RASHIN SO Complete Hausa Novel
*********************
Saliha taba Rayyanu ya siyowa Naja’atu sugar da k’osai akatangar gidanta ta kirasa ta amshi sak’onta, tana amsawa ta shiga cikin room d’inta ta zuba cikin kunun data had’a d’ibawa Rufaida nata tayi ta bata tareda k’osai, ita kuma taci nata itada d’anta Suhail dayake ya fara cin abincin tuntuni, tana kammala karyawa ta kwashe kayayyakin da suka b’ata ta wankesu fess ta adana cikin kwandon zuba kwanoni.
Tana gama wanke-wanke saiga sallamar yaro Masa’uda ta aikoshi da wankinta, Naja’atu ta amshi k’unshin wankin da kud’in da Masa’uda taba yaron yaba Naja’atu tana amsar wankin yaron ya fice daga cikin gidan, fitowa Naja’atu tayi rik’e da k’unshin wankin ta nufi wurin famfon gidansu dake tsakiyar filin gidan tana isa ta tara bucket da babbar roba abakin famfo,bokitin yana cika Naja’atu ta bud’e kayayyakin Masa’uda cikin wankin taga sabulun wanki da klin ta fara wankin tufafin cikin kwanciyar hankali.
Tana wankewa idan ta wanki kamar kala hud’u saita d’oraye cikin ruwa ta shanya saman igiyar shanya, haka dai ta cigaba dayi harta kusa kammala wankin tana zaune saiga Haseena ta fito daga cikin d’akinta tana yamutsa fuska cikin tafiyar gadara,panties da bra d’inta data wanke atoilet ta fito dasu ahannunta direct wurin igiyar shanya ta nufa ta shanyasu ganin Naja’atu tana wanki yasa tayi mata walak’antaccen kallo tace”‘yar gawanki wanki ne akeyi yanzun nan kuma!?”.
Maganar ta soki k’ahon zuciyarta sosai wani irin rad’ad’i da d’aci ne ya ziyarci sassan jikinta da k’wak’walwarta amma dayake ta iya siyasa bata nuna b’acin ranta ko afuska ba, murmushi ta sakar mata tace”eh gawanki na samu aka kawo mini Haseena”.
Bintsire baki tayi tace”hmmm agaskiya baki k’yautawa Basheer ba taya kina matar malamin makaranta kikeyin ga wanki, salon ki jawa mijina zagi agari wannan bai dace ba!”.
Mamaki da takaici ne ya shimfid’u afuskar Naja’atu k’arfin hali tayi ta kauda komai cikin ranta tace”Haseena maganarki gaskiya ta bani mamaki taya zaki fad’i irin wannan maganar mai matuk’ar d’aci, har zaki bud’i baki kice ina b’atawa Basheer suna agari bayan kinsan baya bani hak’k’ina dake rataye awuyansa, daga ni har yarana baya kulamu to idan ban nemi na kaina ba karuwanci kikeson inje inyi in nemo mana abinda zan ciyar da yarana in kula da lafiyarsu?”.
Haseena tace”ai ko baya baki ci da sha bai kamata kiyi gawanki ba wannan ai zubar da girma ne da k’ask’anci!”.
Naja’atu ta cire hannunta daga cikin robar wankin tace”karki yiwa sana’ar gawanki mummunan fahimta Haseena,kowace irin sana’a zan iyayi domin ganin na tseratar da mutuncina dana yarana kina zaune cikin gidan nan kina ganin irin abubuwan Basheer yakeyimin na tasku da walak’anci! Rana d’aya ban tab’a jin kinyi masa nasihar ya daina yimin irin abubuwan da yakeyimin saboda kinga yana baki kulawa da nuna miki tsantsar soyayyar gaskiya,nima fa da kike gani auren soyayya mukayi dashi tun yana saurayi ina budurwa amma ban tab’a zato ko tsammanin soyayyar da yakeyimin ba zata juye ta koma *RASHIN SO* !”.
Haseena ta gyara tsayuwarta tace”babu abinda ya shafeni akan lamarinki keda mijinki tare nazo na taras daku bansan musabbabin abinda ya had’aku ba, saboda haka babu wata nasihar da zanyi masa idan yaga dama ya gyara rayuwar gidansa idan yaga dama kada ya gyara wannan ba damuwata bace!”.
“dole kice haka saboda bake yake walak’antawa ba ni yake yiwa, amma inason ki sani duk inda shanuwar gaba tasha ruwa ko ta baya can zata nufa”.
“wannan ya rage naki Naja’atu!”.
Haseena tana gama fad’ar maganarta taja k’afafunta tayi tafiyarta tana girgiza k’ugu da karkad’a jikinta.
Cikin d’acin rai Naja’atu ta share hawayenta ta cigaba da yin wankinta harta k’arasa wankin ta shanya saman igiyar wanki, zuciyarta sai suya da tafasa takeyi mata wanke hannunta tayi ta mik’e tsaye cikin sanyin jiki ta nufi cikin d’akinta.
