HAUSA NOVELRASHIN SO Complete Hausa Novel

RASHIN SO Complete Hausa Novel

Saliha tace”ai Basheer kin gama da babinsa saidai tarihi”.

“haka ne kam saidai idan na tuna dana tab’a aurensa”.

Firar Na’im suka cigaba dayi suna k’yalk’yalar dariyar farin ciki da nishad’i sosai aransu, kallo d’aya zakayi musu ka gano suna cikin tsantsar walwala da fahimtar juna.

____________________

Bayan Saliha ta dawo gida ta isko har mijinta Salisu ya dawo gida yin wanka domin zafi yakeji ajikinsa bayan ya fito daga wanka ya maida tufafinsa ajikinsa,yana shiryawa saiga sallamar Saliha ta shigo cikin tsakiyar gidan fuskarta k’unshe da farin ciki sosai, amsa mata sallamar yayi ya duk’a har k’asa ya goge k’urar saman takalminsa yace”a’aaaa uwayen yawo sai yanzu kinka gadamar dawowa gida kinacan wurin Naja’atu kina fira”.

K’arasowa tayi kusa garesa tana jifansa da kallon k’auna tace”baka rabo da tsokana Baban Hassan ai ziyarar dana kai mata tayi amfani idan ba haka ba saidai muji labari amak’wabta”.

Salisu ya taso daga duk’awar da yayi yace”to sabuwar magana wace irin magana ce zamuji ana fad’i amak’wabta?”.

“hmmmm Naja’atu ce zatayi aure sati biyu masu zuwa ranar juma’a da safe”.

“keee Saliha da gaske kike fad’a?”.

Saliha ta kallesa tace”da gaske nake mana kana mamakin ikon Allah ne?”.

“a’a bana mamakin ikon Allah ashe lokaci yayi Allah ubangiji ya nuna mana juma’a lafiya yasa rayuwarmu takai”.

“Amin kaidai bakasan irin farin cikin da nake ciki ba akan wannan auren da Naja’atu zatayi”.

“ai dole ki tayata murna saboda biki na farar kaza balbela ba gayyarta akeyi ba, ni zan koma shago kinji”.

Saliha tace”Allah ya kiyaye saika dawo”.

“Amin ya rabbi”.Yana kai k’arshen kalamansa yaja k’afafunsa yayi wucewarsa zuwa shago.
**********************
*BAYAN KWANA GOMA SHA D’AYA*

Ranar Alhamis yah Basheer ne ya shigo ya iske Haseena tana zaune aparlour ga I. V nan na auren Naja’atu rik’e ahannunta tana karantawa tana dariyar k’eta, yah Basheer ya iso kusa gareta gab da gab suna jin numfashin juna ya zauna yace”mi kike karantawa Hasee baby?”.

Murmushi kawai Haseena tayi ta mik’a masa I.V card tace”ka amsa ka karanta ka gani da idanunka”.

Basheer bai kawo komai cikin ransa ba ya amshi I.V card ya fara karantawa dalla dalla tun kafin ya k’arasa karatun bak’in ciki da damuwa ya d’arsu azuciyarsa, sunan Na’im Abdulhakeem dana Naja’atu Zakari ya gani cewa gobe za’a d’aura aurensu misalin k’arfe sha biyu 12:00pm daidai na rana, kasa b’oye damuwarsa yayi ya kalleta cikin b’acin rai yace”wane shege ne ya kawo miki katin gayyata!? “.

Haseena tayi masa kallo mai d’auke da ma’anoni da yawa tace”babu shegen da ya kawo mini ak’ofar gidanka na tsinceta! “.

“shine da kika gama karantawa kika ajiyemin domin in gani in karanta”.

“eh mana domin ka gani ka karanta aiba wani abu bane”.

“awurinki ko?”.
“har awurinka idan ba akwai sauran sonta azuciyarka ba miye na damuwa da kishinta? “.

“a ina kikaga damuwa da kishinta ajikina? “.

Haseena ta bintsire baki tace”acikin k’wayar idanunka ka zata ni wawuya ce banida lura da ganewa ne?”.

Basheer yace”mak’aryaciyar banza to baki cinka daidai ba domin abinda kika fad’a k’arya ne”.

“mak’aryata dai na ganoka babu wani kame kame da zakayimin Naja’atu dai tayiwa yaro nisa saidai ya tada kai yayi kallo! “.

