RASHIN SO Complete Hausa Novel
Kafin Haseena ta auri Basheer saida suka samu matsala da saurayinta Nasir saboda yadda ya nuna mata bai amince ta auri Basheer ba, Haseena ta kallesa cikin sanyin murya tace”haba Nas kana tunanin idan na auri Basheer zanci amanarka ne?Ka fahimceni sosai masoyina na sanardakai zan auresa ne domin in d’auki fansar walak’ancin da yayimin arayuwata har ya zamo sanadiyyar mutuwar Innata”.
Nasir yace yana hawayen rad’ad’in rabuwa da ita”ina kishinki Haseena fiye da zatonki banason kowa yasanki ‘ya mace idan bani ba, amma tunda kin zab’i Basheer akaina babu damuwa nagode sosai”.Haseena ta rik’o hannunsa ta fashe da kuka mai ban tausayi tace”nayi maka alk’awarin dakai zan rayu Nas amma na rok’eka kabarni in cika burina idan ba haka zan iya mutuwa ka huta! “.Jin kalamanta yasa Nasir yaji tsoro hankalinsa yayi k’ololuwar tashi yace”ki daina cewa zaki tafi ki barni na yarda na amince ki auri Basheer, nayi alk’awarin zan taimaka miki domin ganin burinki ya cika masoyiyata”.Haseena ta fad’a saman faffad’an k’irjinsa tana kukan farin ciki tace”nagode da halaccin da kayimin arayuwa har abada bazan tab’a cin amanarka ba domin ka nunamin k’auna da tsantsar *SOYAYYAR GASKIYA*”.Shafar fuskarta yayi cikin so da shauk’in sonta sannan daga k’arshe suka biya buk’atarsu cikeda matuk’ar farin ciki da nishad’i.
_Dawowa cikin ainahin labari._
Haseena tana gama bashi labarin rayuwarta ta kallesa cikin b’acin rai da tafasar zuciya tace”saboda haka Basheer saina kasheka na d’auki fansar jinin mahaifiyata! Babu wanda ya isa ya kub’utar dakai daga kaidina sannan bud’e kunnenka da k’yau ka saurareni nice nan na kashe mahaifiyarka Hannatu nice na kashe d’anka Suhail bugu da k’ari nice nasa aka turawa ubanka Tasi’u ciwon zuciya wanda ya zamo ajalinsa, dukansu uku mun shanye jininsu wato abinda baka sani ba shine dalilin dayasa nayi galaba akanka ya samo asali ne saboda ka rabuda matarka Naja’atu, alokacin dana aureka shugaban matsafa ya sanardani cewa muddin kana tareda Naja’atu bazan tab’a cin galaba akanka ba shiyasa nabi duk hanyar data dace na ganin ka saki matarka kun rabu! Bayan kun rabu na samu nasarar tarwatsa iyayenka da hargitsa farin cikinka nasan har abada nayi maka mugun dafin da bazaka tab’a mantawa dani ba, nasan kuma zaka fahimci illar walak’anta rayuwar d’an Adam! “.
Basheer ya fashe da wani irin rikitaccen kuka ya gurfana k’asa agabanta yace”kiyi hak’uri Haseena kiyafemin tabbas nayi matuk’ar kuskure arayuwata amma ban cancanci irin wannan sakayyar agareki ba, idan kikayi duba da la’akari duk d’an Adam ajizine mai aikata kuskure saboda haka kada ki kasheni kibarni in rok’i gafarar Naja’atu”.
malam Haliru yayi tsagal yace yana kuka”karki kasheni Haseena banyi miki laifin komai ba Basheer ne ya cutar da rayuwarki ni banida masaniya akan abinda ya faru atsakaninku”.
Gigitacciyar tsawa Haseena ta daka musu cikin hargowa da rashin imani tace”kuyimin shiru banason jin komai abakinku ku sani har abada babu yafiya atsakaninmu! Saina kasheku sannan inje in kashe Baffa Salihi da matarsa babu sani babu sabo duk wanda yayi sai anyi masa! “.Tana rufe bakinta ta d’aga hannunta sama tana karanto d’alamisai na tsafi saiga wata irin mahaukaciyar tsawa da tartsatsin wuta sun bayyana fasss fasss fasss! Zad tsoro nan da nan duk jikinsu Basheer ya d’auki mazari da kad’uwa kafkafkaf zungureriyar wuk’a ce ta bayyana ahannunta, tsawa da tartsatsin wuta suka b’ace b’at kafin k’iftawa da bismillah Haseena ta nufi wurin Haliru da wuk’a ahannunta tsirara, malam Haliru yana ganin ta nufoshi ai sai ya rikice da rud’ewa akan tsabar tashin hankali da ganin mutuwa k’iri k’iri ga fili, zabura yayi zai shek’a da gudu kenan matsafa ‘yan uwanta suka damk’esa ya kasa kufcewa sai mutsul mutsul yakeyi tana isa wurinsa ta dab’a masa wuk’a aciki sauran sukayi sauri suka d’auko tukunya jinin Haliru ya fara zuba cikin tukunyar.
