RASHIN SO Complete Hausa Novel

Na’im ya ware
idanunsa yace “waye yace miki shanye masa jini akayi har ya zama sanadiyyar rasuwarsa!? “.
Naja’atu ta gaya masa abinda baba maigadi yace sannan ta k’ara da cewa “kaga kuwa maganarsa akwai k’amshin gaskiya acikinta”.
Na’im ya girgiza kansa ya kalli Naja’atu yace”ki daina furta wannan kalmar bakida shaidar cewa matsafa ne suka shanye jininsa, sannan ki cire komai azuciyarki ki fawwalawa ubangiji lamarinki, duk wanda yakeda sa hannun acikin mutuwar Suhail sai Allah yayi miki muguwar sakayya tun anan duniya! “.
“na fahimci maganarka mijina na hak’ura duk abinda mutum yayi don kansa.
Na’im ya sakar mata murmushi yace “good my Najerty haka nakeson ganin kin saki jikinki tareda share komai cikin rayuwarki ubangiji zai baki wani d’a namiji kinji”.
Naja’atu tayi masa martanin murmushinsa tareda gyad’a kanta alamar gamsuwa da kalamansa, gyara mata zama yayi yace”bari mu kwanta before gari ya waye “.Yana rufe bakinsa ya rungumeta ajikinsa yana lallashinta tareda gaya mata daddad’an kalamansa masu dad’i da sanyaya zuciyar d’an Adam, lullub’e jikinsu sukayi da blanket yah Na’im ya tofe musu jiki da addu’o’i na neman tsari.
*Da safe misalin k’arfe bakwai Naja’atu ta tashi itada mijinta tare sukayi wanka suka shafa lotions masu k’amshi ,,sannan Naja’atu ta had’a breaskfast sharp sharp yah Na’im yaci abinci ya d’auki briefcase d’insa ya fice daga cikin gidan, alokacin ne Naja’atu ta k’ara gyara bedroom da palourn tass tareda fesa room freshner k’amshi mai shiga rai da zuciya ya gauraye sashenta.
Haka zalika ab’angaren Raliya haka abin yake ta gyara bedroom da palournta tass ta feshe da room freshner, sannan tayiwa ‘ya’yanta wanka ta shiryasu cikin tsadaddin kayansu wanda kallo d’aya zakayiwa tufafin ka gano quality ne, bayan ta kammala shiryasu tace”ku tafi parlour ku zauna kafin nima inyi wanka”.Sukace “to Umma”.Shek’awa da gudu sukayi suka nufi palourn suna ‘yar rigangaya ganin sun fita yasa Raliya ta cire tufafinta ta fad’a bathroom domin tayi wanka, ta jima sosai tana gurza ko’ina ajikinta sannan daga baya ta fito d’aure da towel ajikinta gaban dressing mirror ta nufa ta zauna saman k’aramar kujera ta fara tsantara kwalliyarta mai k’yau da tsari, tana k’are kwalliya ta nufi drower ta ciro doguwar rigarta d’inkin lace tsadadden gaske maroon colour ta sanya ajikinta sannan ta d’aura d’an kwali cikeda matuk’ar iyawa da gwaninta, masha Allah Raliya k’yakk’yawa ce ba laifi feshe jikinta da turare masu tsada tayi sannan ta d’auko plat shoe maroon colour ta sanya direct ta nufi cikin parlourn, ttana isa bata hango kowa cikin parlourn ba sai akan dinning table sunyi zazzaune suna jiranta suda Aunty Naja’atu dayake haka suke kiranta, Raliya tana isowa taja kujera ta zauna yayinda Naja’atu ta mik’e tsaye ta fara serving d’insu tace “kin tashi lafiya Aunty? “.”Lafiya k’alau na tashi kefa? “……….
[11/27, 9:24 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????
*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sis Najer’art*
*PAGE 35*
Naja’atu ta saki murmushi tace”lafiya k’alau na tashi Aunty”.Tana rufe bakinta ta k’arasa serving d’insu ta zauna saman kujera, kowa yaja plate d’insa ya fara kintsa cikinsa bakajin surutun kowa yayi tsit kamar mutuwa ta gifta, haka dai suka cigaba da cin abincinsu cikin natsuwa da kwanciyar hankali har sukayi nak su Naja’atu suka tattara plates suka nufi kitchen dasu suka wankesu fess suna wasa da dariyarsu kamar k’awayen juna, sannan suka adanasu cikin kwandon plates suka fito daga cikin kitchen d’in direct parlour suka shiga suka zazzauna suna fira.
Babu dad’ewa saiga sallamarsu Anna itada k’awarta Safara’u sunzo gaisuwa rasuwar Suhail, Naja’atu tana ganin mahaifiyarta ta shek’o da gudu ta fad’a ajikinta tana cewa”oyoyo Anna nayi matuk’ar farin cikin zuwanki”.
Anna ta jayeta daga jikinta tana harararta da wasa tace”dallah jayemin ajiki kedai bak’ya rabo da shirme wlh”.
