HAUSA NOVELRASHIN SO Complete Hausa Novel

RASHIN SO Complete Hausa Novel

Suna gama fira Saliha ta had’awa mijinta ruwan zafi ya shiga cikin toilet yayi wanka,kayan shan iska ta ciro masa ya sanya sannan suka tattaro suka dawo cikin parlourn da zama suna fira cikin kwanciyar hankali da farin cikin aure.
*********************
Da safe Naja’atu tayiwa Rufaida wanka ta had’a mata karin kumallo taci jan hannunta tayi ta kaita wurin Salis mijin Saliha, kud’in makaranta ta ciro zata bashi ya nuna mata ta barsu godiya tayi masa ta dawo cikin gida direct ta fad’a cikin d’akinta, gyara room d’inta tayi ta shimfid’a zanen gado sabo fil aleda turaren hayak’i ta kunna ya gauraye ciki da wajen d’akin gaba d’aya, Suhail ta d’auko taci abinci tana sanya masa abaki har ya k’oshi itama taji abincin ya isheta d’aukarsa tayi ta shiga cikin toilet dashi tayi masa wanka itama tayi, fitowa tayi ta sanya lace d’inkin zane mai pieces riga da wando ta sakawa Suhail.
Fitowa daga cikin room d’in tayi ta zauna cikin parlourn tana sauraren wa’azin da akeyi cikin TV, mayarda hankalinta tayi kacokam wurin kallo da sauraren wa’azin dake fitowa daga cikin bakin sheik Giro Argungu, wa’azin da yakeyi wa’azi ne dayake ratsa jiki da jijiyoyin d’an Adam.
____________________
Naja’atu tana zaune rungume da Suhail ajikinta tana cin danbun naman da Saliha ta aiko mata yanzu, saiga sallamar Rufaida ta dawo daga school agajiye amsa mata sallama Naja’atu tayi tace”maraba da zuwa Rufaida”.
Isowa tayi wurin mahaifiyarta tayi ta zauna tace”washhh na gaji sosai Ummi”.
Naja’atu tayi murmushi tace”ina ruwan sabuwar shiga makaranta an fara karatu ne?”.
Rufaida ta jingina jikinta akan Naja’atu tace”eh sun fara karatu tuntuni”.
Naja’atu tace”Allah ubangiji ya taimaka ya bada sa’a”.
“Amin ya rabbi Ummi”.
Naja’atu tace”tashi ki shiga cikin d’aki ki cire tufafinki kiyi wanka sannan kizo kici abinci”.
“bari in d’an huta”.
“tashi kije kiyi wanka wani aiki kikayi ne da zakice sai kin huta ragguwa kawai”.
Tashi tsaye Rufaida tayi tana zumb’ura baki tareda buga k’afafuwa akan sagarci, ficewa tayi daga cikin parlourn kamar zatayi kuka ta shige cikin room d’in Naja’atu.
Kallon bayanta Naja’atu tayi harta fice daga cikin parlourn, mik’ewa tsaye tayi ta aje Suhail saman kujera ta isa wurin TV ta kunna tana kallon hausa fim, ta fara kallo kenan saiga Rufaida ta fito sanye da doguwar riga tana isowa tsakiyar parlourn ta zauna tace”Ummi gani na fito ina abincina?”.
“shiga kitchen ki d’ebo abinci”.
“to Ummi”.Inji Rufaida.

Rufaida ta shiga cikin kitchen ta d’ebo shinkafa da yaji da mai aplate, tana d’ebowa ta fito daga kitchen d’in ta dawo cikin tsakiyar parlourn ta zauna k’asan cushion tana kallon fim d’in da Naja’atu ta kunna.

