HAUSA NOVELRASHIN SO Complete Hausa Novel

RASHIN SO Complete Hausa Novel

Gidan Alhaji Na’im Abdulhakeem yara k’anana ne na gani suna wasanni da guje-gujensu ga kayan wasa nan birjik ako’ina kala kala, Shaheed ne zaune saman kujera yana lura da duk motsinsu Suhail ya dubisu Suhailat yace”dallah ku tashi ku bani wuri kunzo kun hanamin jin dad’i! “.
Suhailat ta kalli Khairat itama Khairat ta kalleta cikin jin haushin maganarsa Suhailat ta zumb’ura baki tace”babu inda zamuje saidai idan ka matsu ka tashi ka bamu wuri”Khairat tace”ai shine idan ka nemi ka takura mana mu had’aka da yah Shaheed”Suhail ya murtuk’e fuskarsa yace”yara idan baku bini sannu ba saina yi muku dukan tsiya”.
Dayake Suhailat akwai baki da tsiwa ta murgud’a masa bakinta tace”idan ka dakemu sai mun had’aka momy”.Khairat taja hannun Suhailat dayake ita akwaita da tsoro tace”muyi wucewarmu cikin gida kinji sisterna muje muyi wasa da Sa’id”.”To Khairat”.Suhailat tana rufe bakinta suka shige cikin gidan.
Ba’a dad’e ba yah Na’im ya kunno hancin motarsa cikin gidan bayan getman ya wangale masa get d’in, parker motarsa yayi aparking lot sannan ya fito daga cikin Suhail yana ganinsa ya shek’o da gudu ya rungume mahaifinsa yayinda Shaheed yazo ya amshi kayayyakin dake hannunsa tareda yi masa sannu da zuwa, yah Na’im ya amsa masa fuska asake sannan ya jaye Suhail ajikinsa yaja hannunsa suka nufi cikin parlourn da sallama abakinsa.
Su Naja’atu suka amsa masa sallamarsa fuskarsu d’auke da annuri da fara’a, zaunawa yayi tsakiyarsu yana jifarsu da kallon k’auna da soyayyar gaskiya numfashi yayi yace”uwayen gida sannunku da aiki”.
Raliya tayi murmushi tace”yauwa maigidanmu”.Naja’atu murmushi kawai takeyi tana shayar da Sa’id daya dameta da kuka tun d’azu yayinda su Suhailat sukayi mata tsaye saita basu Sa’id suyi wasa, Fa’iza da Fa’iz sai harara suke aikowa su Khairat dayake takaici suke basu saboda rashin jinsu, fira ta b’arke atsakaninsu tareda yaransu kowa sai fad’in albarkacin bakinsa yakeyi.

