RASHIN SO Complete Hausa Novel

Tafe take ak’afa duk ta gaji da tafiyar k’asa kallo d’aya zakayi mata ka gano tana buk’atar taimako da agajin gaggawa, babu dad’ewa ta isa adai dai wurin data had’u da yah Basheer ganin bata ganeshi ba yasa taji hankalinta ya kwanta ta k’ara gaba kenan kanta yana noce ak’asa, gwafff taji tayi karo da mutum kusan atare suka dafe goshinsu alamar sunji ciwo, d’agowar da idanunta zasuyi idanunta ya fad’a cikin na Basheer gabanta ya fad’i rasssss zuciyarta ta girgiza hankalinta ya d’unguma sosai, ganin itace yarinyar daya tsana arayuwarsa yasa ya harzuk’a b’acin rai da tsantsar bak’in ciki ne shimfid’e afuskarsa,bai tsaya dogon nazari ba ya kwasheta da gigitattun maruka biyu masu k’yau da zafi! Wani irin k’ara Haseena ta saki ta durk’ushe ak’asa dafe da kuncinta tana hawayen k’unci da rashin gata.
Sa k’afafunsa yayi ya shureta ta fad’i k’asa d’immmmm kanta ya gwaru ga dutse rikitaccen zafi da rad’ad’i ne ya ziyarci sassan jikinta da k’wak’walwarta!.
Tana kwance ak’asa tanata kukan bak’in ciki yah Basheer ya iso wurinta yace”idan baki daina zuwa inda nake ba wata rana nine ajalinki shegiya mara k’yawo mummuna mai bak’ar fuska! “.Yana k’arasa maganarsa yayi tafiyarsa yabarta kwance cikin mayuwacin hali, tana kwance ta kasa tashi tsaye saida wani bawan Allah ya gifto yaganta cikin matsanancin yanayi ya taimaka ta tashi tsaye tareda bata k’yautar dubu biyar ya wuce, ta dad’e tana kwararo masa addu’o’in gama lafiya da duniya sannan dak’yar taja k’afafunta tayi gida domin kada Basheer ya dawo ya isketa.
Tana isa Inna Ik’ilima ta tambayeta ko andace Haseena ta gaya mata gaskiyar abinda ya faru, har azuciya Inna bataji dad’in yadda Basheer yake walak’anta rayuwar d’iyarta ba saidai ta fawwalawa Allah lamarinta tasan komai yake faruwa dasu k’addara ce, sannan basu isa su kaucewa k’addararsu ba kud’in data samu k’yauta ta mik’awa mahaifiyarta domin ta ajiye su samu abinda zasu iya ciyar da kansu, haka dai suka cigaba da rayuwarsu cikin gidan babu wani mai taimakonsu sai ubangiji rayuwa ta juya musu ciwon Inna Ik’ilima sai habb’aka yakeyi, yayinda take nuna dauriya afuskarta domin kada ta tayar da hankalin yaranta amma tsakar dare ciwon baya bari ta runtsa har sai gari ya waye take samu ta d’an runtsa koshi bata dad’ewa da fara barci ciwon ya dinga sanya mata zafi da rad’ad’in jiki.
Bayan kwana biyu Haseena ta sake komawa wurin ganin Alhaji Tasi’u ko yanzu bata samu damar had’uwa dashi ba, har ila yau da Basheer ta sake had’uwa awannan karon matsiyacin duka yayi mata saida ya barta kwance tana fitar da numfashin galabaita sannan yayi tafiyarsa ya barta rai ahannun Allah, taimako ta samu aka kwasota aka kawota har bakin k’ofar gidansu kwatsam!Idanunta ya sauka ga cinciridon mutane gasunan birjik ako’ina sun d’auko gawa cikin makara zasu kaita mak’abarta, wanda ya kawota yayi tafiyarsa zuwa inda zaije zuciyar Haseena ta cigaba da bugawa da k’arfi fasss yayinda taji hankalinta yayi k’ololuwar tashi sosai agefenta taji mutane suna cewa “Allah sarki rai bak’on duniya ubangiji ya jik’anki Ik’ilima yakai haske kabarin………”.
