RASHIN SO Complete Hausa Novel
*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sis Najer’art*
*PAGE 34*
Na’im yayi huci mai tattare da d’acin rai yace”kiyi hak’uri maybe dogon suma ne tayi zata farfad’o da yardar Allah, yanzu bari in kaita d’aki in kwantar saiki zauna wurinta mu kuma zamuje mukai d’anta gidansa na gaskiya”.”To daddyn Shaheed hakan ma yayi”.
Jaye jikinsu sukayi daga na juna yah Na’im ya sungumi Naja’atu ya nufi room d’insa da ita yayinda Raliya take biye abayansa, har suka iso tsakiyar d’akin ya shimfid’eta saman tangamemmen gadonsa ya fice daga cikin d’akin da saurinsa hawayen jimami da d’acin mutuwa suna zuba a k’yakk’yawar fuskarsa, kafin ya isa wurin mutane ya ciro handkchief aljihunsa ya goge hawayensa tsab cikin sanyin jiki ya isa waje inda mutane suke damk’am kamar tururuwa, ana ganinsa akayi masa caaaa anata yi masa gaisuwar rasuwa yana gyad’a kansa, sannan aka fito da gawar Suhail akayi masa sallah ana kammala yi masa sallah Na’im yayi masa addu’o’in samun rahamar ubangiji, ya jima yana kwararo addu’o’i masu yawa sannan daga baya ya tsagaita, ganin ya gama yasa aka d’auki gawar aka saka cikin mototin dake k’ofar get d’in gidansa.
Mutane da mak’wabta suka shisshige cikin mototin suka nufi hanyar zuwa mak’abarta domin akaishi gidan gaskiya, gidan da kowa zai girbi duk abinda ya shuka adoron duniya gidan da za’a kai mutum dagashi sai halinsa. _(Hmmmm Rayuwa kenan juyi-juyi tabbas mutuwa rigar kowa ce,da ace ubangijin rahama bai halicci mutuwa da wasu shegatakarsu da buro ubansu sai ya zarce tunanin mai karatu, gara daya zama duk tsiyar da mutum ya tsola aduniya saiya barta ko yanaso ko bayaso yaje can lahira ya girbi abinsa! Saboda haka muji tsoron Allah ‘yan uwana musulmai mu kasance masu yawan tunawa da cewa ba’a tabbata aduniya duk wanda ka cutar sai ubangiji yayi masa sakayya tun anan duniya, sannan duk abinda bai shafemu ba kada mu sanya kanmu cikinsa banda shaidar zurr wato shaidar abinda baka gani da idanunka ba, ubangiji yayi mana jagora cikin lamarinmu ya kuma yafe mana kurakurranmu)._????????????
____________________
Anje ankai Suhail makwancinsa na gaskiya mutane sunata tururuwa zuwa gaisuwar rasuwa, Raliya itace ke amsar gaisuwa yayinda har yanzu Naja’atu bata farfad’o ba, yanayin gidan ya chanza gaba d’aya akan mutuwar Suhail saboda kosu Shaheed ka kalli yanayinsu zaka gano basa cikin walwala da annashuwa.
Yah Na’im daya dawo cikin gida yazo da wani babban likita ya duba Naja’atu allurai yayi mata na barci domin ta samu zafi da rad’ad’in dake cikin zuciyarta, sannan ya rubuta mata magunguna atakarda ya mik’awa Na’im yace”idan ta farfad’o akula da ita sannan ayi k’ok’ari asiyo mata magungunan dake rubuce atakardar”.
Na’im yace”ba matsala insha Allahu zanyi yadda kace nagode friend”.
“karka damu nina wuce”.
Hannunsu suna mak’ale da juna suka fito waje har wurin parking lot, doctor ya shige cikin motarsa baba maigadi ya wangale masa get d’in gidan ya fice daga cikin gidan yayinda Na’im yake d’aga masa hannu cikin sanyin jiki.
Yah Na’im ya juya ya koma cikin gida baba maigadi ya maida get ya rufe, yana isa ya iske Raliya tayi tagumi cikin damuwa isa wurinta yayi ya jaye mata hannun da tayi tagumi dashi yace”ki daina tagumi dukkan tsanani yana tareda sauk’i kinji”.
Raliya ta d’ago idanunta jajir tace”na daina daddyn Shaheed Allah ubangiji ya jik’an musulmai”.
“amin haskena”.
Zaune suke sunyi shiru dukansu suna cikin damuwa da tsananin bak’in ciki fiyeda misali, zuciyarsu sai sak’e sak’e takeyi musu rayuwarsu cunkushe da tsantsar b’acin rai da jimamin rasuwar Suhail.
*********************
Basheer yana school yaji labarin d’ansa Suhail ya rasu! Ai kuwa hankalinsa yayi k’ololuwar tashi zuciyarsa sai zugi da rad’ad’in ciwo takeyi masa, fitowa yayi daga cikin office d’in yayi fuuuu yana sauri kamar zararre, sauran malaman sai magana sukeyi masa suna tambayarsa ina zaije? Amma ina baya cikin hayyacinsa baiji abinda suke fad’a ba saboda yadda yake tafiya kamar zai tashi sama akan sauri, yana isa bakin get d’in makarantar yahau mashin d’insa ya nufi hanyar gidansa.