******************
Naja’atu tana shiga cikin d’akin ta watsa ruwa ajikinta tana fitowa ta sanya doguwar rigarta, kwantawa tayi na d’an lokaci can ta tashi zaune ta dubi agogo taga azahar ta kusa mik’ewa tsaye tayi ta shiga cikin bathroom ta d’auro alwala, tana fitowa ta shimfid’a sallaya ta d’auko qur’ani ta fara karatu cikin zazzak’ar muryarta ta jima kad’an aka kira sallar azahar, tashi tayi ta kabbarta sallah raka’a hud’u tayi sannan taja casbaha tana gama ja ta fara kwararo addu’o’in neman sassauci azuciyarta, hawaye masu zafi sai shatata sukeyi asaman k’yakk’yawar fuskarta wani irin k’ololon bak’in ciki da takaici sai taso mata yakeyi a k’irji,ta jima zaune tana kai kukanta wurin Allah sannan daga baya ta shafa addu’ar afuskarta tareda linke sallaya ta adanata awurin da take ajiyewa.
Tana tsaye kafin ta zauna saiga sallamar Saliha ta shigo cikin d’akin kai tsaye, amsa sallamar tayi ta juyo ta kalli Saliha fuskarta asake kamar babu abinda yake damunta, zaunawa Saliha tayi ga cushion d’in dake cikin d’akin tace”Naja’atu nazo ne domin muyi wata muhimmiyar shawara dake”.
Naja’atu ta mayarda hankalinta kacokam wurin Saliha tace”ina saurarenki Aminiyata”.
Gwauron numfashi ta sauke tareda yin shiru na d’an lokaci can tace”kud’i ne nazo dasu dubu hamsin zan ara miki kija jari ki samu na tallafawa kanki da yaranki,saboda gawanki bazai baki kud’i masu yawa ba wanda zaki iya d’aukar lalurorinku keda yaranki”.
Naja’atu tace”kina ganin yin sana’a shi yafi dacewa awurina?”.
“tabbas shi yafi dacewa saboda kinga bai dace ace kodayaushe kina hanyar zuwa gidanku su Baffa suna baki ba, kamata yayi ki tsayu saman k’afafunki domin ganin kin inganta rayuwar ‘ya’yanki da kanki”.
Idanunta ne suka cicciko da hawayen tausayin kanta da farin ciki alokaci guda Naja’atu ta dubi Saliha tace”nagode sosai da fitar dani da kikayi daga cikin k’angin rayuwa banda abinda zan iya saka miki dashi sai dai inyi miki addu’ar gamawa lafiya da duniya Aminiyata”.
Saliha ta girgiza kanta cikin tausayinta tace”ki daina yimin godiya Naja’atu mun riga mun zama k’awayen juna kuma duk abinda nayi miki nayi miki ne saboda Allah da k’aunar dake tsakaninmu, sannan kiyi tunanin irin sana’ar daya kamata kiyi”.Mik’a mata kud’in tayi Naja’atu ta amsa cikin sanyin jiki tana kallon kud’i masu yawa haka wai acikin hannunta.
Naja’atu tana amsar kud’in ta saka cikin k’aramar jikkar da take ajiye ‘yan kud’ad’en da take samu idan tayi gawanki ko surfen hatsi ko kuma idan taje gidansu ziyara yayanta Hamid ya bata.
Kallon Saliha tayi da murmushi afuskarta tace”wace irin sana’a kikaga ya dace inyi?”.
Saliha ta gyara zamanta tace”ki fara saida kayan miya yafi miki sauk’i”.
“ba matsala insha Allahu zan fara?.Inji Naja’atu .
Saliha ta mik’e tsaye tace”ni zan wuce gida Allah ubangiji ya sanyawa sana’arki Albarka Aminiya”.
“amin”.Acewar Naja’atu.
Itama Naja’atu ta mik’e tsaye domin ta rakata har waje fitowa sukayi daga cikin room d’in suna tafiya suna fira cikin natsuwa, suna isowa tsakiyar filin gidan suka iske Haseena zaune tana dafa shinkafa da miyar tumatur taji naman rago acikinta k’amshin girkin duk ya gauraye ciki da wajen gidan, suna isowa wurinta Haseena ta kauda kanta gefe tayi kamar bata gansu ba domin har azuciyarta ta tsani ganin Saliha tana zuwa wurin Naja’atu, babu yadda ta iya ne amma tayi alk’awari azuciyarta wata rana sai ta shukawa Saliha rashin mutunci, tunanin da takeyi ne ya katse saboda gaisuwar da Saliha tayi mata taji ance”sannu da aiki Amarya”.
Adak’ile ta amsa domin ganin ta b’oye damuwarta da b’acin ranta tace”yauwa munafi!”.Tana sokawa Saliha magana mai zafi ta juyar da kanta gefe kamar ba itace tayi maganar ba.
Kalmar munafi data kira Saliha dashi abin yayi matuk’ar yi mata ciwo azuciya amma bata nuna mata komai afuska ba, murmushi kawai Saliha ta sakar mata suka rankaya suka fice daga cikin tsakiyar gidan, hak’ik’a murmushin da Saliha tayiwa Haseena ya matuk’ar bata haushi da jin wani irin d’aci da k’ololon bak’in ciki azuciyarta, musk’utawa tayi ta hasala ta k’udurta abubuwa da dama cikin zuciyarta……..
[11/18, 6:11 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????