“ba komai ko tayi mini nisa ai komai ya faru haka ubangiji ya k’addaro”.

Mtsssss Haseena taja tsoki tace”sai yanzu kasan komai ya faru k’addara ce”.

Ganin maganar bata k’arewa dole yasa yah Basheer yaja bakinsa ya tsuke bai sake tanka mata ba domin har azuciyarsa damuwa da bak’in ciki ne ya shimfid’u afuskarsa rad’ad’in ciwo sai yawo yakeyi cikin sassan jikinsa da jininsa, ganin ya k’yaleta yasa Haseena ta mik’e tsaye ta fad’a cikin kitchen domin ta aza abinci.

____________________
Washegari da safe misalin k’arfe goma sha biyu daidai 12:00pm mutane suka shaida d’aurin auren _Na’im Abdulhakeem da Amaryarsa Naja’atu Zakari_ akan sadaki dubu ishirin lak’adan,d’auren aurensu ya samu halartar mutane da dama duk sunzo wurin d’aurin auren ya cika mak’il babu masaka tsinke ko’ina ka duba kawunan mutane ne birjik motoci da mashuna gasunan birjik ako’ina kamar an bud’e companynsu, can na hango Ango yasha farar shadda sai washe hak’ora yakeyi yana gaisawa da abokaninsa da mutanen arzik’i wad’anda suka halarci d’aurin aurensa, haka dai akayi d’aurin aure lafiya mutane suka watse kowa ya kama gabansa.

Cikin gida Anna sai kai da kawo takeyi acikin mutanenta itada k’awarta Habbe sune suke k’ok’arin ganin sun wadatar da kowa kayayyakin abinci da ruwan sanyi, mata kawai ne zazzaune kowace sai zabga lomar abinci takeyi yara k’anana sai guje gujensu sukeyi suna jin dad’i.
Haka dai kowa yaci yasha sannan suka watse da daddare misalin k’arfe takwas dai dai aka d’unguma akaje aka kai amarya d’akin mijinta, da yake bazawara ce ba budurwa ba mata biyar ne kawai sukayi mata rakiya har d’akinta, sannan suka rankayo suka dawo gida suna wucewa Na’im ya shigo d’akin Amaryarsa ya taras da ita lullub’e cikin mayafi sanya hannu yayi ya cire mata mayafinta ya ajiye agefe d’aya, ledar daya shigo da ita ya d’auko ya bud’e kaza ce k’atanya anyi mata jan gashi tana tururin zafi fara ci yayi ya yago ya sanya mata abaki, cikin kunya ta kauda kanta dak’yar da lallashi ya samu taci kazar har suka k’oshi sannan suka mik’e atare suka shiga toilet suka wanko bakinsu tareda d’auro alwala suka fito, shimfid’a sallaya yayi ya jata sukayi raka’a biyu na godiya ga ubangiji daya nuna musu wannan babbar rana.
Suna kammala sallah ya dafa goshinta ya fara kwararo addu’o’in neman tsari daga shairin shed’an la’ananne, ya dad’e yana addu’o’in sannan daga baya ya kashe wutar dake haskaka dakin gaba d’aya, dawowa yayi ya sungumeta sai saman gado domin su raya wannan dare mai tarin albarka, adaren ranar ya nuna mata tsantsar soyayyar gaskiya da k’auna wadda babu algussu acikinta sun shayar da junansu madarar k’auna da zumar soyayya, daga k’arshe naja k’afafuna na k’ara gaba domin kada in fallasa sirrin ma’aurata………
[11/27, 9:24 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sis Najer’art*

