HAUSA NOVELRASHIN SO Complete Hausa Novel

RASHIN SO Complete Hausa Novel

Sannan ta cigaba faffalawa da gudu harta b’acewa ganin matasan samarin, gudu takeyi batama san inda take jefa k’afafunta ba har taci karo da mota saura kiri’s mai motar ya kwasheta ya taka birki da k’arfi tareda fitowa daga cikin motar idanunsa yayi tozali da yarinya wadda bata wuce 15years ba, jikin Haseena yana rawa ta isa wurinsa tana kuka tace”bawan Allah ka taimakeni kamar yadda Allah ya taimakeka wasu ne suke bibiyata zasu kasheni! “.Bawan Allah mai suna Nasir yace”su waye zasu kasheki!? “.”Yanzu ba lokacin tambaya bane kaidai ka taimakamin daga baya zan sanar maka labarin rayuwata”.”OK ba damuwa”.Ya bud’e mata k’ofar gaban motar ta shiga cikin motarsa shima ya koma gefen driver ya zauna tareda tadda motar suka nufi wata unguwar daban wadda take nesa da gari, suna wucewa saiga matasan samari sun iso wurin sukayi dube dube ko mai kamada Haseena basu gani ba, sannan suka juya sukaje gidan baffa Salihi suka gaya masa sun kashe Haseena da Hakeem baffa Salihi yayi matuk’ar farin ciki da murna mara misaltuwa, ya basu dubu hamsin suka k’ara gaba shi kuma ya shige cikin gidan domin ya sanarwa Inna Madina burinsu ya cika.
____________________

Nasir bai zarce ko’ina da Haseena sai akatafaren gidansa wanda ya had’u da k’awatuwa fiye da tunanin mai karatu da kansa ya wangale musu get d’in, domin bayada maigadi sannan ya danna hancin motarsa acikin gidan ya parker aparking lot shi ya fara fitowa sannan ya bud’e mata k’ofa ta fito, yana gaba tana biye dashi har suka shiga cikin parlourn suka zauna, bayan ta huta ta samu natsuwa ya kawo mata abinci taci tasha ruwa sannan ya tambayeta labarin rayuwarta,Haseena tana kuka ta kawo labarin duk irin gwagwarmaya da masifun da suka fuskanta arayuwarsu hak’ik’a Nasir ya tausaya mata tareda zubar kwallar zallar takaici da haushin abinda Baffa Salihi yayi musu, bata hak’uri yayi tareda nuna mata zai taimaketa ya rik’eta amana bisa gaskiya .

Haka rayuwar Haseena ta cigaba da tafiya agidan Nasir wanda yake rayuwa shi kad’ai agidansa, haka suka cigaba da zama gida d’aya tamkar mata da mijinta, Nasir yana tsananin kulawa da ita da nuna mata tsantsar soyayyar gaskiya acikin haka ne shak’uwa da soyayya mai k’arfi ta shiga atsakaninsu, duk dayake Haseena batasan ko wa nene Nasir ba sannan wace irin sana’a yakeyi, babu wanda ko wadda ke shigowa cikin gidan kud’i kuwa awurin Nasir kamar ledar pure water duk abinda takeso shi take ci da kuma sanya suturar da duk taga dama, lokacin da Haseena takai 18years Nasiru ya bijiro mata da maitarsa afili babu yadda ta iya dole ta bashi had’in kai suka fara sanin dad’in juna, tun daga lokacin da yasan dad’inta shikenan ya maidata kamar matarsa aduk lokacin daya gadama yana iya biyan buk’atarsa da ita, acikin haka ne ya sanyata a cikin k’ungiyarsu ta matsafa itama ta zamo ‘yar mafiya.

*WA NENE MAHAIFIN HASEENA*
Mahaifin Haseena shine malam Kabiru mahaifiyarta Inna Ik’ilima auren soyayya ne sukayi itada mijinta Malam Kabiru, ita Inna Ik’ilima ita kad’aice awurin iyayenta yayinda Kabiru shida k’anensa Salihi .
Lokacin data auri Kabiru bata fuskanci komai ba azamantakewar rayuwar aurensu ba domin yana tsananin sonta da bata kulawa na musamman, bayason b’acin ranta ko kad’an arayuwa amma Salihi azuciyarsa babu wanda ya tsana fiyeda yayansa domin ganin cikin k’ank’anin lokaci ya samu ‘yan kud’ad’en dazai rufawa kansa asiri da iyalinsa,hassada da k’yashi ne yake wanzuwa azuciyar Salihi domin ya tsani yaga wani yafishi arayuwa shiyasa yake hantar Ik’ilima da tsangwamarta ko ta kawo masa abinci yake barinta dashi.
Yasha zaginta agabanta tana sharesa domin ta fahimci bak’in ciki kecin zuciyarsa, haka dai ta cigaba da hak’urin halayyar Salihi na rashin mutunci da walak’anci iri iri daban daban harta haifi d’iyarta Haseena, dayaga ta haifi mace bai wani damu ba duk baiso ace Inna Ik’ilima tana haihuwa ba, tunda ta haifi Haseena bata koma samun ciki ba saida Haseena takai shekara biyar wanda alokacin tuni Salihi ya auri Madina,Inna Ik’ilima tana d’auke da cikin Hakeem wata biyar Allah ubangiji yayiwa mijinta Kabiru rasuwa, aranar karkuso kuga bak’in ciki afuskar Inna Ik’ilima har suma sau biyu tayi ana watsa mata ruwa tana farfa’dowa .

