tun fil’azal idan wani ya k’ika wani saiya soka, Basheer ya tsangwami Naja’atu tareda nuna mata tsagwaron *RASHIN SO* itada yaranta saigashi Allah gafururraheem ya bata Na’im daga sama yana k’aunarta tareda nuna mata tsantsar *SOYAYYAR GASKIYA*,shiyasa akeson komai mutum zaiyi ya dinga sara yana dibin bakin gatari”.
Baffa Zakari ya numfasa yace”kedai bari ahalin yanzu Basheer d’in yana cikin matsananciyar damuwa da jimamin rashin da yayi”.
Anna ta ware idanunta tace”subahanillah!Waye nasa ya rasu?”.
Baffa Zakari cikin jimami da tausayi yace”mahaifiyarsa hajiya Hannatu itace ta rasu!”.
Anna ta rik’e baki cikin jimami tace”Allahuakbar!Duniyar kenan ubangiji ya jik’anta ya haskaka kabarinta tabbas duniya gidan aro ce, hmmm Allah yasa mu cika da imani baki d’ayanmu”.
Baffa yace”amin Balira abin akwai matuk’ar ban tausayi”.
“da tausayi kam sai hak’uri lamarin duniyar haka yake tafiya yau da gobe kana jin ana cewa wane ya rasu wance ta rasu ????,wata rana kaine ko kece za’a wayi gari kin mutu kinbar duniya mai cikeda datti da zaluncin rayuwa”.
“hak’k’un ce ita mutuwa ba domin rai yaso ba shiyasa komai mutum zaiyi ya dinga sanya imani da tausayi acikin lamarinsa,duk wanda ya cuci wani tun anan duniya zai girbi abinda ya shuka adoron k’asa sannan idan akaje lahira akwai hisabi tsakanin wanda ya cutar da wanda aka cuta, ubangiji dai ya tsaremu daga aikata aikin da zamuyi nadama da dana sani ya kuma tsare mana imaninmu”.
“Amin lamarin duniya ya zamo abar tsoro wlh”.
“ya zama kam”.Naja’atu ta mik’e tsaye tsam ta fito daga cikin d’akin ta samu wuri ta zauna farin ciki da kwanciyar hankali k’unshe afuskarta, ta fad’a kogin tunani can saiga sallamar k’awarta Saliha ta shigo cikin gidan bataji sallamarta ba saboda tayi nisa cikin tunani, saida ta iso wurinta ta bugi kafad’arta tayi firgigit! Ta dawo cikin hayyacinta yayinda taga Saliha murmushi ta sakar mata tace”yaushe kika zo ban sani ba?”.
Saliha tace”ya za’ayi kisan lokacin dana zo bayan kinyi nisa cikin kogin tunani wai mi yake damunki Aminiyata?”.
Murmushi ta saki farin ciki da annuri kwance afuskarta tace”banida wata damuwa ko kad’an Saliha dama inada niyar zuwa gidanki kenan saigashi kinzo, aurena ya gabato sati biyu kawai ya rage ad’aura min aurena nida masoyina Na’im”.
Saliha ta waro idanunta awaje alamar mamaki kallon Naja’atu kawai takeyi cikin murna tace”Allah abin godiya ne kayyyy k’awata na tayaki farin cikin wannan auren da zakiyi, hmmmm haka rayuwa take idan wani ya nuna maka rashin so wani sai ya nuna maka tsantsar kulawa da soyayyar gaskiya, shiyasa akeson komai mutum zaiyi ya sanya hak’uri da juriya arayuwarsa yaushe kika had’u da Na’im d’in?”.
Naja’atu tace”ba mufi sati uku had’uwa da juna ba aranar wata talata na tafi kasuwa sayayya bayan na kammala siyayyar kayan dana je siya, ina fitowa bakin titi da nufi in tari keke napep anan nayi gamdakatar dashi horn ya dingayimin da motarsa…………”.Labarin yadda yazo gidansu wurinta duk saida ta gaya mata babu abinda ta b’oye mata saboda ta yarda da ita d’ari bisa d’ari.
Saliha tana sauraren duk abinda Naja’atu ke gaya mata har takai k’arshe alokacin ne ta saukar da nannauyar ajiyar zuciya tace”tabbas kinada sa’a k’awata ubangiji ya dubi hak’uri da kukan bak’in cikin da kikayi agidan Basheer shine ya kawo miji na bugawa a mujalla, ayanzu dai kinga ribar hak’urinki tun yanzu bai fad’i k’asa abanza ba”.
“na gani Saliha shiyasa nake k’ara godiya ga ubangiji daya fitar dani daga cikin uk’ubar rayuwar dana tsinci kaina agidan azzalumin nan Basheer”.