RASHIN SO Complete Hausa Novel

“to Inna kamar kinsan mu dawo da yunwa”.Inji Haseena.
“na sani mana ai ko yawon da kukeyi aiki ne”.Cewar Inna Ik’ilima.
“haka ne Inna Hakeem tashi muje muci abinci”.Inji Haseena alokacin ne ta mik’e tsaye Hakeem ma ya tashi tsaye direct cikin d’akin k’asa suka shiga, babu komai cikin d’akin sai tsummokara da yakutattar katifa duk ta k’anjame akan tsananin talauci, Haseena ta mik’e tsaye ta d’auko kwano ta kwad’a musu k’anzon da gayen zogale tasa maggi guda biyu tasa tareda gishiri, sannan tasa hannunta ta yamutse k’anzon da zogalen sannan suka fara ci hama-hama kamar mayunwata kallo d’aya zakayi musu ka gane suna cikin tsananin talauci da rashin mataimaki arayuwa, saboda tunda mahaifinsu malam Kabiru ya rasu dangi da ‘yan uwansa suka fita sha’aninsu babu wanda yake taimaka musu da ko k’wayar hatsi, musamman k’anen malam Kabiru Baffa Salihi ya kasance mai son kansa kuma azzalumi mara tausayi acikin lamurransa.
Su Hakeem suka cinye k’anzon tass tareda sud’e kwanon da suka ci k’anzon cikinsa, sannan suka fito daga cikin d’akin sukaje wurin randar ruwa suka d’iba sukasha harda yin gyashi alamar sun k’oshi, sannan Hakeem ya koma wurin mahaifiyarsa ya zauna yayinda Haseena ta d’auki tsintsiya ta share gidan tass sannan ta kwaso uban kwanoni da tufafin mahaifiyarta ta wankesu fess sannan ta shanya saman igiyar shanya, tsaye nayi na saki baki ina matuk’ar mamakin yadda yarinya k’arama ta kammala duka ayyukan nan kafin k’iftawa da bismillah, sannan ta dawo wurinsu suka cigaba da firarsu itada Hakeem k’anenta yayinda Inna Ik’ilima taketa fitar numfashin wahala, can ta kalli Haseena tace”ki tafi wurin babanki Salihi ki gani ko za’a samu kud’in gadonku ahannunsa saiya baki mu tafi asibiti “.Haseena ta zumb’ura baki tace”nifa Inna bason zuwa gidan Baffa Salihi nakeyi ba saboda duk lokacin da mutum ya shiga cikin gidansa sai yaci karo da walak’anci da k’ask’anci iri iri awurinsa da wurin matarsa “.”Hak’uri zakiyi ki daure kije ai duk yadda yake babanki ne sannan hannunki bai tab’a rub’ewa ki yanke kiyarsuwa “.Haseena tace”naji Inna na tafi”.”Yauwa d’iyar albarka sai kin dawo “.Inna tana rufe bakinta Haseena ta fice daga cikin gidan da sassarfa zuciyarta cunkushe da damuwa da bak’in cikin rayuwa………….
[11/27, 9:51 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????
*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sis Najer’art*
*PAGE 37*
Haseena tana fita daga cikin gidansu batayi tafiya mai nisa ba da k’afafunta ta isa k’ofar gidan baffa Salihi, kutsa kanta tayi ta iskesa zaune shida matarsa Inna madina gaishesu tayi suka amsa mata adak’ile fuskarsu k’unshe da tsananin tsana da k’iyayyar iyalin malam Kabiru,tun anan jikin Haseena yayi matuk’ar sanyi cikin yanayin damuwa da sanyin murya tace”baffa wurinka aka aikoni”.
Baffa Salihi da yake zaune agefen Inna madina ya bankawa Haseena uwar harara cikin tsana da tsananin *RASHIN SO* yace”lafiya mi munafukar uwarki ta aiko kizo ki gayamin!?”.
Inna madina ta bintsire baki kamar taga kashi tace”ai kasan gatanar gizo bata wuce kok’i banda rok’on tsiya babu abinda Ik’ilima ta iya! Sai kace mune muka kashe mata miji da zata damemu damu taimaka mata”.
Baffa Salihi yace”yi shiru madina barta ta fad’i sak’on da aka aikota, keee d’iyar *MAYYA* mi tace ki gayamin dan kutumar buro ubanki Kabiru!? “.
Jikin Haseena yana rawa da kad’uwa tace cikin tsoro da fargabar kada baffanta ya daketa”cewa tayi idan kanada kud’i ka taimaka ka bata so take taje asibiti saboda batada lafiya”.
Baffa Salihi ya juya ya kalli Inna madina yace”kinji sak’on marok’iya ko ai nasan batada aiki sai faman cewa ataimaka mata batada lafiya, kaza-kaza saboda ta iya iyamatikwati to ni ina ruwana da rashin lafiyarta ta mutu idan domin nine babu abinda ya shafeni!”.
