HAUSA NOVELRASHIN SO Complete Hausa Novel

RASHIN SO Complete Hausa Novel

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sis Najer’art*

_Free page._

*PAGE 5*

 

Naja’atu ta raka Saliha har bakin k’ofar gidansu anan taja ta tsaya Saliha ta k’ara jaddada mata akan tayi k’ok’ari wurin fara sana’a domin gujewa afkawa cikin tarkon wahala, Naja’atu ta nuna mata zata fara sana’ar da yardar Allah saida ta k’ara yi mata nasiha akan hak’uri da rungumar k’addararta hannu bibbiyu sannan tayi masa sallama ta wuce zuwa gidanta dake kusa danasu Naja’atu.
Saida taga ta wuce zuwa gidanta sannan Naja’atu ta juyo ta dawo cikin tsakiyar gidan, koda ta iso wurin Haseena ta iske harta kammala dahuwar abincin ta dib’awa mijinta cikin kula sauran kuwa ta zauna tana ci tana hango Naja’atu tafe ta gefenta, sai naga ta d’ebo miyar tumatur ta sanya cikin wani k’aramin kwano Naja’atu tana isowa wurinta Haseena ta mik’e tsaye ta watsa mata miyar ajikinta, jin abu ya zuba ajikinta saida Naja’atu ta zabura da k’arfi domin ta firgita sosai tace”Haseena miye kika zubamin ajiki bak’ya gani ne?”.
Haseena tayi mata kallon banza tace”kin makauce ne da baki dibin abinda yake gabanki? Nifa banga giftowarki ba shiyasa nayi nufin zubar da miyar sai aka samu akasi ta sauka ajikinki”.
Imani da mamaki ne suka sa Naja’atu ta kasa d’aga k’afafunta daga inda take tsaye, tsurawa fuskar Haseena tayi da kallo saboda walak’ancin da tayi mata yayi matuk’ar k’ona ranta da sanya d’aci da rad’ad’i azuciyarta,kallonta takeyi cikin k’unar zuciya da tsanar walak’anci tace”bakiga giftowata ba kikace?”.
Haseena ta musk’uta tareda yi mata kallon sama da k’asa tace”keee!Ki wuce ki bani wuri kin cikamin kunne da surutun banza an watsa miki miya ajiki da sanina na watsa miki miyar mi zakiyi!?”.
Naja’atu ta kalli jikinta daya b’ace da miya rayuwarta ta k’ara b’aci sosai zuciyarta sai k’una takeyi mata,b’acin rai ne kwance afuskarta numfashi ta sauke tace”kin k’yauta Haseena duk abinda kikayi ba laifinki bane laifin wanda ya ajiyeki ne wanda bai mayardani abakin komai ba bayan banza jaka, amma inason ki sani duk abinda ya sameni kema wata rana zai iya samunki na barki lafiya”.
Tana kai k’arshen maganarta tayi ficewarta ta shige cikin d’akinta tabar Haseena tsaye tana hararar bayan Naja’atu kamar idanunta zasu fad’o ak’asa, tsaki taja mtssss sannan tace”babu abinda zai sameni sai alkhairin Allah mugun bakinki ya sari d’anyen kashi mai bak’ar aniya!”.
Rufe bakinta keda wuya saiga sallamar yah Basheer ya shigo hannunsa rik’e da manyan ledodi guda biyu, tana ganinsa ta fad’ad’a murmushi afuskarta tace”darling sannu ya d’alibbai?”.
Murmushi yah Basheer ya sakar mata yace”Alhamdulillah”.
Haseena ta amshi ledodin dake hannunsa ta mak’ala hannunta d’aya akafad’arsa tace”mu shiga ciki ko akwai wanda zaka ba matarka?”.
Basheer ya kalleta yace”a’a babu rabonta aciki”.
Haseena tayi murmushin dake bayyanar da hak’ora jansa tayi sai cikin d’akinta tana dariyar farin ciki, suna shiga ta cire masa tufafinsa ya fad’a cikin bathroom yayi wanka bayan ya fito ta shafe masa jiki da mai shi kuma sai lumshe idanu yakeyi yana k’ara narke mata ajiki, tana gama shafa masa mai ta d’auko masa jalabiya bak’a ya sanya jansa tayi sukayi masauki saman gado rungume da juna, shafar fuskarta yakeyi cikin so yace”Hasee baby wannan kwalliyar taki tayi k’yau matuk’a”.
Haseena tayi shame shame ajikinsa tana shagwab’a tace cikin sanyin murya”kaima darling kanada k’yau sosai”.
“harna kaiki k’yau ne?”.
“kama fini nesa ba kusa ba”.
“da gaske?”.
“Allah kuwa”.Ta fad’a tana zumb’ura baki cikin sagarta.
Kissing yayiwa bakinta yasa hannu ya dinga yawo dashi asassan jikinta ita kuma sai wani narkewa takeyi tana lumshe idanunta alamar abin yana yi mata dad’i sosai, cigaba da shafarta yayi hankalinsa yana tashi babu abinda yafi d’aukar hankalinsa irin boobs d’inta da suke tantsa-tantsa kamar zasu faso daga cikin rigarta kallon k’urilla yakeyiwa k’irjinta yasa hannunsa ya shafa yace”ina mugun so wad’annan abubuwan akwaisu da d’aukar hankali baby”.
Kallon k’auna Haseena ta jefeshi tace”darling ai naka ne kai kakeda ikon kayi abinda kaga dama dasu babu mai hanaka saboda halalinka ne”.
Basheer yace”naji dad’ina kenan tunda nikeda ikonsu kinsan wani abu babyna”.
“sai ka fad’a”.
“aduniya ban tab’a fad’awa cikin tarkon k’aunar wata mace fiye dake ba, saboda soyayyar da nake miki baki bazai iya k’irga adadinta ba banda *ABAR SO* da k’auna fiye dake Haseena, ina mutuwar sonki arayuwata banda nufin cutar dake ko inci amanarki soyayyar gaskiya nake miki”.
Kalamansa sunyi matuk’ar yi mata dad’i sosai saboda tana hango abinda yake fad’a acikin idanunsa gaskiya ne, wani irin sanyi ya tsirga mata cikin jiki da jininta sai shawagi yakeyi murmushi mai tsada tayi tace”naji dad’in kalamanka matuk’a agareni mijina saidai kuma har Naja’atu kafi sona akanta koba auren soyayya kukayi ba?”.

