HAUSA NOVELRAYUWAR HUMAIRA Complete Hausa Novel

RAYUWAR HUMAIRA Complete Hausa Novel

 

[30/09 11:23 AM] Aishat muh’d: [30/09 10:33 AM] aishat muh’d: 24RAYUWAR HUMAIRAT
ihun dayakejine yatayar dashi daga baccin dayake yamike ahankali yaje jikin windo yaleka mezai gani humairat durkeshe tana kuka ga belt a hanun dad da alamun dukanta sukayi…su kultum kuwa waka sukeyi mata Amalala mai fitsarin kwance ta tsula takuma tsulawa tabar anty ta da wanke wa kausar ne takaraso wajen tace naci ubanku tadaibar uwarta ta kabari da wankewa baniba…wani bakin ciki yatasoma islam da sauri yakoma yabude kofa yafita wani kallo yabi kanen nashi dashi nan da nan kowacce ta kama kanta sumi sumi suka koma dakin mamarsu ,ya dago humairat dake kuka ya rungume batare dayaji kyaman jikinta daya jike da fitsari ba yaja hanunta haryakai bakin kofa kausar tace kabamu yarmu karka lalata mana ita…juyowa yayi yamata wani irin kallo da saida hanjin cikinta ya kada, yaja hanunta suka shiga dakinshi ya maida kofan yarufe…kausar tace haba alh bazakai magana ba, yace kyaleshi zan gyara mishi zama indai wanan yar shegiyan zai kare to wlh saina kusa kasheta a gidanan kausar tai murmushi tajashi daki..
Islam da kyar yasamu humairat tai shiru ya rungumeta chan yadago ta ya share mata hawaye ya isa kinji sis bazan kara bari a dakekiba yace zan nemo miki magani zaki dena wanan bed wet din kinji ko,oya stop crying u are my lil sis my baby i will always take care of u.. karan wayanshi ne yasa yay shiru ya dauko wayan daga aljihu ya kalli screen din yay murmushi ya amsa “hello sweetheart zan kiraki anjima am somehow engage right now …ok luv u too ya katse wayan “itadai humairat tai shiru tana jinshi yariko hanunta muje kiyi wanka yakaita har bayi tai wanka yadauko tsaraban daya siyomata daga Malaysia kayane masu kyau arab wears tasa lokacin data fito bude baki yay yana kallonta dan sun karbeta sosai sun mata kyau dama gashi kirjin nata a cike yake yace kinyi kyau taji kunya batace mai komiba shima ya shiga yacire jalabiyar ya wanke ya shanya sanan yafito yace karfa kije waje bari na je dakin anty na dauko mana abinci….yafita anty tace naji lokacin dasuke dukanta tsoron rashin mutuncin dad nake saisa ban fitoba islam yace anty wlh zan iya komi kan humairat duk randa dad yakara dukanta ko..yay shiru kawai ya karbi abincin yabar dakin.
Maman shakur
[30/09 10:51 AM] aishat muh’d: 25RAYUWAR HUMAIRAT
Yazuba mata abincin tafara ci hannu baka hannu bisa kwarya islam da mamaki ya tsaya yana kallonta shakewa tayi da sauri yabata ruwa tasha saida ta cinye yakaro mata taci rabi sanan taji takoshi tai hamdala ahankali tace yaya nagode wani yarr yaji ajikinshi dan yaune yaji magananta sosai ya kalleta yace basu baki abinci ne??tace tun jiya anty bataban ba ya girgiza kai,yace ban labarin ki tai murmushi tace yaya ni bani da wani labari kawai makaranta nakeson nakoma munyi resuming jiya nama dad magana dukana yayi tafara sheshekan kuka ni yaya nafison makaranta wlh kan gidanan ya janyota jikinshi is ok sis dazaran Abba yadawo zan mishi magana dole yasa dad ya maidake makaranta tace to kwace kanta tayi daga jikinshi dan taji matsan yay yawa..shikuma a bangarenshi baisan mesaba yana samun kwanciyan hankali da nishadi duk inyajita a jikinshi…tace yaya maisa kake taimakona??tambayar tabashi mamaki yace mata saboda ke yar uwatace kuma marainiya kaman ni,inajinki a zuciyata banason naga kina wahala nima bansan mesa ba amma banason ganinki a halin kunci ko damuwa,tai murmushi tace nagode yaya,tace yaya na tambayeka?yace go ahead tace mekafi so??yay shiru chan ya kalleta yace yara i luv children a lot inason innai aure matata ta haifamin yara dayawa inason yara sosai tai dariya tace wlh yaya