HAUSA NOVELRASHIN SO Complete Hausa Novel

RASHIN SO Complete Hausa Novel

Yayi tafiya mai tsawo ya isa wurin mai saida kayan marmari da doya, carton d’in taliya dana maggi duk saida ya siya tareda biyansa kud’insa ya tadda motarsa ya kama hanyar zuwa gidan Baffa Zakari bada jimawa ba ya k’arasa bakin k’ofar gidan, parker motarsa yayi abakin gidan sannan ya fito daga cikin motar hannunsa rik’e da ledodi sannan ya samu yara ya sanyasu jidar cartons d’in kayayyakin zuwa cikin gidan,Anna tana zaune rungume da Suhail ajikinta taga anata shigowa da kayayyakin abinci dasu lemu da ayaba tun alokacin ta fahimci Na’im d’an albarka ne yazo, saida yaran suka gama shigowa da kayayyakin cikin gida sannan suka nufi wurin Na’im dake jingine motarsa yana ganinsu yayi musu godiya, sannan su bakwai ne yaran saida ya bisu da k’yautar kud’i d’ari biyar biyar yaba kowane yaro daga cikinsu, amshe kud’in sukayi sunata tuma da tsalle kamar an basu k’yautar mota sunyi masa godiya suka wuce zuwa gidan iyayensu.

Na’im yabi bayansu da kallo yana murmushi azuciyarsa sai cewa yake k’urciya kenan wata rana sai labari, ganin yaran sunyi tafiyarsu yasa Na’im ya sanya key ya kulle motarsa kai tsaye ya nufi cikin tsakiyar gidan daga nesa ya hango Anna zaune tayi jugum cikin matsananciyar damuwa da jimamin rashin lafiyar Suhail, k’arasowa yayi wurinta ya duk’a har k’asa ya gaida Anna cikin sakin fuska da girmamawa ta amsa masa cikin walwala sannan ya zauna yace”Anna ya jikin Suhail ina fatar da sauk’i”.

Anna ta saukar da numfashi tace”da dama dama gashinan dai kwance sai ahankali”.

Na’im ya sanya hannunsa ya tab’a jikin Suhail yace”Ok ba matsala karki damu Anna da yardar Allah zai samu lafiya zan wuce dashi can gidana daga can in kaisa asibiti”.

“basai ka kaishi asibiti ba ku gwada maganin gargajiya ko Allah zaisa adace amma asibiti zuwana dashi yakai sau hud’u Hamid sau uku yana kaishi asibiti, magunguna kawai aka dinga rubutawa atakarda muna siye ak’arshe ciwo sai k’aruwa yakeyi bamu gane komai ba “.

“ba damuwa zanyi iyakar bakin k’ok’arina wurin ganin ya samu lafiya, nizan wuce ina gaida su Baffa idan sun dawo”.
“zasuji da yardar Allah”.Inji Anna.

“OK”.Ciro kud’i yayi daga cikin aljihunsa wanda baisan ko nawa bane ya mik’awa Anna yace”ga wannan ayi hak’uri ba yawa Anna”.Anna ta nok’e tak’i amsa tace”da kabar kud’inka d’an nan ai yadda ka rik’e mana Naja’atu amana ko baka bamu komai ba ya wadatar”.Na’im ya girgiza kansa tareda marairaice fuska kamar zaiyi kuka yace”wannan k’yautar na baku ne saboda Allah ba domin ina auren ‘yarku ba, dama haka rayuwata take Anna idan zanso mutum zan soshi tsakani da Allah tareda nuna tsagwaron kulawa da *SOYAYYAR GASKIYA* miye amfanin kazo ka auri yarinya ka rabata da iyayenta da duk wasu danginta sannan ak’arshe ka walak’antata tareda musgunawa rayuwarta wannan ai cin amana ne da zalunci! “.Anna tace”tabbas cin amana ne kamar yadda ka fad’a Allah ubangiji dai yasa mufi k’arfin zuciyarmu”.

“Amin amin”.
Na’im ya matso kusa ga Anna ya sungumi Suhail kamar wanda ya d’auki karan tsintsiya domin duk ya rame ya k’anjame kamar wanda baida jini ajiki, yana d’aukarsa ya fice dashi daga cikin gidan bai zarce ko’ina ba sai wurin motarsa, sanya hannu yayi ya bud’e gaban motar ya kwantar dashi sannan ya koma mazaunin driver ya zauna tareda tadda motar ya nufi hanyar zuwa asibiti.
Yana isa asibitin ya kaishi wurin babban likita mai suna Sabeer yayi masa gwaje gwaje da bincike bincike, ya jima yana binciken lafiyar Suhail sannan daga baya ya rubuta magungunan da za’a siyo atakarda nan da nan yayi inchanger d’in Suhail,Na’im ya sake rungumar Suhail ajikinsa ya dawo dashi cikin motar sannan ya sanya key ya rufesa direct chemist d’in dake kusaga asibitin ya siyo magungunan dake rubuce atakarda, saida ya biya kud’in ya juyo ya dawo wurin motarsa sanya key yayi ya bud’e car d’in ya zauna sannan ya tadda motar ya nufi hanyar gidansa.

