HAUSA NOVELRASHIN SO Complete Hausa Novel

RASHIN SO Complete Hausa Novel

Matsowa yayi kusa gareta yace”ban gane Allah ne ya baki ba a ina kika samu kud’in yin girki ko kin fara karuwanci ne ban sani ba!?”.
Kalmar karuwa daya jefeta dashi ya soki k’ahon zuciyarta b’acin rai da tsantsar damuwa ne ya shimfid’u afuskarta idanunta sukayi jajir akan bak’in ciki, juyar da kanta tayi tace”agaskiya na gaji da irin abubuwan da kakeyimin acikin gidanka! Ni kenan kullum saika jefeni da mummunan kalma sannan hankalinka yake kwanci irin wannan d’abi’ar da kakeyi bayada k’yau ko kad’an”.
“idan kin gaji da halina mana ki tattara kayanki ki barmin gidana! Ai nasha gaya miki ba k’aunarki nakeyi ba to uban wa yace ki zauna dole cikin gidan nan?”.
“haka ka fad’a?”.
“na fad’a tunda na aureki ban ganewa komai ba sai hasara da bak’in ciki, kuma kada in sake ganin kin girka abinci cikin gidana tunda ba gidan karuwai bane taya bansan inda kika samu kud’i ba zakizo kinamin girkin abincin haramu cikin gida”.
Hawaye masu zafi suka wanke mata fuska saboda taji zafin k’azafin da yah Basheer yayi mata har cikin zuciya, kallon tsana tayi masa tace”Allah ubangiji yayimin tsari daga kaidinka ya kareni daga fad’awa cikin tarkon mugun bakinka! Tabbas ka nunamin baka k’aunata aduniya ba komai rayuwa ce da sannu komai zai zama tarihi”.
Yah Basheer ya hasala ya kalli tukunyar da take dahuwar macaroni duk’awa har k’asa yayi ya ciko hannunsa da k’asa ya zuba acikin tukunyar abincin yace”na zuba k’asa cikin tukunyar je kici abincin keda shaggun yaranki! “.
Alokacin Naja’atu ji tayi kamar ta kashe kanta akan bak’in ciki da k’uncin rayuwa kukan da takeyi ne ya fito fili ta rufe bakinta da tafin hannunta, kasa ce masa komai tayi akan d’aci da k’ololon bak’in cikin abinda yayi mata direct d’akinta ta shige tana rusa uban kuka mai ban tausayi da tsuma zuciyar mai sauraro, tana shiga ta fad’a asaman cushion sai risgar kuka takeyi Rufaida dake zaune tana wasa da Suhail ta nufi wurin mahaifiyarta ta rungumeta itama ta fashe da kuka tace “Ummi miya sameki ko Abbanmu ne ya sanyaki kuka dan Allah kiyi hak’uri ki daina kuka?”.
Naja’atu ta k’ara k’ank’ame Rufaida ajikinta tana kuka tace”bashi bane ya sakani kuka Rufaida banajin dad’in jikina ne”.

Rufaida ta dubeta cikin tausayawa tace”ayyah Allah ya baki lafiya Ummi bari in d’ebo miki magani kisha ai kin kusa kammala abincin ko?”.

Naja’atu tace mata”rago ya kifar da tukunyar abincin bari dai in jik’a mana gari da sugar musha”.
“to Ummi”.Inji Rufaida.
Naja’atu ta tashi tsaye da kumburarrin idanunta ta nufi wurin ledar gari kofi biyu ta d’auko ta jik’a garin tareda saka sugar aciki, Rufaida ta tashi ta nufi drower da suke ajiyar magani ta b’allowa mahaifiyarta sannan ta koma ta zauna saman cushion Naja’atu ta d’auko kofin biyu ta mik’awa Rufaida d’aya suka fara sha, tana gama shan nata Rufaida ta sanya mata maganin cikin bakinta cikin tsananin k’aunar mahaifiyarta dak’yar Naja’atu ta had’iye maganin tana yamutsa fuska kamar zatayi kuka, suna kammala shan gari suka k’unshe cikin room d’in zuciyar Naja’atu cunkushe take da b’acin rai da bak’in ciki mara misali, tunanin rayuwarta na baya ta dinga yi abubuwa da dama suka dawo mata sabbi fil cikin k’wak’walwarta………..
[11/18, 6:11 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sis Najer’art*

_Free page._

*PAGE 6*

 

Haka Naja’atu ta kwana cikin bak’in ciki zuciyarta cunkushe da b’acin rai adaren ranar kasa runtsawa tayi akan tsantsar damuwa, juye juye kawai takeyi saman gado cikeda matuk’ar zullumi da rad’ad’in zafin abinda yah Basheer yayi mata ganin ta kasa barci yasa dole ta mik’e tsaye, shiga cikin bathroom tayi ta d’auro alwala shimfid’a sallaya tayi ta dinga jera nafiloli tana kuka tareda kai kukanta awurin Allah, ta jima sosai tana yin addu’a sannan daga k’arshe b’arawon barci yayi awon gaba da ita batare data ankara ba.