nima inason yara.tace amma yaya ko yanzu zaka iya samun yara basai kai aureba kawai cemata zakiyi inason yara kiyi ciki ki haihu tunda tana sonka zakaga tai cikin tai haifi yaran dayawa yaya….kallonta ya tsaya yanayi yarinta ne akanta sosai yace hw old are u??tai murmushi tace 15 yace a school kinada kawaye tace yaya ni bantaba yin kawa ko dayaba hakanan bansan mesaba ban samu irinaba a zuciyanshi yace no wonder…tace yaya yanzu inkaje wurinta zaka cemata tai ciki tai haihu ko??yace wace??tace ba dazu naji kace sweetheart ba kuma nasan haka anty kecema dad ,tace kaga yaya inta haihu zan dinga goya yaran ai zaka bari ko??yace eh mana y not lil sis dina zata kulanmin da yarana tai murmushi yauwa yaya promise??yace promise sukai shaking hannu…
Maman shakur
[30/09 11:22 AM] aishat muh’d: 26RAYUWAR HUMAIRAT
Yace humairat dama kinada magana haka??tai murmushi tace yaya inada magana kuma kaga kai ina sonka kana hana adakeni saisa i feel free and safe wen ever am with u yaya kwalla ya ciko idonta tace yaya number 1 u are my yaya ,number 2 u are my friend, number 3 u are my saviour, number 4 tai shiru zan fadanma amma ba yanzu ba kawai kallon yarinyar yake tana burgeshi yarinyar very sharp and clever,,yace zomuje dakin anty amarya tai rau rau da ido yaya wlh banason fita daga nan idan anty ta ganni ko dad dukana zasuyi kuma su komar dani dakinsu…yace to shikenan zauna anan…da azahar yace tai salla bari yatafi masalaci yafito har key saida yasa yakulleta yatafi bayan an idar da salla yafito daga masallacin yakira Abba saida yafadama Abba komi ran Abba yabaci sosai yanzu abunda sukema yarinyar kenan dama gobe zan dawo zan gamu da usaman hakadai sukai sallama.. yashiga gida dakin anty amarya yatafi yazauna suka gaisa yace anty yanzunan nagayama Abba komi amma anya Abba zai iya taimakon humairat kuwa??dan naga kausar tariga tagama da dad ko Abba yamishi magana bazai jiba,yace anty kinada wani solution??ta kalleshi tace islam niko keda solution amma ina fargaba dan ba lallai bane ka yardaba kuma ina mai tabbatar ma inhar kai hakan babu mai iya cutar da humairat again, islam ya gyara zama yace anty ni aganina ko menene zan iya wlh ko kadan banason ganin humairat cikin kunci fadi naji,tace islam inhar kanason cire humairat daga kangin nan to ka AURETA gaban shibe yafadi dummm dan bai taba kawo tunanin aurentaba,anty ta cigaba da magana inhar ka aureta kanada right ka cireta daga gidanan,daga hanun kausar, inko ba aurenta kayi ba kwana nawa zakayi a gida ka koma camp dinku dake port Harcourt??ni bazan iya taimakontaba saboda dad, amma inhar ka aureta ka dauketa kubar kano ka kaita chan port Harcourt tacigaba da makaranta tace islam ina tausayama humairat ina tausayama rayuwar ta, wlh kausar zata iya kasheta tunda har ta iya kashe mamanta saisa nafiso ka aureta ka janyeta kubar gidanan kaima hankalinka zaifi kwanciya nima haka Abban kama haka,,tace islam humairat yarinya ce mai shiga rai abar kaunace ga kowa i understand nasan baka sonta but i assure u inhar ka zauna da humairat wlh saika sota saboda kyawawan dabi’unta ,nama humairat alkawari nazama mamanta tace kuma a matsayina na uwa a gareta ban hango mata wani namiji dazai kula da ita ya raineta har ta girma ba kaman kai tace islam bancema dole ba just think about it kayi tunani da kyau u are my onlp hope 4 saving humairat islma…
Maman shakur
[30/09 9:55 PM] Aishat muh’d: [30/09 8:21 PM] aishat muh’d: 27RAYUWAR HUMAIRAT
Islam yay shiru chan yadago da idanunshi dasukai ja yace anty i will think about it,tace ok take ur time kadai make sure kayi tunani kan maganar da kyau yace to anty…ta dauko abinci a kula tabashi yakarba yadau two plates da two spoons yajuya yafita duk jikinshi yay sanyi….
