RASHIN SO Complete Hausa Novel

Haseena tayi murmushin da baikai zuci ba tace”ai wannan ba komai bane Malam karramawa ne”.
Malam Haliru yace”hakan yanada k’yau matuk’a Allah ubangiji ya nuna mana kin haihu munzo sunan d’a ko d’iya”.Yana kai k’arshen kalamansa yasa d’auki ya tsiyaya lemun akofi yasha.
“Amin amin”.
Ganin Haliru yasha lemun wani abu bai faru ba yasa Basheer ya tsiyaya nasa lemun yasha yana kallon fuskar Haseena, kozai hango abinda yake cikin zuciyarta amma ina babu abinda ya gano domin Haseena hatsabibiyar mace ce wadda ta iya tako da b’oye sirrinta.
Basheer yana shan lemun yaji dad’i ya sake k’arawa yana lumshe idanu alamar barci yanason d’aukarsa, malam Haliru duka ya shanye lemunsa yana lasar baki kamar maye, Haseena tana kallonsu tana murmushi alokacin ne taji dad’i azuciyarta tabbas burinta ya kusa cika zata d’auki fansar abinda yah Basheer yayi mata!.
Can su yah Basheer suka fara hamma alamar barci sukeji sosai lumshe idanunsu sukayi suka kishingid’a saman kujerun dake k’awace cikin parlourn, nan da nan barci mai nauyi yayi awon gaba dasu batare da b’ata lokaci ba, tana ganin barci ya sacesu Haseena ta mik’e tsaye ta k’yalk’yale da dariyar k’eta hhhhhhhh harda hawayen k’eta akan dariya can ta tsagaita dariyarta tace”k’aryarku ta k’are Basheer kwananku ya k’are!”.Tana rufe bakinta ta nufi cikin room d’inta ta d’auko wayarta tayi dialling nombar Nasiru yayi receiving call d’inta tace”hello Nas aiki ya kammala suna nan suna barci”.
Nasiru ya bushe da dariyar mugunta harda fad’uwa k’asa akan dariya can ya tsagaita dariyarsa yace”da k’yau Haseena ina k’ungiyarmu ina jiranki kizo dasu karki b’ata lokaci fa”.
“bazan b’ata lokaci ba ina zuwa yanzu nan”.
“OK k’ungiya ke kad’ai kawai take jira sai kinzo”.
“to my Nasiru”.Katse wayar tayi k’it domin tayi sauri ta gama komai kafin wani ya shigo, juyawa tayi ta d’auko handkchief d’in tsafi da sihiri ta nufi wurinsu yah Basheer dake kwance, tana isa wurinsu ta shafa musu handkchief d’in afuskarsu suka shak’i k’amshin dake cikinsa, nan da nan daga ita harsu Basheer suka b’ace b’at kamar basu tab’a wanzuwa ba.
*********************
Su Naja’atu suna zaune cikin parlourn suna fira saiga sallamar yah Na’im ya shigo hannunsa rik’e da briefcase d’insa, mik’ewa su Naja’atu sukayi kowace ta amshi kayan dake hannunsa d’aya briefcase d’aya ledodin biyu ta amsa tareda yi masa sannu da zuwa, wurin kujera suka iso suka zazzauna yayinda Raliya ta mik’e ta shigewarta cikin d’akinsa domin ta surka masa ruwan zafi, tana gamawa ta fito ta iskosu shiru yah Na’im duk ya gaji sai saukar da numfashin gajiya yakeyi kallonsa tayi tace”daddyn Shaheed muje kayi wanka”.
Na’im ya kalli Raliya cikin alamar gajiya sai lumshe idanu yakeyi yace”to first lady bazaki barni in d’an huta ba?”.
Raliya ta langwab’e kanta cikin sagarci tace”kadai daure muje kayi wanka idan kayi wanka kaci abinci zakaji gajiyar ta gudu da kanta”.
“gaskiya Aunty ta fad’a ka daure kaje kayi wanka zakafi jin dad’in jikinka”.
Na’im ya kalli gefen Naja’atu yace”hmmm wad’annan matan nawa duk kun had’emin kai bari dai in tashi karku cinyeni d’anye”.Yace cikin zolaya da wasa.
“ai bakaji ance muna cin mutane ba bale mu cinyeka ba”.Cewar Raliya tana dariya.
Na’im ya mik’e tsaye zumbur cikin sanyin murya yace”muje na tashi domin na lura idan ban tashi ba kuna iya yimin duka keda k’anwarki”.
Naja’atu tayi tsagal tace”kamar ko ka sani da baka mik’e ba zamu iya dukanka”.
