HAUSA NOVELRASHIN SO Complete Hausa Novel

RASHIN SO Complete Hausa Novel

Agidan mai motar yah Basheer ya kwana sannan da safe ya taimaka masa da kud’in hawa keke napep yahau ya nufi hanyar gidansa, mai keke napep yana ajeshi gefe ya k’ara gaba juyawar da Basheer zaiyi yaga filin gidansa ya zama kango ko’ina ya k’one k’urumumus babu abinda yake iya ganewa,nan da nan idanun Basheer suka cicciko da ruwan hawaye cikin sanyin jiki da rashin kuzari ya nufi k’ofar gidan Salisu yana knocking ba’a jima ba Salisu yazo da kansa ya bud’e k’ofar gidan ganin Basheer ne atsaye yasa yaji tsoro jikinsa yana k’yarrma yace”Basheer dama kana raye baka mutu!? “Hawayen da yake b’oyo suka zubo afuskarsa yace”ban mutu ba Salisu mu shiga ciki in baka labarin irin gwagwarmayar dana sha arayuwata! “.Salisu ya bashi hanya yace “ka daina kuka Basheer shigo ciki ba damuwa “.Salisu yana gaba Basheer yana biye abayansa har suka iso tsakiyar gidan suka iske Saliha zaune tana tsintar k’asa acikin wake, tana ganinsu ta gaishesu tareda mamakin ganin Basheer araye domin su dai duk azatonsu tuntuni ya mutu cikin gobarar data kama gidansa ya k’one k’urumumus.

Saliha ta mik’e tsaye ta d’ebo ruwa masu sanyi cikin jug ta kawo ta dire agabansu sannan ta koma ta zauna alokacin ne Salisu ya dubi Basheer yace “bismillah sha ruwa kaji sanyi azuciyarka domin kaji dad’in bamu labarin irin gwagwarmayar daka sha arayuwa “.Basheer ya d’an kurb’i ruwan yayi ajiyar zuciya yace “ku saurari labarin dazan baku Salisu hak’ik’a hak’k’in Naja’atu da yaranta ne ke bibiyata har yanzu saboda naci amanarta tareda cutar da rayuwarta……. abinda ya faru shine…… “.Duk abinda ya faru ya kwashe ya sanar musu yana kukan nadama da dana sani arayuwa suma su Salisu sai zubar da hawayen tausayin Basheer sukeyi suna jimami acikin zuk’atansu duk dayake sunyi imani da cewa hak’k’in Naja’atu da yaranta ne ke bibiyarsa. Alokacin ne Salisu ya kallesa yace”hakika kaga fitinar rayuwa Basheer amma ya kamata kaje ka nemi gafarar Naja’atu domin hak’k’inta ne ke bibiyarka, sannan ina Haseena ta tafi ne ko ta mutu!? “………..

 

“`Duniya abar tsoro ce mutane muji tsoron Allah komai zamuyi mu dinga sara muna dibin bakin gatari, alal hak’ik’a duk abinda mutum ya shuka saiya girbi abinsa tun anan duniya, magidanta kuji tsoron ubangiji ku daina nuna bambanci atsakanin matanku kada ku nuna fifiko atsakanin yaranku mafi akasarin matsalolin da ake samu yanzu agidaje shine rashin adalci, rashin so, bayyana soyayya afili atsakanin mataye “`
[11/28, 9:09 AM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sis Najer’art*

*THE LAST PAGE.*

*PAGE 40*

Hawaye masu zafi suka wanke fuskar Basheer yace”ko bakace ba ya zamo dole inje in nemi gafararta tun kafin mutuwa ta riskeni, sannan Haseena ta kwashemin duk wasu kadarori nawa ta gudu ko sabon gidana dana gina ta siyar ta gudu da kud’inta,kaga kuwa bansan duniyar da taje ba domin yanzu ni bata gabana tuni na rubuta mata takardar saki naba Ila mai shago ya bata idan wata rana ta gifto wurin shagonsa”.Salisu ya girgiza kansa cikin matuk’ar tausayi yace”hmmm ubangiji ya sawwak’a ya baka ikon neman gafararta”.Amin amin Salisu nizan wuce zuwa wani wuri”.Basheer ya fad’a tareda mik’ewa tsaye alamar zai wuce.
Alokacin ne Saliha ta dubesa cikin tausayawa tace”idan kaje wurin Aminiyata ina gaidata ubangiji ya sassauta maka lamarinka”.”Uhmmm”.Basheer yace.
Basheer ya nufi hanyar fita daga cikin gidan yayinda Salisu ya rakashi har bakin k’ofar gidan, sannan suka tsaya Salisu ya ciro kud’i dubu ishirin daga cikin aljihunsa ya mik’awa Basheer, Basheer ya amsa tareda yi masa godiya sosai sannan sukayi musabaha da juna Salisu ya juya ya koma cikin gidansa yayinda yah Basheer ya nufi hanyar zuwa wani wurin.