Yana zuwa yabude dakin yashiga bama tasan ya shigo ba tana chan hankalinta nakan TV tana kallon cartoon ya kura mata ido bai taba jinta daban a ranshi ba sai yanzu but y??ahankali yamaida kofan yarufe yakarasa wajenta yace humairat tadago ta kalleshi tace laa yaya kadawo?yace yes,ga abinci muci ta zuba mishi yace kara muci tare taimai murmushi daya kawata fuskarta dimple dinta suka lotsa ta zuba tasa spoons suka fara ci kadan kadan takeci abincin ahankali batare da hadama ba gabaki daya ta tafi da imaninshi yarinya akwai hankali ga natsuwa wurin cin abinci…
Luv kanaji dai ko nariga nafadama dole gobe muje da humairat adaurata kan kada (crocodile) yace but luv ….kausar ta tari numfashin sa banason naji wani abu daga gareka ko bakason yarka ta warkene??yace inaso mana tace kasan yawancin yara masuyin fitsarin kwance ana daurasu akan kada ko zaki(lion) wanan tsoratar dazasuyi zaisa kaga bazasu kara yin fitsarin kwance ba yace to luv yanda kikeso hakan zamuyi,amma inane wurin tai murmushi tace wata kawata tamin kwatance itama yarinyar ta takai shekara 17 amma tana fitsarin kwance shine aka kaita aka daurata akan kadan tunda ga ranan bata karayiba…ana kiran wurin MAGANIN AMALALA yana hanyar by pass yace shikenan amma ai tana dakin islam kuma kinsan bazai bariba tace kabar komi a hannuna dole zatama fitone yace to shikenan luv….
Maman shakur
[30/09 8:41 PM] aishat muh’d: 28RAYUWAR HUMAIRAT
Har bayan isha humairat tana dakin islam bai bari tafita wajeba itama batai gigin fitaba dan tasan gamuwarta da kausar ko dad….
Islam ne ya kalleta yaga tana ta hamma da misalin karfe 9 nadare yace bacci ko??tace eh,yace jeki kwanta akan gado nan da nan hankalinta yatashi tafara kuka sosai yaya kabari anan zan kwana banason nabatama gadonka,mikewa yayi yazo kusa da ita ya share mata hawaye yace shii Humairat bazan taba kyaman kiba ciwo ne kuma babu wanda yafi karfin jarabawan Allah kinji kullum fatana addu’a ta gareki shine Allah ya yaye miki matsalan kinjiko humairat, oya muje ki kwanta ya dagota ya rike mata hannu har gado yakaita ta kwanta yarufeta da bargo…saida yakai bakin kofa tace yaya yajuyo batare daya amsaba tace kasan menene number 4 din??yace a’a tace kaine dady na saboda kana sona baka kyamana kanamin abu kaman yanda dad yakemin da kafin ya tsaneni amma yanzu kaine dady na tundashi baya sona. dawowa yayi yay huging dinta sosai yana shafa kanta karki damu humairat ur dad luvs u alot nan gaba zaki gane hakan da kyar yasamu ta dena kuka yafita yana kara tunanin humairat aranshi….daga baya ya dauko waya suka soye shida budurwarshi farida…
Dasafe humairat tatashi taga taima yaya amalala a gado tadinga kuka ya shigo yasameta ahaka yagane abunda yafaru yace mata kidena kuka kiyi addu’a Allah yaye miki jekiyi wanka tashiga wanka shikuma yadau katifan yakai waje dan tasha iska yana dawowa daki aka kirashi ana son ganinshi yanzunan a headquarter dinsu dake kano sharp sharp yashirya cikin kayan Air force din yaje dakin anty yadauko mata abinci danshi baida tym din ci…humairat duk hankalinta yatashi yaya fita zakayi wlh dad zaizo ya dauken yace karki damu bazan dadeba karki fita,saikin fita wajene zasu ganki kinji ko dakayr tadena kuka yawuce yafita yace mezan siyo miki tace crackers yace to bye takecare yafita yaja motanshi yatafi ashe kausar taga fitanshi….