Bata bari suka k’arasa maganarsu ba ta fashe da rikitaccen kuka da kuwwa ta fad’i k’asa tana birgima kamar mahaukaciya tace”wayyo Allah! Na shiga uku na lalace mahaifiyata ta rasu yanzu ya zanyi da rayuwata? Wadda nake tink’aho nake kallo inji sanyi araina ta tafi ta barni cikin duniyar nan mai cikeda bak’in cikin rayuwa da rashin gaskiya! “.Dandazon mutane sukayi tsaye suna kallonta cikin tausayawa da tsantsar damuwa wad’anda suke d’auke da gawa suka gifto ta gabanta zasu wuce kenan Haseena ta zabura ta rik’e makara tana cewa “wallahi k’arya kukeyi Innata bata mutu ba saboda haka babu inda zakuje da ita da ranta ku binneta cikin k’asa! “.Ganin yadda take zabure zabure ta rik’e makara yasa maza hud’u suka b’anb’areta dak’yar daga wurin makarar cikin tsananin tausayi, sauran suka wuce da gawar Inna Ik’ilima domin akaita makwancinta na gaskiya.
Bayan an wuce da gawar Inna Ik’ilima zuwa mak’abarta Haseena ta shige cikin gidansu da gudu tana kukan k’unci da bak’in cikin rayuwa, acan cikin d’aki ta hango Hakeem rakub’e wurin katifa yanata risgar kukan maraici Haseena ta isa wurinsa ta rungumesa ajikinta tana cewa”kayi hak’uri k’anena ka daina kuka domin dukkan mai rai mamaci ne”.
“ya zamuyi Adda iyayenmu duka sun mutu bamuda wanda zaiji tausayinmu ya d’auki nauyinmu! Yanzu haka zamu cigaba da rayuwa cikin k’unci da uk’ubar rayuwa”.
Hawaye masu zafi suka cigaba da shatata afuskarta bubbuga bayansa takeyi cikin lallashi da tausayi tace”ka daina fad’ar wannan maganar Hakeem ubangiji shine ya bamu su Inna Ik’ilima amatsayin iyaye sannan daga baya ya amshi ransu, to ya zamuyi idan ba hak’uri ba dukkan abinda ya faru damu rubutacce ne awurin ubangiji domin ya gwadamu yaga ko zamuyi hak’uri “.Hakeem yayi doguwar ajiyar zuciya yace “naji Adda gidan wa zamu koma kwana da dare kinsan kwana cikin gidan mu kad’ai hatsari ne? “.Jaye jikinta tayi cikin nasa tace “bari yanzu muje gidan baffa Salihi mu rok’i alfarmarsa akan yabarmu mu dinga kwana agidansa”.Hakeem kamar zaice mata kar suje baffa ba k’aunarsu yake ba amma gudun matsala yaja bakinsa yayi shiru, Haseena ta chanza kayan jikinta taja hannunsa suka fice daga cikin gidan suka nufi hanyar zuwa gidan baffa Salihi…………
[11/27, 10:05 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????
*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sis Najer’art*
*PAGE 38*
Su Hakeem suna isa cikin tsakiyar gidan baffa Salihi sukayi sallama Inna Madina tana zaune itada baffa ko kallonsu basuyi ba bale su amsa musu sallama, isowa wurinsu Inna Madina sukayi suka gaidasu alokacin ne baffa ya b’ata fuska yace”lafiya zaku shigo mana cikin gida ko bashi kuke biyanmu!?”.Inna Madina ta bintsire baki tace”ai shine na gani zakuzo kuyi gurfane kamar masu rok’on gafara!”.
Bakin Haseena yana rawa tace”baffa da….ma wa…ta alfar…ma… ce mu..ke ne..ma “.
Baffa Salihi ya hararesu yace”fad’i alfarmar inji don ubanki kafin in fatattakeku kubar mini gidana!”.
“wai dama taimako muke nema tunda mahaifiyarmu ta rasu mu dinga kwana da dare gidanka da rana da marece duk muna cikin gidan babanmu”.
Inna Madina ta katsa musu tsawa tace”sam!Bazai tab’a yiyuwa ba ayanzu kuka sanmu ada lokacin iyayenku suna raye ko kallon arzik’i bakwa yi mana, saboda haka ku tashi ku b’ace mana da gani kafin inci gidanku!”.
Baffa ya dubeta yace”kwantar da hankalinki Madina ko bakice subar mana gida ba nizan koresu! “.
Ya juya ya kallesu cikin tsananin tsana da k’iyayya yace”kuuu tashi ku barmin gidana ko yanzu jikinku ya gaya muku! “.Ya fad’a cikin hargowa.
Jikinsu Haseena yana makarkatar tsoro da mazari suka tashi suka fice daga cikin gidan da saurinsu.
Inna Madina tayi k’yafci cikin hasala tace”sakarkarun banza haka kawai zaku kwaso jiki kuzo ku cinye mana tuwo saboda tsabar kwad’ayi”.
“bar d’iyan banza waye zai zauna dasu su tauyewa mutum rayuwa,amma ki k’yalesu kawai nasan matakin daya kamata in d’auka akansu”.