Kallonta takeyi tana cin abincinta cikin natsuwa Suhail yana zaune saman cushion ya sauko ya nufi wurin Rufaida, zaunawa yayi ya lank’washe k’afafunsa ya sanya hannunsa yana cin abincin Rufaida murmushi ta sakar masa tace”Suhail wa yace kazo ka saka hannunka cikin abincina?”.
Suhail ya dariya yace cikin hausarsa da bata gama fitowa”yinya naceji(yunwa nakeji)”.
“shine zakazo kayimini sukwati”.Cewar Rufaida.
Suhail baice komai ba ya cigaba da cin abincinsa yayi shiru, daga baya Rufaida ta tsame hannunta daga cikin abincin tabar masa sauran shi kad’ai ya cinye, tana gamawa ta d’auki plate d’in direct kitchen ta nufa dashi ta wanke plates d’in data isko cikin kitchen tass sannan ta sanya plates cikin kwando, d’oraye hannunta tayi ta fito daga cikin kitchen d’in ta isa wurin k’anenta tana wasa dashi yana b’angalar dariya sosai, Naja’atu sai kallonsu takeyi cikin so da k’aunar ‘ya’yanta farin ciki da murna ne shimfid’e afuskarta.

Haseena ce ke wanke wanke abakin famfo tana wak’e wak’enta cikin jin dad’i, Rufaida ce ta fito d’auke da Suhail ahannunta hannu d’aya rik’e take da buta tana k’arasowa wurin famfo inda Haseena take wanke wanke, aje Suhail tayi atsaye ta isa kusaga famfon zata sanya buta ta d’ibi ruwa kenan Haseena tana hankalce da ita ta kawo buta zata tara kenan Haseena ta amshe butar tayi jifa da ita, tareda sanya k’afarta tayi shuri da Rufaida saida ta wuntsila k’asa ta fad’o kanta ya bugi k’asa gwafff! Asanadiyar haka ta saki gigitacciyar k’ara da kuwwa alokaci guda yayinda wani irin rad’ad’in ciwo ya ziyarci sassan jikinta da k’wak’walwarta,ganin abinda ya samu yayarsa yasa Suhail ya fashe da kuka tareda shek’owa da gudu ya iso wurin Rufaida dake kwance k’asa kanta ya fashe jini yana zuba! Haseena ta iso wurinsa tasa hannu ta d’ungujeshi k’asa ya fad’i k’asa d’immmmm bakinsa ya gwalje jini ya tsattsafo awurin daya gwalje.
Rikitaccen kuka Suhail ya cigaba dayi wanda adalilin haka Naja’atu ta tashi daga nauyin barcin daya d’auketa, fitowa tayi da sauri daga cikin d’akinta ko d’an kwali babu saman kanta tana isowa tsakiyar gidan ta hango ‘ya’yanta duka biyu kwance a k’asa jini sai zuba yakeyi daga kan Rufaida, gabanta ya fad’i rasssss zuciyarta ta girgiza hankalinta yayi k’ololuwar tashi sosai wani irin masifaffen fargaba da zullumi ya ziyarci sassan jikinta da jininta, tana isa wurin Rufaida dake kwance cikin mayuwacin hali harta suma akan azaba da rad’ad’in ciwon da takeji Naja’atu ta aza hannu saman kai hawaye masu zafi sai kwaranya sukeyi daga cikin idanunta hannun Suhail ta jawo ta rungumeshi ajikinta shima sai shasshekar kukansa kakeji yana tashi, sanya hannu tayi ta share masa bakinsa inda yaji ciwo tsantsar bak’in ciki da k’uncin rayuwa ne suka shimfid’u asaman fuskarta tace “na shiga uku! Haseena waye yayiwa Rufaida wannan ta’addanci?”……….
[11/20, 5:47 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sis Najer’art*

_Free page._

*PAGE 7*

 