Maman shakur
[30/09 9:14 PM] aishat muh’d: 29RAYUWAR HUMAIRAT
komawa daki tayi da sauri luv oya tashi mutafi islam yariga yafita. kura mata ido yayi baisan mesa baya iya mata gardamaba har cikin ranshi bayason a daura humairat kan kada karyazo ya cijeta ko kuma yahadiyeta, dan bazai taba mantawaba akwai wani abokinsu lokacin suna matasa shekara 18 yana fitsarin kwance iyayenshi suka kaishi aka daurashi akan kadan sai ihu yake aiko tsautsayi mistakenly kadan ya cijeshi akafa tundaga lokacin yadinga ciwo har ya mutu saboda akwai dafi a hakorin kada kuma masu kadan sunce baya cizo ….tunanin me kake haka cewar kausar,yamike bakomi yashirya suka fito direct dakin suka bude suka shiga lokacin humairat na kallon cartoon hankalinta kwance..ganin su yasa tamike tafara ihu wayyo Allah kutaimaken zasu kasheni jikinta rawa yake,kausar ne takarasa wajen munafuka yimana shiru taimakonki xamuyi za’a dauraki akan kada daganan baxaki kara fitsarin ba arude tace anty kada??wlh inta fitsarin indai kada ne maganin, tsoron kada nake anty a natgeo wild fa ana nunowa kada na cinye mutane..dad ne yaxo wajen ya wanka mata mari ba shawaranki muke nemaba dan uwarki muje yaja hanunta iya karfinta ta daddage ta fixge hanunta wayyo yaya islam come back dey want to kill me dad ya tokareta a ciki mune zamu kasheki kasa ihu tayi saboda azaba,chak dad yadauketa suka fito waje tsakar gida hango hassan da hassanat tayi suna ball tace hasanat kifadama mama na zasu kasheni zasu daurani kan kada,kausar ta nushi bakin nata dan ubanku kucema uwarku munje nema mata magani za’a daurata akan kada suka sata amota dad yaja motan sukabar gidan…
Maman shakur
[30/09 9:55 PM] aishat muh’d: 30RAYUWAR HUMAIRAT
Da gudu su twins suka koma daki suna haki dama hasanat tafi iya shatato zance tace mama su dad da anty sunsa humairat amota wai zasu kaita adaurata kan crocodile hasan yace kada mama,anty amarya tace wot?crocodile it cant be they must be crazy zasu kashe humairat ne??sunsan tanada tsoro yarinyar nan ooo wot do i do now?duk ta rude, wayanta ta dauka takira islam lokacin yakawo gate baidau wayan ba katsewa yayi yay parking direct dakin anty yayi dan jin dalilin kiran..da sallamanshi yashiga yaga twins na kuka anty kuma dukta rude yace lpy anty maiya faru??nan tafadan mishi abunda yafaru rudewa yayi sosai yace anty kinsan wurin ne tace eh hanyar by pass ne yace muje dukya rude wanan wani irin rayuwane uba na wulakanta yar cikinshi da kyar suka lallaba twins suk zauna a daki suna fitowa sukaga Abu a tsakar gida kaman da gaske fuskar damuwa tayi tana ganinsu ta mike wurin zaku dan Allah zan biku abun nasu kausar yay yawa kar yarinya taje tamutu…wlh mutanen karya suke suna cewa wai kadan basa cizo amma wlh cizo suke sosai islam ganin zata bata musu lokacin da surutu yace inzaki kizo muje bamu tambayeki komiba ranshi yariga yabaci…
Suna shiga mota gudu yake kaman zai tashi sama wayanshi yaciro daga aljihu yakira Abba yafada mishi komi Abba yace my son calm down yanzu nan na sauka a airport kuje nima zan sameku a wurin inanae wurin ganin zaije yabige mota yasa yaba anty wayan taima Abba kwatance yace gashinan zuwa gudu yake kaman zai tashi sama…
Bangaren humairat kuwa ……….
Maman shakur
[01/10 11:47 AM] Aishat muh’d: [01/10 10:32 AM] aishat muh’d: 30RAYUWAR HUMAIRAT
Suna shiga wajen taga gidane babba mutane dayawa a wajen dan ana kawo yara amalala sosai a tsakiyan filin wani katon ruwane kaman swimming pool saida ruwan mai kaman kasa kasa ne saidaga wani bangare daban na barin ruwan wani katoton crocodile ne but an kulleshi yana cikin protector…humairat bata komi sai kuka ta kalli babanta dad inhar ka daukeni a matsayin yarka dan Allah kar adaurani a kan crocodile i will just die dad ko kallonta baiyiba dan dazaran yahada ido da ita sai yaji ya tsaneta..kausar ta riketa shikuma dad yaje yabiya kudi naira dubu biyar,aikuwa guards din wajen da dad suka dawo suka karbi humairat. humairat bama ta iya ihu da kyau muryanta ta dishi bata taba ganin tashin hankali irin nayau ba live crocodile yau tagani kuru kuru amma wai akanshi za’a daurata ….
