RASHIN SO Complete Hausa Novel

Na’im yayi ajiyar zuciya yace”yaron Naja’atu ne ba lafiya naje kaishi asibiti daga can nayo nan dashi”.
Raliya ta dafe k’irjinta cikin yanayin damuwa tace”ina lillahi wa inna ilaihirraji’un! Yana ina yanzu?”.
Na’im yace”yana d’akin Naja’atu”.
Itadai Naja’atu tayi shiru tana sauraren duk abinda suke fad’a.
Raliya ta kalli fuskar Naja’atu cikin tausayawa tace”haba k’anwata yanzu ashe baki yarda dani ba tunda kike b’oyemin matsalarki miyasa zakiyi haka banji dad’in wannan maganar ba?”.
Naja’atu tayi yak’e tace”afuwan Aunty ki tambayi daddyn Shaheed kiji nima banida labarin bayada lafiya sai d’azu da Anna ta kirani muna tare dashi, amma gaskiyar zance banida labarin komai bale in gaya miki”.
“ba komai na fahimceki yanzu dai muje inga lafiyar jikinsa”.Raliya tace yayinda ta mik’e tsaye alokaci guda.
“to Aunty”.Inji Naja’atu.
Itama Naja’atu ta mik’e tsaye ta shiga gaba Raliya tana biye abayanta har suka k’arasa cikin room d’in, suna isowa suka hango Suhail kwance yanata barcinsa kallon tausayi Raliya ke binsa dashi tace”ayyah daga gani yana jin jiki sosai Allah ubangiji ya bashi lafiya”.
“amin”.
Sun jima jugum cikin d’akin suna tsurawa Suhail kallo sannan daga baya suka fito daga cikin room d’in, suka dawo parlour suka zauna cigaba da kallonsu sukayi cikin walwala da annashuwa yayinda yah Na’im ya rik’i newspapers ahannunsa yana karatun labaran duniya.
____________________
Haseena ce na hango zaune cikin mota itada tsohon saurayinta Nasir suna fira cikin farin ciki.
Alokacin ne ta dubesa cikin yanayin damuwa da b’acin rai tace”Nas ya kamata muyi wani abu fa wannan alak’ak’an auren ya isheni! Ka diba ka gani shekaranjiya har dukana Basheer yayi akan ya nemi in bashi hak’k’insa na nuna masa na gaji shine ya rufeni da duka”.Nasir ya hasala b’acin rai da tsantsar damuwa ya shimfid’u k’arara afuskarsa cikin takaici yace”yanzu shi har yakai matsayin da zai d’aga k’azamin hannunsa ya bugi lallausan fatar jikinki tabbas zan nuna masa shi k’aramin tak’adari ne zaiyi nadamar dukanki arayuwarsa! “.
Haseena tayi kalar tausayi sosai tace”ba haka nakeson naji ba sai yaushe zamu aiwatar da k’udurinmu akansa!?”.
“ki kwantar da hankalinki mi kikeci na baka na zuba? Dani yake zancen zai gane inda duniya ta sawa gaba”.
“ba matsala na barka maka wuk’a da nama ahannunka kayi abinda ya kamata”.
“OK cool down my sweet muddin ina raye babu ke babu kukan bak’in ciki”.
**********************
Naja’atu tayiwa d’anta Suhail wanka ta shafe masa jikinsa da mayuka masu k’amshi, sannan ta sungumoshi ta dawo dashi cikin parlourn dasu Shaheed suke zazzaune suna fira cikin parlourn shimfid’e Suhail tayi saman cushion, Raliya ta matso kusaga Naja’atu tace”kin fito dashi hayaniyarsu Fa’iza bazai damesa ba shida bayada lafiya? “.
Naja’atu tace”idan na barshi ad’aki kuka yakeyi shiyasa na fito dashi cikin mutane”.
Raliya ta langwab’e kanta cikin tausayawa tace”Allah sarki ubangiji yayi masa sauk’i”.
“amin”.Sakashi atsakiya sukayi itada Raliya sai kallonsa sukeyi duk bayan mintuna k’alilan.
Mutum ne ya bayyana agaban Suhail da jajayen tufafi gashi zago zago lullub’e ajikinsa, wani irin siddabaru yayi da sandar tsafinsa yana karanta d’alamisai na tsafi da sihiri, kwatsam!Saiga wani irin jan haske ya fito suuu suuuu suuu daga cikin sandar Suhail kawai ne ke ganin mutumen su Naja’atu Allah bai basu ikon ganinsa ba, jan hasken ya nufi Suhail ya shige cikin jikinsa kaf, nan da nan ya tsandara ihu yana fisge fisge kamar mahaukaci sai cewa yakeyi “Ummi.. mu….tum… mu….tum… “.
Ganin Suhail ya rikice yana fisge fisge yasa hankalinsu Raliya yayi k’ololuwar tashi sosai zuciyarsu ta tsinke,rirrik’eshi sukayi su biyu yayinda kowaccesu ta tsorace da wannan rikitaccen al’amarin mai ban tausayi da al’ajabi, su Shaheed suna ganin yadda Suhail keyi kowanensu cikinsa ya d’uri ruwa suka shek’a da gudu suka nufi wurin baba maigadi suna haki da nishin gudu, baba maigadi yana ganinsu ayamutse tsoro da tsananin fargaba ne ya bayyana k’arara afuskarsa jikinsa ya dinga karkarwa yace musu “yaran manyan gobe mi ya koroku daga cikin gidan!?”.
