RASHIN SO Complete Hausa Novel
Naja’atu tana shiga cikin d’akin ta shimfid’e Rufaida saman gado shi kuma Suhail ya zauna saman cushion hawaye yab’e yab’e afuskarsa, share masa hawayensa tayi wurin tufafinta ta nufa ta ciro hijabinta ta sanya tana sanyawa ta fito daga cikin d’akinta tareda nufar gidan Saliha.
Da sallama ta shiga cikin gidan isko Saliha da mijinta tayi zaune suna fira, Naja’atu ta gaidasu cikin kunya ta samu kujera ta zauna tace”Baban Rayyanu wurinka nazo”.
Salisu ya gyara zamansa yace”ina jinki”.
“Rufaida ce kanta ya fashe da jini yana zuba shine nace bari inzo in gani in kana gida kazo kayi mata dressing kada jininta ya k’are”.Ta k’arasa maganarta cikin b’acin rai da jimamin abinda ya faru.
Had’a baki sukayi tare sukace”subahanillah!Yaushe wannan tsautsayi ya sameta?”.
Duk’ar da kanta tayi tace”yanzu ne abin ya faru ina barci taje d’ibar ruwa abuta shine Haseena ta tunkud’eta itada Suhail suka fad’i k’asa bako tausayi”.
Saliha tace”agaskiya Basheer ya b’ata gidansa saboda duk walak’ancin da Haseena zatayi miki keda yaranki shine silar faruwar hakan, saboda bai mayardake ba abakin komai ba a gidansa sannan ya nuna mata baki kowa awurinsa”.
Salisu ya mik’e tsaye tareda shiga cikin d’aki ya fito da kayan aikinsa yace”kinci sa’a ban fita chemist da wuri ba bari inje inyi mata dressing d’in daga can sai in wuce,ki cigaba da hak’uri mahak’urci mawadaci ne wata rana tabbas akwai *RANAR NADAMA*”.
Yana rufe bakinsa ya sanya kai yayi ficewarsa daga cikin gidan yayinda Saliha ta dubeta tace”Naja’atu kina ganin jarabawa iri iri agidan aurenki ubangiji ya baki ikon cinye jarabawar rayuwarki, agaskiya kina cikin tasku da *K’ANGIN RAYUWA*”.
Kwalla ce ta zubo afuskar Naja’atu ta gogeta tace”ya zanyi da rayuwata Saliha kullum kullum masifar da zata tunkaroni daban yake babu inda zan saka raina inji sanyi azuciyata, wurin miji babu dad’i wurin kishiya babu dad’i wannan wace irin k’addara ce mai cikeda tashin hankali da bak’in cikin rayuwa? Agaskiya nayi nadamar auren Basheer arayuwata saboda duk abinda ya sameni shine sila”.
Saliha ta dafa kafad’arta tace”ki daina cewa kinyi nadamar aurensa Aminiyata inason ki kasance cikin masu imani da tawakkali arayuwarsu, duk abinda yake faruwa dake rubutacce ne awurin ubangiji tun ranar gini ranar zane, saboda haka ki rungumi k’addararki hannu bibbiyu komai zai wuce kamar bai tab’a faruwa ba”.
Naja’atu tace cikin sanyin murya”na amshi k’addarata hannu biyu k’awata amma kinsan abin ne da ciwo arayuwa duk yadda kike ganin ina walwala azahiri a bad’ini bak’in ciki da damuwa suna nan cunkushe cikin zuciyata, ina jin tsoron kada wani mugun ciwo ya sameni adalilin bak’in ciki da takurawar Basheer”.
“ki daina fad’ar haka da yardar Allah babu abinda zai faru dake sai alkhairi”.
“Allah ubangiji ya k’addara”.
“amin”.Inji Saliha cikin tausayin k’awarta.
Naja’atu tayi huci mai zafi tace”bari in koma wurin ‘ya’yana kada ta shiga ta kashe mini su in shiga uku”.
“tana farawa ‘yan sanda su kamata dan ubanta bari in baki wani abu ki kaiwa yaranki “.
“da kinbarshi kawai Saliha”.
“ai bake zan bawa ba ‘ya’yana zan ba”.
“to ai shine nace ki barshi kawai”.