“maigida ya kamata ka d’auki mummunan mataki akansu kada suzo su hana mana jin dad’i mu bada haihuwa ba”.
“shakuruminki Madina kedai ki zuba idanu kiyi kallo zakiga abinda zai biyo baya”.
“nayi shiru maigida”.
____________________
Haseena suna komawa gidan iyayensu suka zauna suka sha kukansu saida suka k’oshi, sannan daga k’arshe Haseena ta share gidan tass da tsintsiya ta jawowa Hakeem ruwa arijiya yayi wanka yana fitowa daga cikin toilet, itama ta shiga tayi wanka sannan ta shirya cikin tsohuwar atamfarta gari ta jik’a ta daka k’uli k’uli acikin turmi suka kwad’a suka ci suka k’oshi sannan suka sha ruwa.
Suna zaune cikin gidan sunyi jugum babu mai magana saboda kowa da abinda yake tunani cikin zuciyarsa, idan lokacin sallah yayi sai su tashi suyi alwala suyi sallah haka sukeyi har dare yayi suka kwanta saman katifa.
Da tsakar dare misalin k’arfe d’aya da rabi na dare 1:30am su Haseena suna kwance suna barci da minshari, kwatsam!Wuta ta fara kamawa saman katako harta fara ci balbalbal hayak’i ne ya turnuk’e d’akin gaba d’aya kamar an tsikari Hakeem ya tashi zaiyi fitsari yaga wuta, da sauri ya tayarda Haseena daga barci yana cewa”Adda!Adda!!Adda!!! Gobara ki tashi mu gudu”.
Kamar amafarki Haseena taji an kira sunanta ta mik’e tsaye zumbur cikin magagin barci tace”mun shiga uku rayuwarmu tazo k’arshe Hakeem zo mu fita daga cikin wannan wutar kafin kwananmu ya k’are! “.
Hakeem ya mik’e tsaye zumbur shima itace ta shiga gaba yana bayanta har suka fice daga cikin gidan! Nesa da gidan suka tsaya suna ji suna gani ya k’one k’urumumus kamar ba’a tab’a gina awurin ba!.
Suna tsaye sukaga matasan samari guda hud’u sunyo wurinsu gadan gadan hannayensu rik’e da makami, su Haseena suna hankalce dasu ai kuwa babu b’ata lokaci suka shek’a da gudu yayinda samarin suka biyo bayansu, gudu sukeyi domin ceton ransu su kuma suna binsu saboda su cimmasu su kashesu, haka dai suka cigaba da gudu ana biyarsu abaya.
Sunyi gudu sosai har sun galabaita Hakeem ya fara gajiya sosai ya tsaya yace”Adda na gaji da gudu da wannan bala’i gwamma mutuwa akan rayuwa”.
Haseena taja ta tsaya tana haki tace”ka daure Hakeem mu tsira da rayuwarmu wad’annan mutanen da kake gani ba imani ne dasu ba idan suka riskemu anan zasu iya kashemu!”.
“na gaji da gudu bazan iya kuwa ko’ina ba Adda kiyi tafiyarki”.
Hawaye masu zafi suka gangaro daga idanunta ta girgiza kanta tace”a’a Hakeem bazan iya tafiya inbarka su kasheka ba saidai su kashemu atare!”.
“kiyi tafiyarki Adda banason su cutar mini dake! “.
Haseena ta juya ta hango matasan samarin suna k’araso wurin inda suke, kallon Hakeem tayi tana kuka tana rok’onsa tace”sun kusa zuwa inda muke Hakeem dan girman Allah ka daure kazo mu tafi kai kad’ai ka ragemin arayuwata banida kowa iyayenmu duk sun riga sun mutu”.
“hak’uri zakiyi Adda ki ceci rayuwarki domin kada mu mutu alokaci guda tabbas wata rana zaki d’aukar mana fansar duk wanda yakeda sa hannu cikin cutar da rayuwarmu”.
“nayi maka alk’awarin duk wanda yakeda sa hannu cikin wannan halin da muka shiga saina d’aukar mana fansa! “.Tana rufe bakinta saiga samarin su k’araso wurin Hakeem Haseena ta shek’a da gudu ta kuka kamar zata shid’e akan bak’in ciki da k’uncin rayuwa, tana waigowa taga sun dab’awa Hakeem wuk’a aciki saida ta lume cikin cikinsa ya fad’i k’asa yana kakarin mutuwa, gigitaccen kuka mai cikeda k’unci ta saki domin tayi mugun ganin da har abada baxata tab’a mantawa dashi ba domin samarin sun cutar da rayuwarta da tarwatsa zuciyarta!.