Kasa cewa masa uffan sukayi can Fa’iz ya daure jikinsa yana makarkatar tsoro yace”baba maigadi kaje ka taimakeshi zai mutu! “.
Baba maigadi yaji gabansa ya bada dummmmm zuciyarsa ta girgiza! Ya kallesu yace”waye zai kasheshi!? “.
“bamu sani ba kaje ka gani baba”.Inji Shaheed atsorace.
Baba maigadi ya d’auko addarsa ya rataya awuyansa ya tunkari cikin gidan gadan gadan babu alamun tsoro cikin idanunsa, yana shiga cikin tsakiyar parlourn ya hango Suhail yana kakarin mutuwa bakinsa sai fitar da kumfar d’aukar rai yakeyi, su Raliya sun tsorace sai kwallar zallar takaici da bak’in ciki suke fitarwa yayinda kowace ta kasa dabarar ta kira nombar Na’im, baba maigadi ya isowa gab dasu numfashin Suhail ya d’auke cak ya daina motsi rai yayi halinsa ganin haka yasa baba yace”ina lillahi wa inna ilaihirraji’un! Allahumma ajirni fi musibati wa’akhalufni khari minha Allah ya amshi ran abinsa! “.
Maganar ta daki k’ahon zuciyarsu cikin gigicewa da d’imaucewa alokaci guda suka kalli fuskar baba maigadi Raliya tayi k’arfin halin cewa “baba ya mutu fa kace!? “.
Baba maigadi ya isa wurin Suhail ya shafe masa idanu suka rufe sannan ya kallesu cikin tausayawa yace”ba shakka saidai kuyi hak’uri ubangiji ya karb’i rayuwarsa kuma abinda baku sani ba matsafa ne suka shanye masa jini dibi yadda fatar jikinsa ya koma fari fat babu alamar jini ataredashi, yanzu dai bari in kira maigida Na’im domin yasan abinda yake faruwa”.
“matsafa kuma! A ina Suhail ya jajibo matsafa!? “.Inji Raliya ta tambaya afirgice! Naja’atu kuwa wani duhu duhu ya rufe mata idanu maganar ta soki k’ahon zuciyarta sosai wani irin jiri ne ya kwasheta ta fad’i rib rud da ciki ta some!.
“ina lillahi wa inna ilaihirraji’un! “.Itace kalmar dasu Raliya ke ambata cikin rikicewa ta shek’a da gudu ta jajibo jug d’in ruwa cikin frizer, ta iso wurin Naja’atu dake kwance cikin mayuwacin hali ta kwara mata duka ga jiki, ta aje jug ak’asa cikin yanayin tsantsar damuwa da tashin hankali! Baba maigadi ya zaro nokia a aljihunsa yayi dialling nombar Na’im batare da b’ata lokaci ba yayi receiving call d’insa yace”baba ina wuni “.
“lafiya k’alau yaron albarka kazo gida matarka babu lafiya! “.
“Subahanillah! Ganinan zuwa baba”.Yana kai k’arshen kalamansa k’it ya katse wayar arikice ya fito daga cikin office d’insa direct wurin motarsa ya nufa dake parker parking lot ya shige ya tadda motar da sauri cikin zafin nama da sak’e sak’e cikin zuciyarsa.
Kafin ya iso har baba maigadi ya sanarwa mak’wabta da abokan arzik’i rasuwar Suhail sunyi dandazo sun taru cunkushe cikin gidan Na’im, sannan yayiwa gawar wanka ya sanyata cikin likkafani Naja’atu kuwa tun lokacin data suma bata farfad’o ba domin maganar ta daketa da girgiza mata zuciya matuk’a.
Awaje Na’im ya parker motarsa ya shigo saboda mutane sun taru mak’il babu masaka tsinke ko’ina kana ganin mutane yasa tsoro da fargaba ya d’arsu azuciyarsa anata yi masa gaisuwar rasuwa, amsawa kawai yakeyi atsorace domin zuciyarsa bata bashi cewa Suhail ne ya rasu ba, direct cikin parlourn ya shiga ya hango mutum kwance lullub’e cikin likkafani bud’e likkafanin yayi yaga Suhail kwance kamar kayi magana ya amsa, mayarda likkafanin yayi ya rufe cikin mutuwar jiki da sanyin hali dak’yar ya furta cewa “ina lillahi wa inna ilaihirraji’un! Lokaci ne yayi Allah ubangiji ya jik’ansa da rahama”.Sannan idanunsa ya sauka akan Naja’atu dake kwance asome ga Raliya zaune agefenta tana risgar kuka kamar ranta zai fita, yah Na’im ya jawo Raliya ya rungumeta ajikinsa yana bubbuga bayanta alamar lallashinta cikin tsananin tausayi kwallar zallar tausayi duk ta cicciko masa a idanu yana sharewa awayance cikin dauriya yace”is OK ki daina kuka kinji haskena miye ya faru? “.Tana shassheka cikin damuwa tace”Suhail ne ya rasu shine Naja’atu ta fad’i ta suma tun d’azu bata farfad’o ba””…………..
[11/27, 9:24 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????