Guards din suka sata a layi aka manna mata number a jikinta itace number 8 kowa a layin kuka yake dan duk amalalai ne humairat ma kuka take…..gani sukayi an bude crocodile din yafito masu tsareshi kansu yafi karfinsu da kyar suke iya tankwarashi nan da nan su humairat da sauran yaran ihu suketayi ko wacce na kiran
iyayenta.aka fara number 1 tazo aikuwa yarinyar taki zuwa ta kankame sauran yaran wani guard ne yazo yadauketa chak kaman yarinya tana ihu tana kururuwa tana turje turje amma ina saida aka daurata akan crocodile din wani wawan ihu tasaki ta sume bata kara sanin inda kanta yakeba minti 10 dama sukeyi akan crocodile aka daukota akai kaima iyayenta ita ahaka a sume…akazo kan number 2…
Islam gudu yake sunkawo wajen akaki barinsu shiga saboda wai ba’a gansu tare da yara ba da kyar aka bari suka shiga lokacin dasuka shiga ankai kan humairat wanda take ihu kawai sunan Allah take kira tareda na yaya…Allah katuromin yaya wajennan shikadai ne zai iya ceceni Allah ka tausayamin nasan inhar aka daurani kan abunnan mutuwa zanyi kuka take sosai.islam wajen dad yaje ya cakumeshi anty tana cewa bakada hankaline amma ko jinta baiyi yace ina kanwata?inkai baka bukatarta mu muna sonta dad ya hankadashi yafadi akasa dago kan dazai yi yaga wanan guard din yadaga humairat za’a kaita wani tsalle yayi yadira a gaban guard din ya kwace humairat a hanunshi wanda tama riga ta suma tun kafin asata ya rungumeta tsam a jikinshi humairat am here weak up i will always protect u ya daura hanunshi kan goshinta i swear by Allah i will marry u humairat take care of u….no one and nobody can separate us…
Dad ne yataho azuciye yacema islam kabada yata adaurata nazo nemama mata magani ne islam yakara matseta a jikinshi yace duk abunda zakayi kayi amma wlh bazan badataba yajuya ya kalli kausar tace mishi yafi karfin kane dakeshi wlh dad ya waiga ya hango wani guard yana rike da dorina mai baki 8 yaje wajen yakarba….
Maman shakur
[01/10 10:46 AM] aishat muh’d: 31RAYUWAR HUMAIRAT
Ya karbo dorinar,filin gabaki daya su ake kallo,dad yace islam kabada humairat nace, islam yakara matseta bazan badata ba wanan abun baya aiki is just fraud kudinku sukeci mutane nawa ake daurawa amma basu denayin fitsarin kwance ba dad wlh do ur worse amma bazan taba bari adaura humairat ba, dad yace ok dont blame me cos u ask 4 it ya daga dorinar iya karfinshi ya daddage ya laftama islam abaya islam yay kara sosai amma bai saki humairat ba tana jikinshi yana rike da ita gam…wani ihu anty amarya tayi alh karka kashemana yara,dad yakara daga dorinar ya kuma laftama islam abaya amma still bai saki humairat ba idanunshi sunyi ja koda yay training air force ba’a taba dukanshi haka ba arayuwarshi dad yace bazaka saketaba yakara daga dorinar zai kai mishi ta uku yaji an rike dorinar gam juyowan dazaiyi yaga yayanshi ne alh usman..
Abba yace ba islam zaka dakaba niza ka daka danni naturoshi nan wajen dad sakin dorinar yayi akasa alh usman baicema dad kalaba dan suna gaban mutane ne ya karbi humairat daga hanun islam yaja isalma din da anty da Abu wanda dadi ne yakasheta yanda taga islam yasha dorina itadai arayuwarta ta tsani islam suka shiga mota sai asibiti…..akai treating bayan islam dan ya fashe sanan akaba humairat gado tare da allurai da kuma drip ba ita ta tashiba sai washe garin ranan tanata ihu tana kiran yaya da sauri ya rungumeta yace ganinan da doc yadubata yaga taji sauki yabada sallama suka koma gida tana like da yaya abunta..