Maida kallonta tayi gefen Inna Safara’u tace”barka da zuwa Inna kun shawo rana”.
Inna Safara’u tace”yauwa ‘yar nan”.
Naja’atu taja hannunsu suka iso wurin Raliya dake zaune saman kujera, duk’awa Raliya tayi har k’asa ta gaidasu Anna cikin girmamawa da ladabi suka amsa mata cikin sakin fuska da walwala sosai, sannan ta mik’e tsaye ta nufi room d’inta suna xama fira ta b’arke atsakaninsu tareda yiwa Naja’atu jajen rasuwar d’anta Suhail can suka hango Raliya d’auke da babban tire ahannunta ta iso gabansu ta ajiye tiren, ta koma ta zauna aka cigaba da yin firar da ita sun yini agidan sannan daga baya suka mik’e tsaye xasu wuce, Raliya taje d’aki da sauri ta d’auko musu babbar leda da kayayyaki cikinta dak’yar suka amshi ledar sannan suka nufi hanyar fita daga cikin gidan su Naja’atu sukayi musu rakiya har bakin get saida sukaga tafiyarsu sannan suka koma cikin gida suna fira kamar k’awayen juna.
____________________
Haseena zaune tana waya asirrance itada Nasiru yayinda takeyin k’asa k’asa da murya batason aji ko mi suke tattaunawa, abinda naji kawai ta fad’a shine”zanyi k’ok’arin in aiwatar da k’udurinmu akansa bazan tab’a bari su fahimci manufata ba, domin banason asirina ya tonu ba za’a sami matsala ba insha Allahu”.Banji abinda Nasir ya fad’a ba naji dai yace”Ok ba matsala sai anjima”.”To”.Kawai tace ta katse wayar cikeda murmushin mugunta.
Bata jima da kammala waya ba saiga sallamarsu Basheer da abokinsa Malam Haliru sun shigo cikin parlourn kai tsaye, amsa musu sallamar tayi cikin sakin fuska tace”a’aaaa wata sabon gani yau malam Haliru agidanmu lallai ayau inada babbar sa’a”.
Suka isa wurin cushion suka zazzauna Haliru yayi murmushi yace”miye abin mamaki don nazo gidan abokina? Ai kinsan ba yau na fara zuwa gidan nan ba bale ki zolayeni Haseena amarya”.
Haseena ta yamutsa fuska cikin yanga tace”rabonka da zuwa gidan tun ina amarya sai kuma yanzu, kaga kuwa dole ince maka wata sabon gani”.
Basheer dai yana saurarensu k’ala baice ba saima danne dannen phone d’insa yakeyi cikin natsuwa.
Haliru ya girgiza kansa yace”ai nayi k’ok’ari tunda ina zuwa can ba’a rasa ba kice har yanzu shiru ko b’atan wata bakiyi ba bale kiyi ciki muzo mu kwashi gara”.Yace cikin zolayarta.
Tabbas maganarsa tayi mata zafi azuciya amma dayake akwai abinda take k’ullawa shiyasa ta wayance tace”ai kasan komai lokaci ne dashi da aure, mutuwa, haihuwa duk sunada lokaci komai Allah keyi malam Haliru”.
“haka ne gaskiya”.
Sai alokacin ne yah Basheer ya kalleta cikin sanyin murya yace”ki kawo mana ruwa musha mana tun d’azu kin damemu da surutu”.
Murmushin dake k’ayartar da fuskarta tayi tace”yi hak’uri darling inada niyar in kawo muku ruwa masu sanyaya zuciya abokinka ne yaja ni da surutu”.
Haliru yace”na jaki na kaiki ina?Kedai tashi ki kawo mana ruwa idan kinada niya”.
Haseena ta tashi tsaye tace”kaima kasan akwai niya kam”.Tana kai k’arshen maganarta taja k’afafunta tayi cikin room d’inta.
Tana shiga cikin d’akinta ta nufi fridge d’inta dake cikin d’akin bud’ewa tayi ta d’auko gorunan lemu guda biyu, sanya hannu tayi ta bud’e murfin gorunan duka biyu tana bud’ewa ta ajesu saman tire sannan ta banye k’ullin zanenta ta d’auko wata farar leda da wani irin magani acikinta na gari, bud’e ledar tayi ta zuba maganin cikin gorunan lemu ta sanya murfi ta jijjige yadda bazasu fahimci ta saka wani abu ba ciki, tana kammala abinda takeyi ta sanya farar ledar maganin acikin drower sannan ta d’auki tiren ta nufi hanyar zuwa palourn.
Tana isa ciki yah Basheer yaji gabansa ya fad’i rasssss zuciyarsa tana wani d’ard’ar ya rasa miyasa yakejin yanayinsa gaba d’aya ya chanza, Haseena ta iso wurinsu murmushi k’unshe afuskarta ta ajiye tiren agabansu ta koma ta zauna a inda ta tashi, malam Haliru ya kalleta yace”amarya lemu aka kawo mana bama ruwa lallai kin k’yauta”.