RASHIN SO Complete Hausa Novel

*BAYAN WATA BIYU*
Bayan wata biyu da rasuwar hajiya Hannatu haka Alhaji Tasi’u ya cigaba da zama gidansa shi kad’ai, dayake Mama Zinaru ta tafi gidan mijinta tunda dad’ewa shi kad’ai yake rayuwa acikin gidansa cikin k’unci da yawan mafarkin matarsa, ya d’auki damuwa da rad’ad’in rashinta ya sanya azuciyarsa saboda ba k’aramin so yakeyiwa Hannatu ba, aduniya tun kafin iyayensa su rasu idan aka ciresu babu abinda yakeso fiyeda Hannatu domin aurensu auren soyayya da k’auna ne sukayi tun yana saurayi tana budurwa, idan banda maigadi Dila dake kwana cikin d’akinsa babu wanda yake shigowa cikin gidan sai d’ansa Basheer idan yazo ganinsa su gaisa ko suyi wata shawara akan abinda ya dace.
Idan bashi yazo ba haka yake rayuwa cikin matsananciyar damuwa da jimamin rashin matarsa, wata rana akan damuwa ko abinci dak’yar yake iya loma biyu cikin haka ne ciwo yayi masa buzut guda ya kamu da tsananin rashin lafiya, maigadi baisan Alhaji bayada lafiya sosai ba saida yayi kwana biyu kwance babu ci babu shi, koshi abinda yasa ya gane bayada lafiya yabar ganin giftowar ubangidansa kwata kwata a idanunsa shiyasa rana na uku ya shigo cikin parlourn baiji motsin komai ba, ganin ba kowa cikin parlourn yasa ya nufi d’akin Alhaji Tasi’u yana shiga ya hangosa cikin d’akin kwance shame -shame duk ya fice cikin kammaninsa da sauri Dila maigadi ya nufi wurinsa jikinsa yana makarkatar tsoro yace”sannu Alhaji ashe bakada lafiya”.
Alhaji Tasi’u ya kasa d’aga ko yatsar k’afarsa bale yayi magana da bakinsa.
Dila ya rungumesa ajikinsa cikin yanayin damuwa da tashin hankali yaji Alhaji ko nauyi bayada kamar ya d’auki kara ahannunsa, dube-dube cikin d’akin maigadi ya dingayi kozai hango wayar Alhaji ya kira Basheer ya sanar masa abinda yake faruwa, yana dube dube can idanunsa ya sauka akan wayar dake saman kan gado shimfid’e Alhaji yayi sannu ahankali saman gadon ya tashi tsaye ya d’auko phone d’in kiran numbar Basheer yayi dayake ya iya karanta hausa saboda yayi primary school har zuwa secondary school daga J. S. S3 ya tsaya amakaranta, yana kira nombar ta shiga d’id’id’id’i Basheer yana ganin nombar mahaifinsa ta shigo jikinsa yana rawa ya d’auka yace”Assalamu alaikah Alhaji”.
Dila maigadi yace”amin wa’alaikas salam ba Alhaji bane”.
Gabansa ya tsinke ya bada rasssss yace”idan bashi bane wa nene?”.
Maigadi ya saukar da numfashi yace”Dila ne kazo gida Alhaji bayada lafiya sosai”.
“Subahanillah!Ganinan zuwa yanzu”.Yana k’arasa maganarsa ya katse wayarsa cikin zullumi da fargabar ciwon Babansa.
Direct wurin mashin d’insa yahau yana isa bakin k’ofar gidan ya sauka ya bud’e k’ofa sannan yaja mashin d’insa ya fitar dashi waje, ya koma ya rufe k’ofar gidan sannan ya dawo yahau saman mashin d’in da sauri ya taddashi ya nufi gidan mahaifinsa cikin zullumi da fargaba.
Basheer yana isa parking lot ya parker mashin d’insa ya shige cikin d’akin Alhaji Tasi’u, yana isowa ya hango mutum kwance saman gado lullub’e da bedshit ajikinsa ga Dila maigadi zaune gefensa yayi tagumi cikin yanayin damuwa, jikin Basheer yana rawa ya kalli maigadi yace”mi yake damunsa!?”.Dila maigadi yace”nima ban sani ba ina ganin bayada lafiya sosai”.
Basheer yace”yanzu shiryashi ka canza masa kaya bari inje in fitar da mota mu kaishi asibiti”.
“to Basheer”.Fad’ar maigadi.
Basheer ya fice daga cikin d’akin da saurinsa yayinda Dila maigadi ya d’auko tufafin Alhaji Tasi’u ya sanya masa hakanan, kafin Basheer ya dawo har ya kammala shiryasa yana zuwa bai tab’a lokaci ba ya sungumi Alhaji Tasi’u ya nufi cikin mota dashi alokacin ne maigadi ya iso wurin motar, yana isa ya bud’e gaban motar ya zauna nan da nan Basheer ya tadda motar suka fice daga cikin gidan, direct ya nufi hanyar zuwa asibiti yayinda maigadi yake yawan juyowa yana kallon yadda Alhaji ke makarkatar ciwo gumi sai tsiyaya yakeyi daga jikinsa duk yayi sharkaf da zufa kamar wanda aka tsoma cikin ruwan teku, haka dai suka cigaba da tafiya cikin damuwa da tsinkewar zuciya maigadi sai juyowa yakeyi yana kallon fuskar Alhaji, suna gab da k’arasowa asibitin numfashin Alhaji ya d’auke cak rai yayi halinsa! Dila yana lura dashi ganin ya daina numfashi ne yasa ya dafi kafad’ar Basheer yace”Basheer ka dakata ina ganin kamar fa Allah yayiwa Alhaji rasuwa! “.