Saliha ta mik’e tsaye tace”ki daina fad’ar haka ba’a mayarda hannun k’yauta baya “.
“naji”.Inji Naja’atu tana murmushi alokacin ne taji wani irin sanyi azuciyarta damuwar da take ciki ta d’an ragu, shiyasa ba’a son mace mai yawan zurfin ciki domin barin damuwa cikin zuciya sau da yawa yakan haifarwa mata babbar illa arayuwarsu, duk da yake ba kowace mace zaki fad’awa sirrin dake zuciyarki ba amma akwai wadda kika aminta da ita d’ari bisa d’ari wadda kikasan bazata bayyana miki sirrinki awurin mutane ba, saiki gaya mata ko damuwar da kike ciki zata kau ko ta ragu.
Saliha ta shiga cikin d’akin bata dad’e ba ta fito da leda ahannunta ta mik’awa Naja’atu tace”Allah ya bata lafiya saina shigo anjima in ganta”.
“Amin ya rabbi”.Cewar Naja’atu ta mik’e tsaye.
Saliha ta rakata har bakin k’ofar gidan Basheer Naja’atu ta wuce ita kuma ta juya ta koma cikin gidan mijinta.
____________________
Naja’atu ta shige cikin d’akinta ta iske har Rufaida taji sauk’i sosai domin har yayi mata dressing a inda taji ciwo tareda bata magunguna k’yauta, isketa tayi zaune itada Suhail suna cin indomie da k’wai mamaki ne ya wanzu afuskar Naja’atu ta kallesu tace”Rufaida waye ya siyo muku indomie da k’wai?”.
Rufaida ta shagwab’e fuska tace”Baban Rayyanu ne da yazo yayimin wankin ciwo ya bani magunguna yana fita bada jimawa ba ya aiko Rayyanu yazo ya kawo mana indomie da k’wai “.
Ajiyar numfashi tayi tace”Allah ya saka masa da Alkhairi ina fatar kinyi masa godiya ko?”.
“nayi masa Ummi”.
“ya kan naki ya rage yi miki ciwo ko?”.
“eh ya rage”.
“Allah ubangiji ya tsare gaba”.Tashi tsaye Naja’atu tayi ta cire tufafinta ta fad’a cikin toilet tayo wanka tana fitowa ta shafa mayukanta ta sanya riga da zanen atamfa, d’inkin yayi mata k’yawo sosai tareda k’ara bayyana tsantsar k’yawonta duk dayake bata cikin natsuwa da kwanciyar hankali agidan aurenta, powder kawai ta shafa afuskarta ta dawo wurin ‘ya’yanta tanayi musu labarai masu dad’i suna dariya.
********************
Haseena tana zaune tana kwalliya saiga shigowar yah Basheer kai tsaye cikin d’akinta da leda ahannunsa, juyowa kawai tayi ta kallesa ta b’ata fuska sannan ta kauda kanta gefe kamar bataga shigowarsa ba yah Basheer ganin bai samu irin tarbar da yakeso ba yaji jikinsa yayi sanyi hankalinsa ya tashi, cikin fargaba da tsoron fushin Haseena ya iso wurinta gabansa yana d’ar d’ar d’ar zaunawa yayi ya aje ledodin agabanta marairaicewa yayi kamar zaiyi kuka yace”waye ya tab’amini babyna naga rayuwarta ta b’ace ?”.Kallonsa Haseena tayi tana yamutsa fuska cikin b’acin rai tace”wannan banzar matarka ce ta dinga zagina akan kawai nace Rufaida tazo in aiketa ta siyomin lemun gora “.Yah Basheer yatsura mata idanu yace”zaginki tayi akan kin kira Rufaida? “.Haseena ta gyad’a kanta tace”kana mamaki ne shiyasa ka sake tambayata ko aganinka k’arya zanyiwa matarka? “Yah Basheer yayi sauri ya rungumesa ajikinsa tsantsar bak’in ciki da b’acin rai ne kwance afuskarsa yace “sorry babyna ba haka nake nufi ba yanzu dai bari inje wurinta inji dalilin da yasa ta zagar mini ke! “.Ya fad’a aharzuk’e cikin tsananin b’acin rai da tafasar zuciya. Zai mik’e tsaye kenan ta chapko hannunsa ta rik’eshi cikin kisisina da munafurci tace”ka bari anjima idan ka huta sai muje tare ayi komai agabana kada tace nayi mata k’arya, “.Yah Basheer ya zauna yana kallonta cikin so da k’auna yace “kiyi hak’uri babyna zan d’auki mataki akan Naja’atu insha Allahu hakan bazai koma faruwa ba”.Zumb’ura baki tayi cikin yanga tace”karka damu darling komai ya wuce awurina tashi muje inyi maka wanka “……….