Maman shakur
[01/10 10:58 AM] aishat muh’d: 32RAYUWAR HUMAIRAT
Da suka koma gida yakai humairat part dinshi ya kunna mata kallo yace mata tazauna a wajen karta fito…shikuma yafito yanufi dakin Anty yasameta tana karatun jarida ta dago ta kalleshi ta cire glass din idonta yace yadai samarin Abba?yace anty i have finally made my decision na yarda zan auri humairat kuma i want everything to happen as soon as possible saboda nan da 5 day dan on Saturday zan tafi barrack dinmu na PH.anty tai murmushi tace alhamdulillah naji dadi sosai Allah yatayaka riko muje dakin Abban ka, yace to suka shiga dakin Anty ita tafadama Abba komi Abba yay murna yace son am proud of you kuma nagode dazaka kula da humairat nasan kome baban ta keyi baya hayyacinshi yana cikin shairin mace amma in sha Allah zamu dage da addu’a komi zai dawo normal yanzu tashi ka kiramin dad da kausar din yamike har dakin ya kirasu sukazo kowa aka zauna..Abba yace usama yace naam yaya inason kaba dana islam auren yarka humairat danni bazan tsaya kuna cutar da humairat agabana ba, kausar jitayi kaman andaba mata wuka a wuya, dad ya kalleta ta ballamai harara ya dago yace yaya kabani nan da gobe zan fadama amsa Abba yace shikenan zaka iya tafiya yatafi…islam ya kalli babanshi da anty yace Abba inada magana yace fadi ya sosa keya yace wlh Abba akwai wata yarinya danama alkawarin aure sunanta farida tana nan cikin hotoro ne…
Maman shakur
[01/10 11:44 AM] aishat muh’d: 33RAYUWAR HUMAIRAT
Abba ya kalleshi yace islam bazan taba hanaka aure ba kai mijin 4 ne amma abunda nakeso dakai ka rikemin humairat amana ka kula da iya ka maye gurbin mamanta, yace islam yadago ya kalli Abban yace duk randa naji ka wulakanta min humairat saboda wata bare wlh saina sabama…zamuje mu tambayama auren faridan kuma zamuyi bincike kanta amma saidai ita bikinta dole kujira nan da 3months saboda inason nahada bikin dana kaninka su kultum da babelo duk rana daya zamuyi,meanwhile naka dana humairat kuma ran Friday jibi kenan zamu daura a masallaci bayan sallan juma’a sai ku koma PH tare kasata a makaranta sanan ka komar da ita wajen anty amarya dan bai dace tana kwana dakin kaba yace to Abba.shikenan Allah shima albarka Allah tayaka riko yace Amin yamike yafita…
Anty tace islam na kama dakai akomi hali,dabi’a, tausayi, komi dai kaine Abba yay murmushi yace ni nawasane to duk yarana dani suke kama bakiga yan biyu ba ma anty amarya ta murgudamai baki bawani nan ya manna mata kiss yace i luv u nagode da kula da islam da humairat tace mai shii mention not duk yaranane daganan suka cigaba da farantama juna rai..
Wlh bazai yuba bazata taba sabuwaba wai taba nonon sirika bazan taba barin islam ya auri humairat ba nafadama wlh karka sake ka yarda kanajina ko yace to luv naji…
Maman shakur
[01/10 11:45 AM] aishat muh’d: 34RAYUWAR HUMAIRAT
Yanda Abba yace haka islam yayi ya komar da humairat dakin anty amarya sai wasa suke ita d twins shikuma yakoma dakinshi…
Cikin dare Islam yaji kaman an mintsileshi yafarka daga bacci ya kalli agogo misalin 2:05 ya shiga bayi yay alwala yafito falo harya tada kabbaran salla sai yaji kaman motsi yakara kasa kunne tabbas motsine wanan to menene barawo ne yashigo gidan???komawa yayi uwar daka yaciro bindigarshi da wayarshi yabude kofa ahankali yana tafiya sadaf sadaf yanatajin mitsin towards garden yakoyi hanyar wurin
Itakuma lokacin kausar na kiciniyar hada gawayi ne danyin turaren haka ya dinga bi yana kaiwa garden din yalabe bayan bishiyar mangoro mamaki ne yakasheshi dayaga kausar na hada garwashi a kasko sai fifita take chan daya kama yaga ta dauko wani turare tasa a garwashi ta mike tsaye ta daga abun sama takira Humairatttttttttttt, sa hanunshi yayi cikin aljihu yafito da wayarshi ya dauketa photo flash light din daya haskata ne yasa tasaki kaskon akasa tajuya da gudu takoma daki turaren dabata karasayiba kenan,islam yakai wajen yakashe wutan yadau ledan turaren yatura aljihu yakoma daki ya zauna yana tunani humairat takira metakeson yima humairat?god! yanzu wanan kuma wani irin matsala ne? ya tashi yay salla yadinga rokon Allah yakare humairat daga shairin kausar….kausar ranan baccin dabata koma ba kenan tsoro ya cikata waye yaganta dahar yadauketa hoto na shiga uku…..washe gari islam bai fadama kowa abunda yafaruba tun safe suke jiran dad yazo yanada amsa yaki islam yasan kausar have something todo with it dan haka yace is time to put a stop to kausar drama once and for all ya mike yayi hanyar dakin
Maman shakur
[02/10 11:12 AM] Aishat muh’d: 40RAYUWAR HUMAIRAT
Farida [01/10 1:50 PM] aishat muh’d: 35RAYUWAR HUMAIRAT