Basheer ya k’ara rungumeta ajikinsa yace”aurena da Naja’atu *AUREN HAD’I NE* babana da Baffanta suka had’a aurenmu alokacin ba wani soyayya mukayi ba har akayi aurenmu”.
Haseena taji dad’in wannan maganar tasa har azuciyarta b’oye farin cikinta tayi tace” *AUREN HAD’I* fa kace! Kenan babu soyayya mai k’arfi atsakaninku lokacin da akayi muku auren?”.
“tabbas haka ne kina zaton zanyi miki k’arya ne?”.
Girgiza kanta tayi alamar a’a.
“to ki daina kwankwanton maganata baby kinsan ni mutum ne mai tsattsauran ra’ayi akan abinda banaso shiyasa kikaga bana kulawa da ita da d’iyanta saboda banason mahaifiyarsu”.
Haseena tace”ka dinga kula da yaranka da matarka kada azageni ace nice ke zugaka kana walak’anta rayuwar iyalinka”.
“ki daina damuwa da maganar mutane saboda su mutane babu mai iyawa dasu sai Allah, duk yadda kake kaffa-kaffa da tsare mutuncinka wata rana dole sai sun zageka domin d’an Adam da kike ganinsa *BUTULU* ne!”.

“haka ne gaskiya yah Basheer”.
Firarsu sukeyi cikin nishad’i da soyayyar juna bayan sun gama fira ya d’auko leda d’aya daga cikin wad’anda ya shigo dasu, suka bud’e suka fara cin ayaba da abarba ci sukeyi suna fira cikin kwanciyar hankali, yayinda suka bar Naja’atu baiwar Allah itada d’iyanta acan d’akinta kosu tsakuro kad’an sukai mata amma babu wanda ya tuna da ita acikinsu.

**********************
*BAYAN SATI D’AYA*

Alokacin har Naja’atu ta fara sana’ar saida kayan miya iri iri daban daban da kad’an kad’an ta dinga tara ribar kud’in Saliha, tana tarawa har kud’in suka kai dubun hamsin da kanta taje gidan Saliha ta bata kud’inta tareda yi mata godiya sosai, Saliha ta nuna mata babu komai ai yiwa kaine Naja’atu ta dawo gida ta cigaba da gudanar da sana’arta cikin natsuwa yah Basheer bai fahimci ta fara sana’a ba sai daga baya, koshi ranar daya fahimci tana saida kayan miya shine wata rana ya dawo daga school agajiye ya taradda tana dahuwar macaroni taji kifi acikinta k’amshin girkinta ne ya bugi hancinsa lumshe idanu yayi tareda had’iye miyan kwad’ayi mak’wat amak’oshinsa,kallon abincin yayi zuciyarsa ta biya k’arasowa wurinta yayi yace”Naja’atu girki kikeyi waye ya baki kayan cefane?”.

Kallonsa tayi fuskarta babu annuri tace”Allah ne ya bani”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button