“ai shiyasa na mik’e tsaye Najerty “.Na’im yana kammala maganarsa yaja k’afafunsa ya nufi room d’insa yayinda Raliya ta bishi abaya sukabar Naja’atu zaune ita kad’ai cikin parlourn, yayinda su Shaheed sun tafi school tunda safe shiyasa gidan ya kasance tsit babu hayaniya.
*********************
Su Haseena suna b’acewa b’at basu bayyana ko’ina ba sai cikin wani irin gida da yake cikin k’usurgumin daji mai dogayen itatuwa da yawan tsirrai,atsakiyar mutane sanye da tufafi jajaye suka bayyana yayinda shugaban matsafa yake zaune kan karagar tsafi tukunyar tsafi ce agabansa cikeda jinin bil’adama, Haseena tayi sujjada ga shugaban matsafa ya shafi bayanta alamar amsar gaisuwa.
Sannan ta koma cikin ‘yan uwanta matsafa wad’anda suke tsaye k’yam, sandar tsafi shugaba yayi nuni zuwa ga Haseena saiga jajayen tufafi irin nasu sun bayyana ajikinta ta sare cikinsu, tana cikinsu taji muryar Nasir kusa gareta yace mata”har kinzo dasu?”.
Haseena tace”eh na iso”.
Su Basheer suna kwance saman gadon da yake tsakiyar matsafan suna barci, shugaban matsafa ya fara karanto d’alamisai na tsafi da sihiri wata irin tururin hayak’i ne da guguwa ta game wurin tana zagayarsu Basheer ginin gidan ya dinga rawa da girgiza kamar zai kife ak’asa! Can kaji tsawa ta bayyana ratsatsatsa fassfass! Wurin ya game da masifaffen duhu wanda ko yatsa baka iya hangowa akan bala’i da masifa, can shugaban matsafa yayi siddabaru farin haske ya fito ya gauraye wurin duhu ya yaye, nuni yayi da hannunsa zuwa gasu Basheer dake kwance suna barci ruwan zafi tafasasshi suka zuba ajikinsu saida suka farka da zabura da k’arfi! Ahankali idanunsu Basheer suka waye da k’yau suna kallon mutane da jajayen tufafi tareda matuk’ar mamaki k’unshe afuskarsu, nan da nan tunanin komai ya dawo cikin k’wak’walwarsu suka zabura suka zazzauna saman gadon Basheer ya kalli Haliru yace”Haliru mi ya kawomu gidan matsafa!? “.”Bani ya dace kayiwa wannan tambayar ba matarka Haseena itace ta bamu lemu mukasha muna sha muka b’ingire da barci, saboda haka ita ya dace ka kira ka tambaya “.”Ban ganeta anan ba”.”Idan har tana cikinsu idan ka kirata zata amsa”.”To bari in kirata inji “…………
[11/27, 9:40 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????
*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sis Najer’art*
*PAGE 36*
Yana rufe bakinsa Haseena ta fito daga cikin mutane masu jajayen tufafi ta iso gaba garesu tace”basai ka kirani ba Basheer gani na fito fad’i tambayarka kafin ka mutu kabar duniya!”.Basheer ya kalleta cikin mamaki da al’ajabin da suke kwance afuskarsa yace”Haseena miyasa kika kawomu wurin nan dama ke ‘yar shan jini ce!?”.Haseena ta kallesa cikin ido da ido idanunta sun rikid’a sun koma jawur kamar barkono! Tsananin rashin tausayi da rashin imani ne kwance cikin k’wayar idanunta cikin kakkausar murya tace”kayi tambayar daya dace Basheer yanzu kuwa zan baka amsarka,tabbas ni ‘yar shan jini ce na kawoku wurin nan ne domin in musha jininku!”.
Cikinsu yah Basheer ya d’uri ruwa zuciyarsu ta tsinke gabansu ya bada dummmmm hankalinsu yayi k’ololuwar tashi sosai! Basheer ya kalli Haliru shima Haliru ya kallesa tsananin tsoro ne shimfid’e afuskarsu, jikinsu duk ya mutu Haliru ya fashe da kuka yace”mun shiga uku Basheer! Da nasan matarka matsafiya ce da banzo gidanka ba ashe k’addara ce ta kawoni gidanka, ashe mutuwa ce ke bibiyata kiyafemin matata Hansa’u nasan ni tawa ta k’are ki rik’emin yarona Is’hak’a!”.
“Kaiiiiiii! Ba’a kuka anan rufe mana baki ko yanzu ka bak’unci lahira!”.Inji Haseena.