HAUSA NOVELRASHIN SO Complete Hausa Novel

RASHIN SO Complete Hausa Novel

Bayan sun kaishi makwancinsa na gaskiya suka shisshigo mototinsu suka d’unguma suka dawo gida.

Bayan mutanen da suka raka Alhaji gidansa na gaskiya sun dawo suka iske Mama Zinaru da da k’anwarta Hazira zazzaune suna karb’ar gaisuwa, Basheer kuwa yana dawowa amak’abarta ya k’unshe cikin d’aki yanata riskar kukan rashin iyaye da tunanin iyayensa wad’anda bayada kamarsu aduk fad’in duniyar nan, ya kasa cin komai akan damuwa yini d’aya duk ya zabge ya rame kamar bashi ba.

Mama Zinaru akodayaushe akowane lokaci suna ganin mutane turururu masu zuwa gaisuwar rasuwa, harda abinci kala kala suka girka domin mutanen dake shigowa haka dai suka cigaba da karb’ar gaisuwa har akayi sadak’ar bakwai kowa ya kama gabansa, mutane suka tak’aita da zuwa suna zaune bayan Hazira ta kammala dahuwar abinci saiga sallamar yah Basheer ya shigo cikin gidan babu wani annuri afuskarsa ganinsa yasa Mama Zinaru tayi charab tace”ga abincinka nan kazo kaci “.”Na k’oshi “.Yace cikin rashin walwala sosai. Mama Zinaru ta kalli Hazira itama Hazira ta kalleta……….
[11/27, 9:24 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sis Najer’art*

*PAGE 32*

Suka mayarda kallonsu wurin Basheer cikin tsananin tausayi Mama Zinaru ya furta cewa”haba d’ana miyasa ba zaka sanya hak’uri da dangana azuciyarka ba shin bakasan cewa su yaya lokacinsu ne yayi ba? Kowa da kake gani idan lokacinsa yayi babu makawa sai ya tafi inda sukaje”.Alokacin Hazira tayi huci mai tattare da d’acin rai tace”hak’uri zakayi Basheer dukkan mahaluk’i adoron k’asa baya k’etare sirad’in mutuwa, muma da kake gani anan lokaci muke jira yana zuwa babu mahani sai munje”.Mama Zinaru tace”gaya masa dai amma ka d’auki damuwa da bak’in ciki kasa azuciyarka bakasan hakan yana iya haifar maka da wani cuta bane, dan Allah ka daure ka cire komai aranka addu’ar samun rahama kawai shine su yaya Tasi’u ke buk’ata agareka ba kuka ba”.Hazira tace”daure kazo kaci abinci ko kad’an ne kada yunwa ta illata mana kai, Aunty wai ina matarsa Haseena tun ranar da yaya ya rasu bata tako k’afarta cikin gidan nan ba?”.
Yatsina fuska tayi tace”Hazira kinada wata tambaya to bari in gaya maki gaskiya ba mutuwar yaya Tasi’u kawai ne tak’i zuwa ba, har mutuwar Aunty Hannatu yarinyar nan ko sau daya bata tab’a tako k’afarta cikin gidan nan idan k’arya nayi mata kada in d’aga wurin nan lafiya!”.
Hazira ta rik’e baki cikin matuk’ar mamakin mugun hali irin na Haseena tace”tabd’ijam!Lallai Basheer bayada matar k’warai ace uwarka da ubanka ya rasu amma ko sau d’aya tak bata tab’a zuwa ba, wannan wace irin mace ce mara kai da mutunci!?”.
“ai duk abinda tayi masa shi yaja akanta ne ya saki yarinyar kirki Naja’atu wadda tasan mutuncin ‘yan uwansa da karramamu amma duk da haka babu irin zalunci da *RASHIN SON* da bai nuna mata ba Hazira, duk da haka baisa tabar gidansa ba saida ya saketa!”.Cewar Mama Zinaru.
Hazira tace”Allah sarki Naja’atu akwai hak’uri da kirki Basheer baka k’yautawa rayuwarka ba gaskiya kaci amanar yarinyar mutane! “.
“don ma bakida labarin ire-iren walak’anci da k’ask’ancin da yakeyi mata marasa dad’i tareda k’unsa mata bak’in cikin rayuwa, hak’ik’a Basheer ka b’ata rayuwar gidanka dole kaje ka nemi gafararta tun kafin wani masifar ya sauko maka”.
Basheer dayake zaune ya tashi tsaye d’auke da plate d’insa na abinci yace”nifa ku tsaya tun d’azu kun dameni da surutun inje in bata hak’uri mi nayi mata da zanje in bata hak’uri? Bakuda aiki sai shiga cikin lamarin dabai shafeku ba! “.Yaja tsoki mtsssss da k’arfi ya sake cewa”kunga tafiyata kuci kanku da shegen gulmace-gulmacen tsiya! “.Yana kai k’arshen kalamansa yaja k’afafunsa fuuuuu ya nufi d’akinsa na lokacin samartaka.