[11/20, 5:47 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????
*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sis Najer’art*
_Free page._
*PAGE 8*
Kallon k’auna yake jifarta dashi alokacin ne yakejin wani irin sinadarin sonta da k’aunarta yana yawo cikin sassan jikinsa da zuciyarsa, murmushi yayi mata yace”to Hasee baby shiyasa nake k’ara sonki saboda k’yawawan halayenki”.Haseena tayi masa kiss akumatu tace”ina sonka mijina saboda yadda kake bani kulawa na musamman tareda nunamin tsantsar *SOYAYYAR GASKIYA* banda abin so da k’auna sama dakai farin cikina”.Tabbas kalamanta sunyi matuk’ar tasiri azuciyarsa alokacin ne yaji wani irin shauk’in soyayyarta yana fisgarsa, farin ciki ne ya gauraye cikin jininsa kallo d’aya zakayi masa ka gano yana cikin nishad’i dak’yar yace mata”naji dad’in kalamanki agareni tabbas kina sona da gaskiya, nima k’aunar da nakeyi miki batada adadi arayuwa shiyasa banason inyi miki abinda zai sakaki b’acin rai ko damuwa”.
Cikin jin dad’i Haseena ta fara cire masa tufafinsa tace”bakada damuwa muddin ina numfashi aduniya zanyi maka duk abinda kakeso domin raina fansa ne agareka”.
“ina godiya da soyayya babyna Allah ubangiji yabarmu tare har abadan da’iman”.
Light kiss tayi masa tace”Amin darling”.
Tana gama cire masa tufafinsa taja hannunsa suka shige cikin bathroom, sun jima tanayi masa wanka daga baya suka fito manne da juna kamar zasu had’iye junansu akan so da k’auna, cikin tsakiyar d’akin suka shigo sukayi masauki saman gado rungume da juna jikinsa yana gugar nata, Haseena ta kallesa tace”bari in shafa maka mai”.
“ki barshi kawai bana buk’ata kwanta muyi barcinmu”.
Haseena tayi fari da idanunta tace”to abincin fa baza kaci ba?”.
“banajin yunwa”.Ya fad’a sannu ahankali yana lumshe idanu.
Canza fuska tayi zuwa yanayin damuwa tace”mi kaci awaje ne? “.
Shafar jikinta kawai yakeyi yana murmushi yace”aschool nasha yoghurt naci nama”.
Gyara yanayin fuskarta tayi zuwa fara’a sosai tace”ok i think kaci abincin kasuwa ne”.
Girgiza kai yayi yace”kema kinsan bazan iya cin abincin kowa idan ba naki ba”.
Taji dad’i sosai ta k’ara mannewa afaffad’an k’irjinsa sai ajiyar zuciya takeyi tace”ina alfahari dakai mijina”.
“nima haka”.
Jawo blanket yayi suka lullub’e jikinsu suna mutsurniya acikinsa, suna rufe cikin blanket ya dinga aika mata zazzafan sak’onni tana mayar mishi da martani, motsinsu kawai ake hangowa mammatsa boobs d’inta ya dingayi yana cika hannu bibbiyu cikin sha’awa, ita kuma sai k’ara mak’alewa takeyi ajikinsa tana k’ara bank’aro masa boobs d’inta tana nishin dad’i, yamutsa junansu sukeyi cikin salo da k’warewa akan harakar, dinga rud’ata yayi salonsa tareda rikita mata lissafi ita kuma sai kukan kissa takeyi masa da wani k’ara narkewa, sun jima suna yamutsa junansu sannan yah Basheer ya ware mata k’afafunta ya cilla k’wallonsa cikin raga..
____________________