Suna firarsu saiga sallamar maigadi yah Na’im ya mik’e tsaye ya nufi bakin k’ofar parlour yace”lafiya dai?”.”Lafiya k’alau dama bak’o kayi yakeson ganinka”.”OK kace ya shigo cikin parlourn ba matsala”.”To Alhaji”.Yana rufe bakinsa yaja k’afafunsa ya nufi bakin get, bada jimawa ba saiga yah Basheer ya shigo tsakiyar parlourn Na’im ya isa wurinsa sukayi musabaha da juna duk dayake baisan Basheer amma shi Basheer ya tab’a ganinsa aphoto, ganin Basheer yasa Naja’atu tayi kici kici da rai tareda b’ata fuska domin ganinsa ayau ya tuna mata da irin azaba da sanyata cikin k’angin rayuwa da yayi agidansa, babu wanda ya lura da sauyin fuskarta sai yah Basheer iznin zama saman kujera yah Na’im ya bashi sannan yasa Raliya ta kawo masa drinks masu sanyi, babu abinda yasha saboda kunya kallon fuskar Na’im yayi yace”Alhaji Na’im sunana Basheer Tasi’u nine tsohon mijin matarka Naja’atu mahaifi ga Rufaida da marigayi Suhail”.”Allah sarki kace kaiba bak’o bane ashe nayi matuk’ar farin ciki da ganinka”.Inji yah Na’im murmushi k’unshe afuskarsa.
Basheer yayi gyaran murya cikin sanyin jiki yace”nima ina farin ciki da had’uwa dakai dalilin dayasa nazo gidanka saboda inason ka tayani rok’on gafarar matarka Naja’atu akan irin cutarwa da musgunawar da nayiwa rayuwarta, alal hak’ik’a nayi matuk’ar nadamar abinda na aikata a rayuwata kuma naga sakayyar zalunci da cin amana domin duk abinda na mallaka ya halake matar da nakeso ta cuceni ta gudu ta barni cikin k’unci da uk’ubar rayuwa”.Yana k’arshen maganarsa ya rushe da rikitaccen kuka mai cikeda k’unci da tarin damuwa, yayinda hawayen bak’in ciki keta sintiri akan afuskarsa, yah Na’im ya dafa kafad’arsa cikin jimami da tausayawa yace”ka daina kuka Basheer komai ya riga ya wuce har abada, nasan my Najerty mace ce mai halin dattako da mutunci zata yafe maka saboda haka ka kwantar da hankalinka”.
Na’im ya juya ya kalli Naja’atu yace”Najerty kiyafe masa kuskuren dayayi abaya duk d’an Adam ajizine”.Hawayen takaici ne suka zubo afuskar Naja’atu domin abinda ya faru ya dawo mata sabo fil cikin zuciyarta shiru tayi bata ce uffan ba, ganin tana kuka yasa yah Basheer ya gurfana ak’asa saman gwaiyoyinsa yace mata”ki taimaka ki yafemin duk zaluncin da nayi miki arayuwata tabbas nasan na cutar dake da yaranmu, amma ki sani ubangiji yayi miki sakayya tun anan duniya domin banida komai ayanzu duk abinda nake tink’aho dashi ya lalace abanza, alal hak’ik’a *NAYI NADAMAR* zaluntarki da nayi har azuciyata”.
“dakata Basheer sai yanzu zakayi nadamar cutar da rayuwata da kayi bayan ka auro macen data zamo ajalin d’ana SUHAIL! Saboda haka ka b’acemin da gani banason idanuna su k’ara yin tozali da maciyi amana irinka! “.Na’im ya girgiza kansa cikin tsananin tausayi yace”kiyafe masa ko ubangiji Allah muka yiwa laifi sannan muka rok’esa gafara yakan yafe mana bale mu ‘yan Adam “.Alokacin ne Raliya tace cikin tausayi”ki yafe masa k’anwata ubangiji yanason bayinsa masu hak’uri da saurin yafiya”.Naja’atu tayi murmushin dake k’unshe da d’acin rai hawaye suna kwaranya afuskarta tace”na yafe maka Basheer ubangiji ya yafe mana zunubanmu baki d’ayanmu “.”Amin “.Sukafad’a atare ,yah Basheer ya tashi agurfane yace”nagode sosai da kika yafemin duk zaluncin da nayi miki arayuwata tabbas ke d’in kinada hak’uri da zuciyar alkhairi, ni zan tafi ubangiji ya sada fuskokinmu da alkhairi “.Yana kai k’arshen kalamansa yaja k’afafunsa ya fice daga cikin gidan da saurinsa yayinda yabar yah Na’im da Raliya suna mayarda zancen cikin tausayawa da tsantsar jimami.

Naja’atu itace ta haifi Suhail, Suhailat da Sa’id bayan d’iyarta Rufaida yayinda Raliya itace ta haifi Shaheed, Fa’iza, Fa’iz, da Khairat auta.

Bayan yah Basheer ya gudu agidan matsafa basu gano ba sai daga baya, gani ganin ya gudu yasa shugaban matsafa ya takurawa su Haseena itada Nasir su nemoshi duk inda ya shiga a fad’in duniya, saida ya basu sati biyu rak suka kasa kamosa ganin haka ne yasa shugaban matsafa da wad’anda suke ak’ark’ashinsa sukayi amfani da k’arfin sihiri da gunguma akan tsafi suka shanyewa su Haseena jini naman sassan jikinsu suka mik’awa macizai suka lak’umesu zama guda…

*ALHAMDULILLAHI*.

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button