Tun lokacin da mijinta ya rasu ta fara fuskantar k’yara, tsangwama, walak’anci, tasku, cin amana da rashin so arayuwarta haka dai take takure zaune cikin gidan harta haifi d’anta Hakeem ,ganin ta haifi d’anta namiji yasa tsana da hassada ya k’ara ninkuwa azuciyarsu Baffa Salihi, cigaba da azabtar da Inna Ik’ilima sukayi itada yaranta har suka kai mizanin girma suka tasa, daga baya baffa Salihi ya sace kud’in gadonsu Haseena ya gina nasa gida suka tare shida matarsa Madina, haka dai ya cinye musu kud’in gado har ciwo ya kwantar Inna Ik’ilima wanda ya zamo ajalinta, tunda ta kwanta rashin lafiya Baffa Salihi yake yawan zarya gidansu yana ci mata mutunci tareda d’ebe mata albarka, babu irin walak’ancin da baiyi musu ba arayuwa sunga k’iyayya da *RASHIN SO*.
___________________
Ab’angarensu yah Basheer alokacin har yayi aurensa da Naja’atu yaso Naja’atu kamar yayi hauka cikin ikon Allah akayi aurensu cikin rufin asiri da wadatar zuci, hmmmm sunyi matuk’ar soyayya arayuwar aurensu domin kowanensu yana k’ok’ari wurin ganin ya farantawa abokin zamansa Basheer ji yakeyi da matarsa kamar tsokar miya, Naja’atu ta riga ta iya tafiyar da rayuwarsa domin biyayyar da takeyi masa ta wuce misali.

Haka suke gudanar da tsabtacciyar rayuwar aurensu cikin so da k’auna matuk’a, babu tashin hankali sai tausayi da k’aunar juna haka ta samu cikin Rufaida zo kuga murna da farin ciki sosai afuskokin wad’annan bayin Allah, yah Basheer ya ninka wurin bata kulawa da tarairaiyarta hundred percent kuma duk abinda takeso shi take ci da kuma yin yadda take ra’ayi, haka dai suka cigaba da rainon cikin har ya isa haihuwa ta haifi santaleliyar d’iyarta mace taci suna Rufaida, sunyi matuk’ar godiya da farin cikin k’yautar da Allah ya basu suka cigaba da rainon diyarsu cikin so da tsagwaron soyayyar gaskiya, rayuwa ta cigaba da yin tafiya har Naja’atu ta sake haihuwar d’anta namiji Suhail .
Zaman lafiya sukeyi itada yah Basheer bata tab’a fuskantar k’alubalen rayuwa ba sai wata rana, bayan yah Basheer ya fita zuwa super market yayi siyayya anan ne ya had’u da wata k’yakk’yawar budurwa black beauty ma’ana ya had’u da Haseena, farat d’aya da idanunsa yayi tozali da fuskarta yaji ya kamu da matsananciyar soyayyarta baiyi nauyin baki ba ya sanar mata sirrin dake ransa, dayake Haseena ta fahimci shine yayi mata walak’anci ashekarun baya har ya zamo silar mutuwar mahaifiyarta shiyasa bata tsaya jan aji ba, nan da nan ta amshi soyayyarsa sukayi exchanging numbers kowa ya kama gabansa……..
[11/27, 10:31 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sis Najer’art*

*PAGE 39*

 

Tun lokacin soyayya mai k’arfi ta k’ullu atsakaninsu ta yadda d’ayansu bazai iya rayuwa ba idan babu d’ayan, cikin haka ne Naja’atu ta fara fuskantar k’alubalen rayuwa saboda yah Basheer walak’anci da k’ask’anci iri iri yakeyi mata daga ita har yaranta ya daina basu kulawa da nuna musu tsantsar soyayyar gaskiya, tun anan Naja’atu ta fahimci soyayya mijinta yakeyi addu’ar shiriya ta dingayi masa akullum har yazo ta fara zubar kwallar k’unci da tarin damuwa.
Basheer babu ruwansa da damuwarta ko rashin lafiyarsu har ya fara shirye-shiryen aurensa batada labari, sai a mak’wabta cikin haka ne ya k’ara k’aimi wurin walak’antata tareda musgunawa rayuwarta baida abin tsana da tsangwama fiye da ita, haka Naja’atu ta tank’wari zuciyarta ta daure ta cigaba da zama agidan Basheer har yayi sabon aurensa shida matarsa Haseena.
Kamar kar yayi aure ya sake birkicewa ya zamo baya bawa Naja’atu ci, sha, sutura, sannan da hak’k’in auratayya ya manta da ita ashafin zuciyarsa walak’ancin yau daban na gobe daban na jibi daban, tana ji tana gani zaizo ya wuce ta gabanta da k’unshe leda ya shige d’akin amaryarsa Haseena.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button