RASHIN SO Complete Hausa Novel

Tsawar data dakawa Haliru yasa ya tsure ya saki fitsari tsulutttf cikin wando sannan zawo ya biyo daga baya b’urrrrrrr kawai kaji yana tashi! Nan da nan fitinannen wari da d’oyin kashi ya gauraye wurin gaba d’aya jin warin kashin Haliru ya game wurin yasa Nasiru ya harzuk’a zuciyarsa ta kawo ga wuya akan zawon da Haliru yayi,isowa wurinsa yayi ya d’aukesa gigitattun maruka biyu masu k’yau wanda asanadiyar haka saida ya saki razananniyar k’ara ya dafe kuncinsa yana hawayen k’unci da ganin mutuwa k’iri k’iri babu mai cetonsu!.
Nasir yace musu cikin kakkausar murya”kar in sakejin kukan kowane shege acikinku idan ba haka ba zan sare kawunanku! “.
Jikinsu Basheer ya d’auki k’yarrma cikinsu ya dinga k’ugi k’uuuuuuuu!hanjin cikinsu yahau tsine gumi ya dinga tsattsafo musu ajiki dak’yar suke iya kallon masu jajayen tufafi.
Dak’yar Basheer ya sake jefo mata tambaya yana zubar da hawayen takaici da tausayin kansu yace”mi nayi miki Haseena da zakiyimin irin wannan mummunan sakayyar? Nidai arayuwata bansan nayi miki wani abu na cutarwa ba kullum burina ki kasance cikin farin ciki da annashuwa, amma sai gashi yanxu kinason ganin bayana!”.
Cikin d’acin rai da tunanin rayuwarta na baya ta kallesa cikin idanunta kana hango tsananin damuwa da bak’in cikin abinda ya faru ashekarun baya tace”zan sanardakai dalilin dayasa zan kasheka da kuma musabbabin dayasa na shiga cikin k’ungiyar matsafa! “.
Basheer yace”inason inji saboda in gano bakin zaren”.
Hawayen takaici suka zubo afuskar Haseena bata damu data share ba ta bud’i baki tace”……
*ASALIN LABARI*
Ashekarun baya Alhaji Tasi’u ya kasance gawurtaccen mai arzik’i wanda ya gaji dukiyar ga mahaifinsa Garzali,mahaifinsa ya rasu tun yana matashin saurayi ya mutu yabarsa wurin k’anensa Umar, shi ya cigaba da kulawa da rayuwar Tasi’u har ya girma ya mallaki hankalin kansa ya kammala school sannan baba Umar ganin ya isa aure ya aura masa d’iyar k’anwarsa yarinya mai suna Hannatu, ahaka akayi bikinsu cikin karramawa da wadata sannan baba Umar ya mallaka masa dukiyar mahaifinsa.
Tuni Tasi’u ya gina nashi gidan ya koma shida matarsa ya cigaba da gudanar da harakokin business d’insa cikin kwanciyar hankali, haka ubangiji ya cigaba da bud’a masa falalar arzik’i kud’i masu kauri sunata shigowa ta ko’ina, ganin yana samun kud’i masu yawa yasa ya fara siyen filaye, shagogi, da sauran kadarorin da yake siye yana adanawa domin ‘ya’yan dazai haifa nan gaba.
Bayan wasu watanni Hannatu ta samu ciki zo kuga farin ciki da murna afuskokin wad’annan bayin Allah, haka dai ya cigaba da tattali da bata kulawa na musamman fiyeda tunanin mai karatu, lokaci ya cigaba da tafiya kwanaki suka shud’e har cikin Hannatu ya isa haihuwa ta haifi sankacecen d’anta namiji ‘yan uwa da abokan arzik’i sunzo yi musu barka, ranar suna tana zagoyawa yaro yaci suna Basheer manyan manyan raguna guda hud’u aka yanke masa, anyi wadataccen abinci da gorunan lemuka iri iri gasunan birjik ako’ina haka dai mata ‘yan biki suka ci sukayi nak, sannan taro ya watse kowa ya kama gabansa.
Haka Hannatu ta cigaba da tsantsar kulawa da d’anta tana rainon abinta cikin wadata da kwanciyar hankali, Tasi’u yana sakar mata kud’i sosai domin yana matuk’ar k’aunarta tareda yi mata soyayyar gaskiya wadda babu algussu acikinta.
Bayan shekaru da dama alokacin ne Basheer ya kammala karatunsa babansa ya samo masa aiki asecondary school, idan ya dawo daga karantassuwa saiya iske mahaifinsa akasuwa yana tayasa gudanar da business d’insa, haka dukiyar ta cigaba da bunk’asa tana k’ara yawaita tareda habbak’a.
Wata rana Alhaji Tasi’u yana cikin shagon kasuwancinsa shida yaransa suna kai da kawo yayinda yah Basheer yake matashin saurayi mai ji da kansa, yana tsaye abakin shago saiga sallamar wata budurwa wadda batafi 15 years ba Basheer yana danne dannen wayarsa cikin jin kai ya amsa mata adak’ile.