Mamaki da al’ajabi ne ya shimfid’u k’arara afuskokinsu sun dad’e sunyi jugum cikin tunani da yanayin b’acin rai, saukar da numfashi Mama Zinaru tace”wannan yaron Basheer da kike ganinsa kwata kwata bayada mutunci baisan darajarmu ba”.
Takaici ne k’arara afuskar Hazira tace”wai dama haka Basheer yake d’an rainin wayo da hankali!?”.
Mama Zinaru tace”afff bakida labarin tun iyayensa suna raye baya ganin darajar mutane? Shiyasa nake ganin kamar ba zuri’ar gidanmu ya d’auko ba”.
“to ai kinsan Aunty Hannatu batada wata halayyar banza kowa cikinsu zuri’arsu yanada kirki wata k’ila halinsa ya d’auko daban”.Inji Hazira.
Mama Zinaru tace”haka ne ubangiji Allah ya shiryesa”.
“amin bari in d’ebo mana abinci muci kafin zuwa wani lokaci mubar masa gidan mahaifinsa tun kafin yayi mana korar kare”.
“yana ko iya aikata abinda kika fad’a gaskiya”.
Hazira ta mik’e tsaye tace”kina kwankwanton zai iya aikata hakan ne?”.
“A’a ba abin mamaki bane”.
“ai shine na gani”.
Hazira tana k’arasa maganarta ta fice da sauri daga cikin parlourn direct kitchen ta nufa ta ciko plate shak’e da abinci, tareda d’auko musu gorar lacasera biyu parlour ta dawo d’auke da abincin ta kawo ta dire plate agaban Mama Zinaru.
Tana direwa ta zauna tana yamutsar abincin tace”Aunty sauko k’asan carpet muci abinci”.
“to”.Mama Zinaru ta fad’a tareda saukowa saman carpet d’in cin abinci suka farayi atsanake.
____________________
Tun lokacin da Naja’atu tayi aure tabarsu Rufaida wurin mahaifiyarta to Suhail bai k’ara lafiya ba, yau ciwo gobe lafiya haka ne zuwa da dawowa yanzu ma ajikin Anna yake kwance bai jima da gama shek’a amai ba fiye da misali, Anna tana zaune duk ta shiga cikin tsananin damuwa ayayinda Rufaida take zaune agefe tana cin masa da miya.
Anna tayi tagumi mai tattare da tarin damuwa tace”bari in kira Naja’atu tazo ta d’auki d’anta wannan ciwo yak’i ci yak’i cinyewa, kullum kullum sai munje asibiti amma abu babu ja da baya sai cigaba”.Tana k’arasa maganarta ta dialling nombar Naja’atu ta shiga katse wayar tayi, can Naja’atu ta kirata danna receiving call tayi tace”Naja’atu”.
Naja’atu dake zaune kusaga Na’im tace”na’am Anna ina yini yasu Baffana?”.
Anna tayi ajiyar zuciya tace”lafiya k’alau muke saidai Suhail ne bayada lafiya tuntuni”.
Cikin fad’uwar gaba da tsinkewar zuciya tace”subahanillah!Mike damunsa Anna?”.
“to jikinsa ne ke zafi sannan yana yawan amai”.
Naja’atu zatayi magana Na’im ya amshe wayarta daga hannunta ya kara akunnensa yace”da yardar Allah zanzo yanzu in dawo dashi gidana wurin mahaifiyarsa “.
Anna tace”ayi haka Na’im ya dawo gidanka bayan kana d’awainiya da naka yaran?”.
Na’im yayi murmushi yace”babu komai ai d’a na kowa ne”.
“tunda ka fad’i haka ubangiji ya tayaka rik’o ya kuma saka maka da mafificin alkhairi”.
“ki daina yimin godiya Anna ai anzama d’aya”.
“to shikenan sai kazo”.
“uhmmmm”.Inji Na’im ya katse wayar yana kallon yanayin fuskar Naja’atu da tayi shiru can yace mata”my Najerty bari in tashi in dawo da Suhail wurinki wata k’ila idan ya dawo kusa gareki ya samu lafiya da kwanciyar hankali “.

Naja’atu tayi murmushin dake bayyana hak’ora tace”ba matsala saika dawo”.
Na’im ya tashi tsaye yace”Ok”.Ficewa yayi daga cikin room d’inta yayi ya nufi parking space ya shiga motarsa maigadi ya wangale masa get d’in gidan da sauri, ficewa yayi daga cikin gidan ya nufi zuwa unguwar iyayen Naja’atu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button