“wannan maganar ai zancen banza ne batama kawo kallo ba, gani takeyi kamar Kabiru yabarwa d’iyansa gado alhali baibar musu komai ba illa tsakurarren gidan daya bar musu, Haseena ki gaya mata cewa akwai kud’i amma ko sisi ba za’a bata ba ubangiji yasa ciwon ya zamo ajalinta mu huta da masifa da anyagabu! “.Inji Inna madina.
Baffa Salihi yace”ai shine dallah ki fice mana daga cikin gidan nan kafin insa icce in rafkeki sai kin suma dan dorin uwarki!”.
Hawaye masu zafi suka gangaro afuskar Haseena ta gurfana agabansu saman gwiyoyinta tace”baffa Inna na rok’eku dan girman Allah ku taimaka ku tausayawa rayuwarmu idan baku bayar da kud’i aka kaita asibiti ba mahaifiyarmu zata iya rasa rayuwarta, wallahi muna cikin talauci da k’angin rayuwa!”.
“wato bazaki fice mana daga cikin gida ba ko!?”.
Baffa yana rufe bakinsa ya mik’e tsaye zumbur afusace ya nufi cikin kitchen ya rarumo k’aton icce ya b’oye abayansa,Haseena kanta aduk’e batasan abinda baffanta ya d’auko ba kuka kawai takeyi mai ban tausayi da tarin damuwa, baffa Salihi yana isowa wurinta da take gurfane ak’asa kawai kaji gwafff! Ya buga mata icce ajikinta ai saida ta wuntsila ta fad’i k’asa biffffff sannan ta zabura da k’arfi ta shek’a da gudu baffa Salihi ya bita da k’aton icce har waje.
Tuni Haseena tayi masa fintinkau saboda ba k’aramin gudu takeyi ba domin ganin ta ceci ranta, baffa Salihi yana ganin tayi masa nisa ya juyo ya dawo cikin gida yana sababi yana cewa”‘yar kan buro uba kai data tsaya dasai lahira ya fita jin dad’i,da har zakizo ki hanamin shak’atawa nida matata aini yaya Kabiru yabarmin annoba duniya madina! “.Yace tareda isowa wurinta ya zauna.
Inna madina tace”da ace ma tareda ya mutu shida Ik’ilima da yaransa da duk wasu abubuwa basu dinga faruwa, amma ace mutum ya damemu da yawan rok’o kamar mune muka d’aura mata ciwo! “.
“bar sheggu d’iyan Allah wadai nasan gobe bazata sake dawowa ba”.
“da mun huta”.Inji Inna madina.
____________________
Haseena data gudu daga cikin gidan baffa Salihi bata zarce ko’ina ba sai cikin gidansu tana kawowa ciki Inna Ik’ilima itada Hakeem saida suka zabura zasu gudu, dak’yar Haseena ta tsayar dasu tana haki da nishin gajiya sannan ta zauna ta kawo labarin irin abinda su baffa sukayi mata na walak’anci tana kuka, Inna Ik’ilima ta lallasheta tareda bata hak’uri akan zamantakewar rayuwar duniya .
Hak’ik’a abinda su baffa Salihi suka yiwa Haseena ya matuk’ar b’ata mata rai tareda sanya rad’ad’i da damuwa cikin zuciyarta, ga kuma zafin zaginta da suka dingayi babu dad’in ji sosai, haka suka kwana zuciyarsu cunkushe da bak’in ciki da k’uncin rayuwa sannan ga wata irin bak’ar yunwa dake nuk’urk’usar cikinsu, haka dai suka kwana suna juye-juye akan rashin kwanciyar hankali da tashin hankali mara misaltuwa.
Da safe da suka tashi daga barci garin kwaki da sugar suka siyo suka sha sannan Haseena ta gyare gidan tass tareda kwashe sharar takai bola, sannan ta shirya cikin tsofaffin tufafinta da suka kod’e akan tsufa, sannan ta kalli fuskar mahaifiyarta tace”Inna zan tafi in gani ko zan samu damar ganin Alhaji Tasi’u in sanar masa halin da ake ciki”.
Inna Ik’ilima ta nisa dak’yar tace”to ubangiji yasa ki gana dashi”.
“amin Inna”.
Zata wuce kenan Hakeem ya mik’e zumbur ya isa wurinta yace”Adda ina zuwa”.
Haseena ta shafi kansa cikin k’aunar d’an uwanta tace”kayi zamanka kaji Hakeem yanzun nan zan dawo karka damu”.
Hakeem ya b’ata fuska yace”to Adda naji”.
“yauwa k’anena shiyasa nake sonka saboda kana jin maganata”.
Tana k’arasa maganarta ta fice daga cikin gidan ta nufi hanyar zuwa shagon babban attajirin nan Alhaji Tasi’u dake cikin tashin kud’i awannan lokaci.