Zaune ya isko Haseena tasa riga da wando matsattsu wad’anda suka bayyana surar jikinta tsantsa cin ayaba takeyi tana taunawa guda guda cikin yauk’i, kallo d’aya zakayi mata ka gane batada wata matsala arayuwarta farinciki da murna ne kwance afuskarta, Basheer ya isa wurinta ya zauna yana hucin bak’in ciki da jimamin mutuwar d’ansa gumi sai tsattsafo masa yakeyi masa yakeyi ajiki ya cire hula yana firfita da ita, Haseena tana kallonsa ta gefen wutsiyar idonta can dai ta saukar da numfashi tace”lafiya ya akayi ka dawo gida bayan lokacin da zaka tashi baiyi ba? “.
Basheer yace yayinda tsantsar rad’ad’i da zafin mutuwa shimfid’e afuskarsa”yanzu ne ina zaune a office d’ina aka kirani da wata bak’uwar nomba aka sanarmin da d’ana Suhail ya rasu! “.
Haseena ta yamutsa fuska tareda bintsire baki tace”Allah yasa ya huta tunda Naja’atu tayi sabon aure naji hankalina bai kwanta na, saboda wanda ta aura yanada kud’i sosai kuma ba’asan ainahin sana’ar da yakeyi ba kaga kuwa idan d’an shan jini ne dole ya fara ta kan d’anka!”.
Basheer yayi shiru yana sauraren abinda take gaya masa cikin dogon nazari yace alamar ya gamsu da bayaninta”ai kuwa idan har mijin Naja’atu ne yayi sanadiyar mutuwar d’ana akwai buro uba wlh! Saboda baxan tab’a k’yalesa ba saina d’auki fansar jinin d’ana”.
Haseena tayi charapp tace”karkayi saurin zarginsa ka bari mubi komai sannu ahankali sai muyi bincike”.
“bincike fa kikace! Taya za’a kashemin gudan jinina sannan kice in bari ayi bincike to babu wani binciken da zanyi gaskiya! “.
“idan ba zakayi bincike ba kaje kayi masa duk abinda ka gadama babu ruwana! “.Tace azahiri azuciyarta tace Allah ubangiji yasa ka afka cikin tarkon wahala babu abinda ya shafeni, banda k’wai dakai bale inji ciwo kuma banida cikinka tuntuni na cire mahaifata domin kada in haihu dakai, amma dayake k’wak’walwar jaki dashi har yanzu bai fahimci wa cece ainahina ba!.
“Allah ya huci zuciyarki Hasee baby nifa bawai ban aminta da maganarki ba a’a abin ne da ciwo azuciya ace an kashe maka d’a abanza da yofi “.
Haseena ta sakar masa murmushin da iyakarsa afuska azuciya kuma wani irin mugun haushi da tsanarsa takeji domin idan ta tuna da marin da yayi mata, sai taji zuciyarta tayi bak’ik’irin bayada wata sauran kima ko daraja a idanunta dak’yar ta b’oye mugun nufin dake cikin zuciyarta tace”karka damu ko kad’an baka b’atamin rai ba”.
“OK babyna har kinsa naji sanyi araina”.
____________________
Da tsakiyar dare Naja’atu ta farfad’o daga doguwar suman da tayi alokacin ne yah Na’im yana rungume da ita ajikinsa, yayinda Raliya bata dad’e ficewa daga cikin room d’in ba tana farfa’dowa ta tashi zumbur zaune tana ambatar sunan Suhail tana cewa “Ina d’ana Suhail yake ubangiji yasa mafarki nakeyi bada gaske bane ya rasu yabarni!”.
Yah Na’im ya tashi zaune kwallar tausayinta yana shatata afuskarsa yace”kiyi hak’uri Najerty ubangijin daya baki Suhail amatsayin d’a ya amshi ran abinsa”.
Naja’atu ta saki rikitaccen kuka tana fisge fisge kamar mahaukaciya wani irin sihirtaccen bak’in ciki da zugi yana nuk’urk’usar zuciyarta tace”k’arya ne d’ana bai mutu ba ku dawomin da d’ana kafin zuciyata ta tarwatse in mutu! “.Yah Na’im ya jawota ya rungumeta gamm ajikinsa yana bubbuga bayanta alamar lallashi yace”ki daina fad’ar haka wanda ya riga ya mutu baya tab’a dawowa! Suhail addu’arki yake buk’ata ba kuka ba kinji da sannu zaki samu wani d’an madadinsa Najerty “.
Naja’atu tana ajiyar zuciya da shasshekar kuka tace”zuciyata zugi kawai takeyimin my life mi Suhail yayiwa mutane da har zasu shanye masa jini!? “..