Yariga yasan dad bayanan ya shiga dakin yasameta tana zaune ko gaisheta baiyiba yace nazo nai magana dake, ta daure fuska bani bukata barmin daki yace dole ki sauraren ,yace mata kisa mijinki yaban auren humairat, tace inna kifa?yay wani mugun murmushi yace i will expose u, mikewa yayi yakarasa wajenta yaciro wayanshi ya nuna mata hoton ta jiya lokacin data rike kasko sanan ya ciro turaren ya nuna mata,yace kausar inada enough prove dazan kaiki gidan yari,idan baki sanibaya yau kisani inada evidence daya nuna cewa kece kika kashe maman humairat, kausar ta mike tsaye ta dafe kirjinta au shairi zakamin yay wani bazawarin murmushi dont act smart with me,and stop pretending inada good three evidence dazan iya turaki prison amma banyiba saboda ina tausayin danki kabir banason yataso cikin maraicin uwa but inhar kikai gigin hana dad ban auren humairat i will not think twice and i will not hesitate to put u behind bars nafada miki,yace inhar naga wani abu yakara samun humairat koda dukanta kika kumayi yay kwafa yajuya haryakai bakin kofa yajuyo yace dont forget is a THREAT yajuya yafita…kausar was completely speechless wanan yaron islam ya dagula mata lissafi yanzu wot do i do now??shine tambayar datakema kanta da inje prison gwara nahakura anyi auren takira dad awaya dawo gida yanzunan, ko minti 5 baiyiba yadawo tace mishi tayarda aiyi auren yako fita yafadama Abba washe gari bayan jumma’a aka daura auren HUMAIRAT da ISLAM akan sadaki dubu 80 islam sai murna yake…
Kausar ce take yawo a tsakiyar daki da alamun damuwa a fuskarta tai wani shewa yaro inkasan wata bakasan wataba…i made a vow to make humairat life be a living hell dan haka no going back i will not give up muzuba nidaku….
Maman shakur
[01/10 2:21 PM] aishat muh’d: 36RAYUWAR HUMAIRAT
Da daddare bayan su twins sunyi bacci anty ta kira humairat dakinta taje har dakin tace gani mamana tace zauna, ta zauna kusa da ita tace inaso kisani cewa an daura miki aure da yayanki islam ke yanzu matar aurece kinajinako?tace eh duk abunda yace kiyi karkiyi rashin ji kinji humairat, gobe zaku koma port harcourt zai saki a makaranta ai kinason makaranta ko? ta dinga murna eh mamana inaso tace yauwa to…ta dauko wani ruwan addu’a wanda dazu Abba da islam sukaje gidan liman yafadan mishi rashin lafiyan fitsarin kwance ta shine yay musu addu’a cikin ruwa a jarka guda yace kullum dare kafin tai bacci tasha sanan ta karanta ayatul kursi iklas falaq da nas sanan ta kwanta da yardan Allah koda jinnu ne kokuma sammu bazaiyi tasiriba zai karye, shine suka karba suka dawo gida yabama anty ta dingaba humairat..taba humairat oya sha takarba tasha sanan anty tace oya karatan ayatul kursi tako karanta iklasa falaq nas duk ta karanta sanan anty tace to jeki kwanta taje ta kwanta akan gadonsu kawai tunanin zata koma makaranta take dan bata riga tasan takamaimai menene aure ba saisa batadamu da wanan ba..
Washe gari ikon Allah batai fitsarin ba murna wajen humairat da anty kaman me anty tasa tai wanka takawo mata kaya Abaya ne black mai stones blue, anty ta nannada mata gyalen tai kyau sosai karfe 8 anty ta shiryata tagama komi taja hanunta sukai dakin Abba anan suka tarar da islam shima ya shirya cikin bakin suit sai kollon humairat yake kaman bai taba ganin taba Abba yay musu nasiha sosai
yacema anty takawo musu jarkan maganin dashi zasu tafi. Abba yace kuje kuyima kowa sallama islam yarike hanunta suka fara shiga dakin Abu cewa tayi ace musu tana bacci yaranne dai suka rungume humairat suna kuka daganan sukaje dakin dad da kausar suna falo islam yace dad zamu tafi dad yace Allah kiyaye daganan kausar tajashi suka shiga daki…suka koma dakin Abba daganan suka dunguma suka fito dad da Anty amarya suka kaisu Airport da humairat taga dai tafiya zatayi tabar su anty da Abba sai tafara kuka ta kankame Anty da kayar islam ya bambareta, da akazo wurin shiga jirgi tadinga ihu wai tsoro takeji ta kankame islam da kyar tashiga suka zauna sanan jirgin ya daga nan ma rikeshi tayi dan jitayi kaman hanjinta zai fito waje…
Maman shakur
[02/10 10:01 AM] aishat muh’d: 37RAYUWAR HUMAIRAT
Sun sauka a Airport na ph yakira akazo aka daukeso,tun humairat na kalle kalle harta bingire da bacci dayike da nisa sosai daga airport zuwa Air force barrack,islam ya kwanto da ita jikinshi tako kara gyara kwanciya,harsukakai gidan sanan ya tasheta, ta tashi tana kalle kalle gidan mai kyau suka shiga ciki part biyu ne gidan yabude part din humairat yace ga dakin kinan shiga bari naje nai wanka tace to…yahaura sama itakuma ta shiga dakin dakine mai kyau 2bedroom flat sai bayi da kitchen da kuma dining komi ansa cikin dakin gwanin kyau tashiga bedroom dinta tai wanka tacire kayan jikinta ta dauko wani riga mai kama da vest mai kyau blue armless yana daya daga cikin kayan da islam yasiyo mata tasa dama har guiwa ne tadau hijabinta har kasa tasa tai sallan azahar sanan ta cire hijabin ko dan kwali batasaba tafito har tsakar gida tana kalle kalle tana murmushi taba wanchan shafa wancan hartakai wajen bishiyan gwaiba,takalla taga gwaiban tayi aikuwa tahau saman bishiyan ta katso ta zauna a saman bishiyan tana ci hankalinta kwance wani irin nishadi takeji yau…..