*PAGE 30*

Da safe misalin k’arfe 6:30am sukayi wanka atare suka d’auro towel fitowa sukayi daga cikin bathroom d’in, suka isa tsakiyar fankacecen d’akin Naja’atu wanda ya k’awatu da kayan alatu fiyeda tsammanin mai karatu isa wurin mirrorn dake cikin room d’in sukayi, Naja’atu ta d’auko mayuka ta fara shafawa Na’im ajiki sai lumshe idanu yakeyi yana jifarta da kallon k’auna saida ta shafe masa jiki tsab sannan ta shafe nata jiki, murmushi Na’im ya sakar mata yace”my Najerty barka da shigowa sabuwar rayuwa mai cikeda ni’ima da tarin albarka”.Duk’ar da kanta tayi ak’asa tana murmushi tace”uhmmm my life”.
Na’im ya musk’uta yace”d’ago fuskarki ki kalli fuskar mijinki saboda mun riga mun zama d’aya babu batun kunya”.
Naja’atu murmushinta mai k’yau kawai takeyi batace masa komai ba, jan hannunta yayi suka nufi wurin babbar drower dake cikin d’akinta bud’e drowern yayi ya d’auko shadda light brown taji aiki sosai sannan ya d’aukowa Naja’atu irin shaddarsa sak kalarsu d’aya, mik’a mata yayi yace”ki sanya taki shaddar my Najerty”.
Naja’atu ta d’ago fararen idanunta wad’anda suke k’ara narkar dashi ya fad’a cikin kogin soyayyarta tace”idan na shirya fa waye zai had’a mana breaskfast?”.
Yasa hannunsa ya lakaci kumatunta yace”karki damu matata Raliya ta riga ta shirya mana breaskfast”.
“OK ba komai”.Inji Naja’atu.
Amsar shaddarta tayi ta sanya ajikinta sannan ta zauna tana fuskantar mirror hango surar jikinta tayi cikin madubin,k’arewa kanta kallo kawai takeyi tana murmushin dake k’ayartar da fuskarta kayan kwalliyarta ta jawo acikin wad’anda Na’im yasa mata cikin kayan lefe fara tsantsara kwalliya mai fitinannen k’yau, tana kammala kwalliya ta feshe jikinta da turarurka masu k’amshi alokacin ne Na’im ya gama shiryawa yace”kinyi k’yau Najerty muje parlour muyi breaskfast”.
Naja’atu tayi fari da idanunta cikin sanyin murya tace”kaima kayi matuk’ar k’yawo fiye dani angona”.
Na’im yace”godiya nake Amaryata”.
Jan hannunta yayi suka nufi hanyar zuwa palourn kafin su k’arasa suka hango Raliya zaune taci wankan shadda sak irin tasu, yaranta kewaye kusa gareta Shaheed, Fa’iz, da Fa’iza suna zaune suna jiran fitowar daddynsu da amarya Naja’atu parlourn tsit yake bakajin k’arar komai saina TV suna kallon tashar dad’in kowa.
Su Na’im suka iso tsakiyar parlourn kai tsaye ‘ya’yansa suna ganinsa suka shek’o da gudu suka rungumeshi suna murnar ganinsa, sun k’ank’ame masa ajiki dak’yar ya samu ya jayesu ajikinsa kallonsu yayi yace”mu tafi dinning table muyi breaskfast”.
Fa’iza ta zumb’ura baki cikin sagarta tareda mak’e kafad’a alamar batayi murmushi Na’im yayi yace”baby Fa’iza ya akayi kike fushi da daddynki?”.
Fa’iza tace cikin k’urciya”kaine baka d’aukeni ba”.
Dafe kansa yayi yace”ohhh i’m sorry baby na manta bari in d’aukeki in goge laifina”.
Raliya da Naja’atu sai kallonsu sukeyi cikin sha’awa suna murmushi, Na’im ya d’auki Fa’iza charap yana shillo da ita dariya ta dinga k’yalk’yala itadasu Shaheed daga k’arshe ya sauketa sannu ahankali suka nufi wurin Raliya dake zaune tana kallon kwalliyar mijinta, suna isa suka zauna yayinda suka saka Na’im atsakiyarsu yara suna gefe alokacin ne Raliya da Naja’atu suka gaggaisa atsakaninsu kamar ba kishiyoyi ba, bayan sun gama gaisawa yah Na’im ya bud’e taro da addu’a sannan ya fara yi musu wa’azi da nasihohi akan su zauna lafiya da hak’uri da junansu, sannan bayason fitina ko tashin hankali su had’e kansu domin ganin zamantakewar rayuwar gidansu ta zamo abar alfahari da kwatance cikin al’umma, ya jima yana yi musu misalai da nunin hak’uri da juriya akan zamantakewar rayuwar aure sannan daga k’arshe yayi shiru ya kallesu yace”ko akwai mai magana a cikinku?”.
Raliya ta bud’i baki tace”duk abinda ka fad’a gaskiya ne daddyn Shaheed insha Allahu zamu had’a kanmu mu zama tsintsiya mad’aurinmu d’aya,domin ganin mu kwantar maka hankali tareda baka kulawa na musamman nida ‘yar uwata saboda haka indai ta gefe nace babu wata matsalar da zata kunno kai, haka nake fata awurin amarya k’anwatah”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button