Dummm yaji saukar maganarsa kamar dafin kibiya yaja birki ya tsaya cikin mutuwar jiki yace”na tsaya dibamin
shi da k’yau banason maganar banza! “.
Dila ya fito daga gaban motar ya dawo baya ya kara kunnensa adaidai saitin bakin Alhaji Tasi’u domin yaji ko yana numfashi, shiru yaji babu alamar rai atattare dashi alokacin ne ya d’aga hannunsa sama ya saki jagwaf hannun ya saki sake kallon Basheer yayi yace”baya numfashi ubangiji ya amshi rayuwarsa!”.
Hawaye masu zafi suka wanke fuskar Basheer ya aza kansa yayi saman sitiyarin mota yana fad’in wannan maganar “Ina lillahi wa inna ilaihirraji’un! Yanzu ni shikenan na rasa iyayena duka miyasa kuka tafi kuka barni kusan alokaci guda!? “.Yana rufe bakinsa ya cigaba da rusar kukan bak’in ciki da rashin iyayensa jigon rayuwarsa.
Dila maigadi shima hawaye masu rad’ad’i suka wanke masa fuska yana sharewa cikin yanayin b’acin rai yace”ba kuka zakayi ba addu’arka yake buk’ata yanzu, ina ganin abinda yafi dacewa mu k’arasa cikin asibitin abincika mana idan ba doguwar suma yayi ba”.Basheer ya bud’i baki dak’yar yace”naji bayaninka amma bazan iya tuk’in motar ba kazo ka tuk’amu”.Dila baiyi wata gardama ya dawo gaba mazaunin driver ya tadda motar suka k’arasa cikin asibitin suna parker motarsu nursers sukazo da gadon d’aukar mara lafiya aka d’auki Alhaji Tasi’u, suna azashi saman gadon suka nufi emergency room dashi likitoti kunsan hud’u akansa suna bincike bincike sunyi iyakar bakin k’ok’arinsu domin ganin komai ya daidaita saboda Alhaji Tasi’u yanada rayuwa koda aka kawoshi asibiti, amma daga k’arshe suka gano ciwon zuciya yayi masa mummunan kamu nan da nan zai rai yayi halinsa ya rasu!Likitoti da kansu suka shafe masa idanu kiran Basheer sukayi suka sanar masa su d’auki gawar Alhaji Tasi’u ubangiji ya amshi ransa!. Anan suka zube ga gwiyoyinsu shida maigadi suna zubar da hawayen k’unci da tarin damuwa kuka sukeyi mai cikeda matuk’ar tashin hankali da rikicewa, dak’yar suka had’iye kukansu suka d’auki gawar Alhaji suka sakata cikin mota maigadi shi yaja motar suka fice daga cikin asibitin.
Basu zarce ko’ina ba sai gidan marigayi Alhaji Tasi’u suna parker motar maigadi ya fito da saurinsa suka ciccib’esa sai cikin gidansa sukayi masa wanka, suna kammala yi masa wanka Dila maigadi ya tafi ya siyo likkafani suka lullub’e gawar yayinda Basheer yake zaune wurin gawar sai zubarda hawayen rad’ad’i da zafin mutuwa yakeyi, maigadi ya sake fita ya sanarwa mak’wabta da abokan arzik’i na Alhaji Tasi’u nan batare da b’ata lokaci ba mutane suka taru mak’il babu masaka tsinke kowa ka kalli fuskarsa damuwa da bak’in ciki ne kwance cikin idanunsu.
Maigadi da wasu mutane suka shiga suka fito da gawar Alhaji Tasi’u domin ayi masa sallah sunyi masa sallar gawa Basheer yazo yayi masa addu’o’in daya sawwak’a acikin bakinsa, duk wani mai imani da tausayi abin saiya bashi matuk’ar tausayi daga baya aka sanya gawar cikin makara, aka fita da gawar daga cikin gidan cikin mota aka sanya gawar mutane suka shisshige cikin motocin dake parker da yawa abakin k’ofar gidan, babu b’ata lokaci suka nufi mak’abarta dashi suna isa aka gina rami aka rufe Alhaji Tasi’u. _(Allahuakbar mutuwa rigar kowa mai yankan k’auna mai raba d’a da mahaifi mai raba mata da mijinta mai raba mahaifiya da d’iyarta, hmmmm mutuwa ba dad’i amma ya muka iya dukkan mai rai saiya d’and’ani zafin mutuwa fatanmu shine ubangiji yasa muyi k’yakk’yawan k’arshe)._