Ab’angaren yah Basheer shida matarsa Haseena farin ciki sosai suka kwana dashi saboda ba k’aramar soyayya sukeyiwa juna ba, sun faranta ran juna awannan dare tareda fallasa sirrin dake zuciyarsu gameda tsantsar kulawa da soyayyar da suke yiwa junanku, har azuciya Haseena tanason Basheer sosai amma tasan son da yakeyi mata bai ko kama k’afar wanda takeyi masa ba, ta haka ne takeyi masa abinda taga dama tareda juyashi son ranta kamar waina, saboda ta hak’ik’ance bazai iya rayuwa saida ita ba.

********************
Washe tunda safe misalin k’arfe bakwai Naja’atu ta share d’akinta da parlour sannan ta aza ruwan zafi tayiwa ‘ya’yanta wanka, tana kammala yi musu wanka ta shiryasu cikin sutura masu dama, direct abinci tayi musu sukaci suka k’oshi sannan itama ta fad’a cikin toilet ta fara wanka ta jima tana wanka sannan ta fito doguwar riga ta saka ta fito daga cikin d’akinta, wurin katangar gidan Saliha taje ta kira sunanta da k’arfi tace”Aminiya!Aminiya!!”.
Har sau biyu Saliha ta amsa da na’am tace”gani Aminiyata lafiya dai?”.
“dama so nake in saka Rufaida makarantarsu Rayyanu boko da islamiya kada yarinyar ta taso babu ilmi, domin kinga mahaifinsu ba wani damuwa yayi dasu ba shine nace bari in sanardake idan zai tafi gobe ki gayawa Babansa yakai Rufaida dan Allah”.
Murmushi Saliha tayi tace”wannan shawarar da kika kawo gaskiya tayi saboda haka karki damu Naja’atu zan gayawa Baban Rayyanu, duk abinda ake ciki zamuyi magana kinji”.
Naja’atu tace”ba damuwa Saliha ki shafamin kan ‘yata Shamsiya”.
Saliha tayi dariya tace”zataji gaisuwa daga wurin Mamanta ya sana’ar ina fatar kina samun d’an abinda kike iya d’aukar nauyin iyalinki”.
“Alhmdulillah gaskiya ana samu saidai godiya ga Allah”.
“Allah ubangiji ya k’ara bud’i na Alkhairi”.
“Amin ya rabbi”.Cewar Naja’atu cikin sanyin hali.
Sun jima suna firarsu cikin shak’uwa da yarda da juna sannan daga k’arshe Naja’atu ta sauko saman turmi ta shige cikin d’akinta, itama Saliha sauka tayi ta zauna saman kujera.
Tana zama mijinta Salis ya shigo cikin gidan hannunsa d’auke iccen girki yana shigowa dasu yana ajiyewa,saida ya kammala jide iccen sannan ya iso wurin Saliha murmushi Saliha ta sakar masa tareda yi masa sannu da zuwa, kujerar da take zaune ta bashi tareda mik’ewa tsaye ta shige cikin d’akinta abincinsa da ruwa ta kawo masa agabansa ta ajiye.
Wanke hannunsa yayi ya fara cin abincin cikin natsuwa ci yakeyi hankali kwance har ya kammala, yana gama cin abincin ya wanke hannunsa tareda ajiyar zuciya yace”Allah ubangiji yayi miki albarka Saliha yadda kike farantamin Allah ubangiji ya faranta miki agidan aljanna”.
Taji dad’in addu’arsa har cikin zuciyarta sannan ta d’ago idanunta ta kallesa cikin k’auna tace”Amin Baban Shamsiya”.
Salisu yace”mata yau ana zafi agarin nan sosai gaskiya”.
“ana zafi musamman ku masu fita akowane lokaci, yauwa d’azu Naja’atu ta gayamin gobe zata turo ‘yarta Rufaida kayi mata ja gaba wurin sakata school”.
Salisu ta jijjiga kansa yace”makaranta takeson saka Rufaida kenan kina ganin babu wata matsalar da zata kunno kinsan fa mijinta Basheer bayada mutunci ko kad’an, ko waye kai yana iya yaga maka rigar mutunci agaban mutane”.
“babu abinda zai biyo baya sai alkhairi ka daina tuna Basheer acikin rayuwarka, saboda Naja’atu da yaranta suna buk’atar taimako idan bamu taimaka mata ba waye zaiji tausayinta har ya taimaketa? Rayuwa da kake ganinta abar tsoro ce yau gareka gobe ga d’an uwanka idan kaga gemun d’an uwanka ya kama da wuta yayyafawa naka ruwa”.
“wannan maganartaki haka ne gaskiya to babu damuwa da yardar Allah gobe idan tazo zanje da kaina inyiwa headmaster magana tunda shi Basheer yayi nisa bayajin kira!”.
Saliha ta bintsire bakinta tace”ai lamarin Basheer babu tsoron Allah da gaskiya acikinsa ace mutum ya karkace wurin mace d’aya ita yake bayawa kulawa, Naja’atu ko itada yaranta ko ohoo saidai yunwa ta zamo ajalinsu babu ruwansa aganinsa bayada hasara!”.
“hmm koshi yakeda babbar hasara matuk’ar wani mugun abu ya samesu saboda bazai tab’a haihuwar kamarsu ba aduniya saidai ya haifi k’annensu”.
“kai kakeda wannan tunani shi baya hangen abinda yake nesa saidai kusa”.
“to Allah ubangiji ya shiryeshi idan mai shiryuwa ne yasa ya dawo kan turbar gaskiya”.
“Amin amin”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button