Kud’in da Salisu yaba Basheer k’yauta dasu ya cigaba da amfani yana ciyar da kansa, ashagon abokinsa yake barci yana samu yana ciyar da kansa domin makarantar da yake karantassuwa tuni suka sallamesa daga wurin aiki, aranar yah Basheer yayi kuka kamar ransa zai fice daga cikin gangar jikinsa tsantsar bak’in ciki da nadamar rayuwa ne shimfid’e afuskarsa alokacin ya k’ara nadama da sakankancewa da duniya makaranta ce mai d’auke da classes na d’aukar darasi.
Hmmmm duniya juyi juyi ce yau gareka gobe ga d’an uwanka haka rayuwar Basheer ta cigaba da gudana awahalce, cikeda k’ask’anci da rashin gata har ya zamana abinda zaici wuya yakeyi masa sosai,yanayinsa duk ya chanza ya koma wani irin mutum kodayaushe ka gansa shiru shiru yake ganin yana cikin damuwa yasa abokinsa mai shago yakaisa wurin iyayensa suka bashi auren k’anwarsa Zakiyya akayi aurensu nan da nan batare da b’ata lokaci ba, sannan ya samu d’an kwanciyar hankali da natsuwa azuciyarsa domin Zakiyya tana k’ok’ari wurin bashi tsantsar kulawa tareda nuna masa tsananin soyayyar gaskiya.
____________________
Agidan Na’im su Naja’atu na hango cikin kitchen suna aikace-aikace suna fira cikin farin ciki da nishad’i sosai, alokacin ne Raliya ta kalli Naja’atu tace”kinsan wani abu k’anwata?”.Naja’atu ta sakar mata murmushi tareda langwab’e kanta cikin farin ciki tace”sai kin fad’a Auntyna”.
“kinada labarin cewa Haseena ta sacewa tsohon mijinki Basheer duka dukiyarsa ta gudu sannan duk wasu kadarori daya gada awurin mahaifinsa Alhaji Tasi’u yanzu duk babu su”.
“hmmmm abin takaici kenan hak’ik’a Basheer yaga jarabawar rayuwa ubangiji yayi masa sauk’i”.
“amin k’anwata hak’k’inki ne ya fita akansa”.
“shidai ya sani ai dama duniya ta gaji haka idan ka shuka hairan kaga hairan idan ka shuka shairan kaga shairan”.”Hak’k’un maganarki haka take”.Raliya tana rufe bakinta suka cigaba dayin ayyukansu suna wasa da zolayar juna kamar ‘yan uwan juna ba kishiyoyi ba.

*BAYAN SHEKARU HUD’U*
Agidansu baffa Salihi da matarsa Inna Madina tun lokacin da suka sanya aka kashe Hakeem tareda k’one musu gida k’urumumus, suka bud’e sabon shafin rayuwar jin dad’i da nishad’i sosai saboda dukiyarsu Haseena suka cigaba da ci suna bushasha da ita, ya zamana basa cin tuwo sai nama da kayan mak’ulashe suna shagalinsu.
Haka dai suke gudanar da rayuwarsu cikeda rashin tsoron had’uwarsu da ubangiji, wata rana suna zazzaune suna fira cikin farin ciki da nishad’i sai baffa Salihi ya kalli Inna Madina yace”hmm agaskiya wannan duniyar akwaita da dad’i musamman idan ka tanadi masu gidan rana zaka more rayuwarka”.
Inna Madina ta k’yalk’yale da dariya tace”tanada dad’i kam duniya har dai idan mutum bai tauye rayuwarsa ba, kaga tun lokacin da kasa aka kashesu Haseena komai yayi mana daidai babu mu babu fargabar wata rana za’a iya cewa bamu kud’in gadonmu”.
“maganarki gaskiya ce Madina yanzu dai babu wanda muke fargaba araye”.
“haka ne”.
Firarsu sukeyi cikin nishad’i da jin dad’i kallo d’aya zakayi musu ka gane babu abinda yake damunsu, duk dayake har yanzu Inna Madina bata tab’a haihuwa agidan baffa Salihi ba amma wannan bai damesu ba saboda suna cin duniyarsu da tsinke.
Da dare bayan su Inna Madina sun kwanta barci misalin k’arfe goma sha d’aya na dare, kamar daga sama gobara ta tashi cikin gidan kafin sun ankara har wuta ta iso cikin d’akin da suke kwance suna barci! Kamar an tsikari Inna Madina ta mik’e tsaye taga wuta kuwwa ta saki cikin gigicewa tace”wayyon Allah Salihi ga gobara ta iso har cikin dak’inmu ka tashi “.Salihi ya k’ara gyara kwanciyarsa baiji abinda take fad’a ba, ganin haka ne yasa Inna Madina ta bugi cinyarsa ta sake cewa”Salihi ka tashi wuta ta kama cikin gidanmu!”.Taji shiru bai sake ko motsawa ganin wutar tayo kusa gareta yasa Inna Madina ta shek’a da gudu ta fice daga cikin gidan tana kuwwa da kururuwar neman agaji amma dayake dare babu wanda yajita, tana ji tana gani wuta ta k’one gidan mijinta k’urumumus kamar ba’a tab’a yin gini ba, nan da nan Inna Madina ta k’yalk’yale da dariya hhhhhhhh harda fad’uwa k’asa tana birgima tace”Salihi ya mutu Salihi ya mutu! “.Tana rufe bakinta ta fara cire tufafinta tana yassuwa k’asa har ta koma daga ita sai under sicket da shimi, cire d’an kwalinta tayi tayi wurgi dashi k’asa ta yamutsa gashinta yayi buja-buja ta shek’a da gudu tana hauka, tsakiyar daji ta nufa da gudu tana sambatu da ifface ifface na tab’in hankali..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button