Budurwar ta kallesa cikin tsananin damuwa da zullumi tace”bawan Allah taimako nake nema”.
“ina saurarenki taimakon mi kike nema?”.Cewar Basheer batare daya d’ago kansa ba ya kalleta.
“Alhaji Tasi’u nakeson gani domin ya taimaka mini da kud’i inkai mahaifiyata asibiti dake kwance batada lafiya”.
Sai alokacin ne Basheer ya d’ago fararen idanunsa yayi mata walak’antaccen kallo, ya dubeta sama da k’asa kaya ne wad’anda suke yagaggu sunsha jiki sosai ajikinta ga k’annenta rik’e ahannunta, dak’yar ya bud’i baki cikin kakkausar murya”keee dallah gafaran can da rub’ebb’en bakinki mai shegen wari! Don kina shegiya ki rasa a ina zakiyi bara sai anan b’acemin da gani ko yanzu in halakaki”.
Jikin budurwar ya d’auki rawa hawaye sai shatata sukeyi asaman fuskarta tace”kataimakamin bawan Allah wallahi ba barana nakeyi ba taimako nake nema”.
Basheer ya harzuk’a zuciyarsa ta kawo ga wuya yace”idan baki fice ta lalama kika bani wuri ba kin wuce ta tsiya!”.
“kataimakeni mahaifiyata zata iya mutuwa idan ba’a kaita as…….. “.Kafin ta k’arasa maganarta yah Basheer yazo yaja hannunta k’ik’ik’ik’ik’i kamar karya tana turjewa sai fad’in yake “zanci ubanki karuwar banza k’ona gari!”.
Itama tana turjewa tana kuka k’annenta Hakeem yana kukan rad’ad’in abinda akeyiwa Addarsa, Haseena sai kuka takeyi tana cewa”ka k’yaleni ba wurinka nazo ba”.
“bazan tab’a k’yaleki ba sai kinbar wurin nan d’iyar matsiyata kawai! “.
Hak’ik’a Haseena taji zafi da rad’ad’in walak’ancin da yah Basheer yayi mata wanda har abada baxata tab’a mantawa dashi ba, bai k’yaleta ba saida ya fitar da ita daga cikin kasuwar yakaita har wani b’angare daban,yakaita ya yassuwa k’asa sannan yaja tsoki mtsssss yayi tafiyarsa batare daya ko waiwayosu ba, Haseena da Hakeem sun dad’e zaune sunata rusar kukan bak’in da ban tausayi dak’yar suka tsagaita dayin kukansu suka nufi hanyar zuwa gidansu.
Sunyi tafiya mai d’an nisa saigasu abakin k’ofar wani rusasshen gida ginin k’asa ko’ina ka duba ak’ofar gidan kwata ce mai shegen wari da d’oyi ,suna isa tsakiyar gidan na hango wata mace kwance saman cinyayyar tabarma lullub’e take da raggan zane jikinta sai mazari da kad’uwa yakeyi karrrr karrrr karrrr,da sauri su Haseena suka isa wurin matar tareda yaye mata lullub’in dake jikinta suna mata sannu, taimaka mata sukayi ta tashi zaune Hakeem ya shiga cikin d’aki ya d’auko mata pillow ta jingina jikinta akansa.
Nishi takeyi tana lumshe idanunta alamar ciwon yakai mata mak’ura, hawaye masu zafi suka wanke fuskar Haseena ta kalli mahaifiyarta tace”sannu Inna ubangiji ya baki lafiya”.
Hakeem d’an shekara goma yace”amin Adda”.
Mahaifiyarsu ta kalli Haseena tace”Haseena kun samu taimakon ko kuwa har yanzu babu wani nasara?”.
Cikin mutuwar jiki Haseena tace”Inna duk inda kike tsammanin zamu samu taimako to munje amma babu nasara, wuri na k’arshe da mukaje shagon hamshak’in d’an kasuwa nan Alhaji Tasi’u Garzali muna isa muka iske wani matashin saurayi shine yak’i bari mu gansa tareda yi mana korar kare kamar dabbobi! Wai miyasa masu kud’in yanzu mafi akasarinsu basuda zuciyar imani da taimakon talakawa gashi yanxu adalilin talauci mu shiga cikin matsananciyar rayuwa?”.
Inna Ik’ilima ta bud’i baki dak’yar tace cikin rad’ad’in ciwo”Haseena kenan azamanin nan namu kowa yayi kud’i kansa ya sani sai iyalinsa taimako yayi k’aranci rashin imani ya yawaita, saboda haka ki cire komai azuciyarki da yardar Allah zan samu lafiya tashi ku shiga cikin d’aki k’anzo yana nan na jik’a da dakakken k’uli k’uli ku d’ata kuci”.