Haka suka fed’e masa ciki tareda sassare sassan jikinsa filla-filla gudunwa gudunwa, Basheer ya k’ara tsurewa da gigicewa domin ya k’ara tabbatarwa inda ya zaci rashin imaninsu ya zarce tunaninsa, haka sukayi tsubbace tsubbacensu da jinin Haliru kowa yasha yayi gyashi sannan suka dafa naman jikinsa da kayan ciki suka bawa murgujejen k’attin macizai guda hud’u masu fuskar bil’adama jikinsu jikin tsuntsaye domin har tashi sama sukeyi, sannan daga k’arshe suka d’auki yah Basheer suka kaishi inda suke ajiye mutanen da zasu sha jininsu, d’akuna garesu jajjere gasunan birjik ako’ina cikin gidan saboda gidan yana girma da fad’i fiye da misali.
**********************
*BAYAN WATA GUDA*
Basheer ne zaune na hango cikin mutanen da suke kamowa susha jininsu yayi bak’i ya k’anjame kamar bashi ba, kayan dake jikinsa duk sunyi daud’a akan wahala kansa anyi masa aski ya koma sumul-sumul, zaune yake hawaye suna kwaranya afuskarsa tabbas yayi nadamar abinda yayiwa Naja’atu da yaranta arayuwa, ya tabbatar hak’k’insu ke bibiyar rayuwarsa kuka yakeyi yana cewa”kaicona ni Basheer alal hak’ik’a na aikata babban kuskure arayuwata na walak’anta rayuwar mutane da dama, har iyalina ban rik’esu da amana ba ubangiji Allah ina rok’onka ka fitar dani daga cikin wannan gidan domin in samu damar rok’on Naja’atu gafara kafin mutuwa ta riskeni”.Yana k’arasa maganarsa ya sake fashewa da wani irin rikitaccen kuka mai cikeda k’unci da nadamar rayuwa tsantsar takaici da haushi ne shimfid’e afuskarsa, saboda bai tab’a tsammanin Haseena zata ci amanarsa ba bale harta kawosa gidan matsafa asha jininsa!.
Haseena kuwa harakokin gabanta ta cigaba dayi gudun zargi yasa ta saida sabon gidan da yah Basheer ya gina sannan taba Nasir ajiyar mak’udan kud’in sosai,sannan ta kwashe duka takardun kadarorin daya mallaka ta k’one k’urumumus cikin wuta, gidan da suke ciki tsoho da tsakar dare ta sanya fetur ta fita daga cikin gidan ta turo samari suka sanyawa gidan wuta ya k’one k’urumumus!. Ina lillahi wa inna ilaihirraji’un! Da safe mak’wabta suka wayi gari da fad’ar cewa gidan yah Basheer ya k’one k’urumumus shida iyalinsa gaba d’aya unguwar sun yini cikin bak’in ciki da jimamin mutuwar malam Basheer da matarsa musamman Salisu mijin Saliha abin ya razanasu tareda sanya tsantsar tsoro da tsananin tausayi azuk’atansu”.
Haseena komawa gidan Nasir tayi suka cigaba da zaman tare tareda nunawa junansu tsantsar soyayya da kulawa na musamman, rayuwarsu suke bugawa kamar mata da miji duk abinda suke ra’ayi ko buk’ata shi sukeyi ko’ina zasuje tare kake ganinsu, kallo d’aya zakayi musu ka gane suna tsananin k’aunar juna tareda yarda da zuciya d’aya.
Da tsakar dare misalin k’arfe goma dai-dai agidan matsafa kowane mahaluki dake cikin gidan yayi barci, Basheer zaune yana sallah tareda kai kukansa awurin ubangiji ya kub’utar dashi daga hannun azzalumai, yana shafa addu’a afuskarsa ganin k’afa ta d’auke bakajin kukan koma saina tsuntsaye ya mik’e sadafsadaf sannu ahankali, dayake yana lura da hanyar da suke shiga da fice ya fice daga cikin d’akin da sassarfa jikinsa yana rawar tsoro zuciyarsa tana luguden fargaba, haka dai ya cigaba da ficewa daga cikin k’ofofin gidan masu yawa dak’yar ya samu ya fito daga cikin gidan ya tsinci kansa atsakiyar daji, jin yayi kamar ance masa ka gudu idan ka shek’a karka kuskura ka juyo! Yah Basheer bai tsaya b’ata lokaci ba ya tattare wandonsa ya dinga faffalawa da gudu kamar zai tashi sama, gudu yakeyi harna fitar hankali har ya kawo bakin titi, haki ya tsaya yi akan yadda ya galabaita sosai tsakar titi yahau ko Allah ubangiji zaisa ya samu mota, ya jima tsaye agalabaice saiga fito ta gifto d’aga musu hannu yayi alamar su tsaya dak’yar da sud’in goshi ta ya samu mai motar ya tsaya yace”wa nene kai!? “Basheer yace agajiye “ka taimakeni bawan Allah bazan cutar dakai ba”.
Mai motar yayi shiru yana k’are masa kallo tareda karantar abinda ke cikin k’wayar idonsa dak’yar ya nisa yace”shigo mubar wannan daji domin yanada matuk’ar hatsari! “.Jikin Basheer ya rawa ya shigo cikin motar ya rufe k’ofar nan da nan suka fice daga wurin suka nufi cikin gari.