Kallon banza Haseena ta watsa mata tsananin tsanar kishiya ne kwance cikin k’wayar idonta cikeda matuk’ar son fitina da neman fad’a tace”nice nan na tureta itada wawan k’anenta!Taya za’ayi ina wanke-wanke wurin famfo k’azamar yarinyar nan taxo zata b’atamin kwanoni wannan ai walak’anci ne da rashin tarbiyar da bakiyiwa yaranki ba!”.Kwanonin data wanke ta saka cikin kwandon roba tana jerasu cikin tsabta.
Maganganunta sun matuk’ar k’ona zuciyar Naja’atu tsananin b’acin rai da tsantsar bak’in ciki ne ya bayyana afuskarta, kallon bakida hankali tayiwa Haseena tace”yanzu saboda Allah Haseena akan kina wurin famfo yarinya tazo zata d’ibi ruwa abuta shine zaki tureta ta fad’i har kanta ya fashe da jini!Wannan ai rashin imani ne da rashin tausayi”.Zanen dake jikinta ta yaga ta d’aurewa Rufaida kanta kwantar da ita k’asa tayi butar da Haseena ta k’wace ta yar ahannun Rufaida, ita Naja’atu ta d’auka ta isa wurin famfo ta cikata da ruwa dawowa wurin d’iyarta tayi ta yayyafa mata ruwan ajiki numfashi Rufaida ta saki da k’arfi tana cewa cikin kuka”dan Allah Amarya kiyi hak’uri kada ki kasheni wallahi bazan k’ara zuwa wurin famfo ba idan kina nan!”.
Hawaye masu rad’ad’i suka cigaba gangarowa afuskar Naja’atu cikin tsananin tausayin ‘yarta ta shafa fuskarta tace”Rufaida ki daina kuka kinji gani kusa gareki”.
Rufaida ta lahe ajikin mahaifiyarta tana ajiyar zuciya guda guda cikin shakku tace”Ummi kece kusa dani?”.
Naja’atu ta rik’e hannayenta tace”nice Rufaida”.
Rufaida batace komai ba taja gwauron numfashi ta lumshe idanunta, alokacin ne ta k’ara k’ank’ame Suhail ajikinta ta kalli Haseena da idanunta jajir dasu tace”kin k’yauta Haseena kodayake bakida laifi ko kad’an acikin wannan lamari, amma inason in k’ara tunatar miki domin kamar kin manta ne ko waye ya kashe wani hukuncinsa kisa ne!”.
Haseena ta mik’e tsaye tana karkad’a bayanta cikin nuna isa da gadarar ita miji yakeso tace”keeee Naja’atu!Maganganun da kike gayamini na banza sun fara isata naji banida imani sai mi to? K’azaman ‘ya’yanki kada su kuskura su k’ara isowa a inda nake idan kuma suka k’ara sai nayi musu mummunan hukuncin da yafi wannan, banza kawai mai banzar rayuwa!”.
Kwalla tana zuba afuskar Naja’atu tana sharewa cikeda bak’in ciki tace”bazaki daina ba kenan naji ni banza ce Haseena, duk abinda kikeyi ki cigaba duniya ce wanda baizo bama jiransa takeyi shima wanda ya d’aure miki gindi kina aikata abinda kika gadama tabbas wata rana zakuyi *NADAMA*!”.
“kece kike cikin k’unci da nadamar rayuwa bani ba saboda haka can ta matse miki babu abinda ya shafeni!”.
Murmushi Naja’atu tayi mai k’unshe da bak’in ciki da takaicin rayuwa girgiza kanta tayi tace”babu komai wannan *K’ADDARA CE* duk halin dana tsinci kaina acikinsa tabbas komai zai wuce”.
Tana kai k’arshen maganarta ta goyi Rufaida abayanta yayinda ta rik’i hannun Suhail sukayi cikin d’aki, da harara Haseena ta rakasu kamar idanunta zasu fad’o ak’asa taja tsaki tace”wawuya kawai haka zaki dawwama cikin bak’in ciki da k’angin rayuwa”.D’aukar kwandon kwanoninta tayi ta nufi cikin d’akinta dasu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button