Naja’atu ce ta fito daga wanka d’aure da towel ajikinta ‘yan watannin da tayi agidan Na’im duk yanayin jikinta ya chanza, k’yawonta da hasken fatarta duk sun bayyana kallo d’aya zakayi mata ka gano tana cikin kwanciyar hankali da samun rayayyen abinci mai girka garkuwar jiki, direct saman gado ta zauna ta jawo kayan kwalliya tana hango fuskarta cikin dressing mirror mayuka ta fara shafawa ajikinta sumul, sannan ta ciro powder ta fara shafe fuskarta cikin natsuwa da kwanciyar hankali, tana gama shafa powder ta kawo lipstick ta shafa d’auko doguwar rigarta mai adon flowers light green ta sanya ajikinta ta kawo light green veil ta lailaya akanta kamar ta d’aura gwaggwaro, tana kammala duk abinda takeyi ta kalli kanta cikin madubi tana murmushi tace”wow ashe haka nakeda k’yawo!?”.Tana rufe bakinta aka turo k’ofar room d’inta juyawa tayi charabb idanunsu ya fad’a cikin na juna, ashe Na’im ne ya shigo rungume da Suhail ajikinsa direct wurin gado ya nufa ya kwantar dashi alokacin ne Naja’atu ta iso wurinsa suna aikawa junansu zazzafan sak’onnin soyayya………
[11/27, 9:24 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sis Najer’art*

 

*PAGE 33*

Sun jima suna jifar juna da kallon soyayya mai d’auke da ma’anoni da yawa,sannan Naja’atu ta fara jaye idanunta cikin shagwab’a da salon k’auna ta fad’a a faffad’an k’irjinsa tana shak’ar k’amshin daddad’an turarensa tace”sannu da zuwa my life hop bakada wata damuwa?”.
Na’im yasa hannunsa yayi masauki abayanta cikin tsantsar k’auna da soyayya yace”banida wata damuwa Najerty”.
K’ara mannewa ajikinsa tayi tana murmushi alokacin ne taji dafin soyayyarsa da k’auna sai nuk’urk’usar zuciyarta yakeyi cikin farin ciki tace”ya ka baro su Anna ina fatar tana cikin k’oshin lafiya?”.
“Annanmu lafiyarta k’alau Baffa ne kawai ban samu damar ganinsa saboda yana wurin sana’arsa”.
Naja’atu ta mayarda kallonta wurin Suhail taga sai sharar barcinsa yakeyi cikin natsuwa kallo d’aya zakayi masa ka gano bayada lafiya sosai, cikin sanyin jiki tace”jikinsa da dama ko daddyn Shaheed”.
Na’im ya kalli cikin k’wayar idonta ya hango tashin hankali da fargaba hakan ne ya bashi damar karantar abinda yake cikin zuciyarta yace”my Najerty ki kwantar da hankalinki zai samu lafiya kinji banason in ganki cikin damuwa”.
Naja’atu tace”Allah yasa”.
“Amin my Najerty “.
Naja’atu ta dubesa tace”yanzu muje parlour muyi lunch tun d’azu su Aunty suka hallara adinning table”.
“hmmm ai kuwa dana shigo banga kowa cikin parlourn ba”.
Naja’atu tayi murmushin dake k’ara narkar dashi akogin sonta tace”baka lura bane shiyasa baka gani ba”.
Na’im yace”naji ban lura ba muje parlourn kada su gaji da jiranmu”.
“OK muje”.
Fita sukayi daga cikin room d’in suka iso tsakiyar parlourn can wurin dinning table suka hango Raliya da yaranta zazzaune suna jiran fitowarsu Naja’atu, direct suka isa wurinsu suka ja kujera suka zauna serving din kowa Naja’atu tayi sannan ta koma ta zauna ta fara cin abincinta atsanake kowanensu ya dinga bawa ciki hak’k’insa ci sukeyi bakajin k’arar komai saina chokulla, sun dad’e zazzaune kowa yana cin abinci sannan su Shaheed suka mik’e tsaye suka nufi filin wasa can kusa parking space.
Naja’atu da kanta ta tattara plates da kulolin da suka b’ata ta shiga cikin kitchen ta wankesu fess sannan ta adana plates d’in cikin kwando, fitowa tayi daga cikin kitchen ta hangosu yah Na’im har sun dawo cikin parlour sun zazzauna saman cushion suna kallon Arewa 24,isowa tayi cikin tsakiyar parlourn ta zauna gefen hagu na Na’im yayinda Raliya take zaune agefensa na dama ma’ana dai sun sakashi atsakiya,tana zama Raliya ta sakar mata murmushi tace”sannu da aiki k’anwata”.
K’yakk’yawan murmushi Naja’atu tayi tace”mi nene aiki acikin abinda nayi Aunty Raliya?”.
“wanke-wanke ma aiki ne Naja’atu”.
“haka dai kikace”.
Raliya ta kalli gefen Na’im dake zaune ya kashe kunne yana sauraren firarsu cikin natsuwa da farin ciki, alokacin ne Raliya tace”daddyn Shaheed ad’azu ina kaje ne da naga baka dad’e da fita ba kuma ka dawo?”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button