Islam yagama duk abunda zaiyi yafito yashiga dakinta danya tambayeta mezataci amma baigantaba gadai sallaya alamun tai salla to kodai tafita ne yadinga zagaye tsagar gida dagakan dazaiyi yahangota kan bishiya tanacin gwaiba murmushi yayi yakarasa wajen,humairat ta dago kai tace laaa yaya kaima zakaci gwaiban ne? yace a’a sakko wani tsalle tayi ta diro kasa sakin baki yayi yana kallonta bai taba ganinta da irin shiganan ba ya kalli gashin kanta kaman na jariri duk anannade gwanin ban sha’awa coily dasu ya gangaro kan kirjinta yanda yaga yacika sai yaji yana neman rasa natsuwarsa da sauri ya cire idonshi daga kanta yaja hanunta suka shiga ciki ya zaunar da ita kan kujera yace humairat dagayau karki kara fita batare da kinsa hijabi ba kinji tace to
yaya.yace kin iya girki??tace a’a yace mujeto nakoya miki yanda ake dafa indomie….
Maman shakur
[02/10 10:30 AM] aishat muh’d: 38RAYUWAR HUMAIRAT
Kitchen din suka shiga, duk yay kura ya shiga store ya dauko indomie guda biyu humairat sakin baki tayi tana kallonshi, tace yaya wanan wani irin indomie ne?na ganshi kato a kano babu irinshi saidai super pack, yay murmushi yace humairat sarkin tambaya, yace wanan shine hungry man size,tace to yaya maisa babusu a kano?yace sai nan gaba hala za’a kawosu north amma dai a garinan akwai wanan dayawa, tace hmmm yace oya dauko broom ki share kitchen din ki goge nikuma na yanka albasa na dafamana indomie. tai dariya tace kaii yaya ittakullah nicefa karama amma aikina yafi naka yawa shara da goge goge, yay dariya sosai yace karki cikani da surutu yunwa nakeji dauko kifara, tace to ta shiga store ta dauko tsintsiya da parker shikuma yafara dafa indomie saida ta goge ko ina sanan tafara shara yajuyo yana yanka albasa idonshi yakai kan humairat dataketa sharan kitchen din abunta yanda take shara ana ganin komi na jikinta har boobs dinta,kara yasaki ya yarda wukan humairat tadago daga sharan datake ta yarda tsintsiyar takarasa da gudu ta rike yatsan yaya dama baka iya yanka albasa ba kakeyi gashi ka yanke kanka,ai da kabani na yanka dukta rude takai hanunshi kan famfo ta wanke jinin amma bai dina zubaba, wukar ta dauka tayaga kasan riganta ta daure yatsan dashi duk kallonta yake tashi daya yaji wani kifiyan sonta ya soki kirjinshi, dara daran idonta ta dago wanda suka cika da kwalla tace yaya sannu har yanzu yanama zafi?ganin ta rude tana shirin kuka yasa yace mata baya zafi humairat a kin riga kin dauremin tace to ta dauko stool tabashi yaya zauna ai tunda kariga kasa a wuta zan iya karasawa tadau albasan ta yanka tasa sanan tazo tacigaba da sharan duk idonshi na kanta ganin numfashin sa na neman daukewa yasa yamike yace bari na naje daki inyayi kizuba a plate sai kizo ki kirani bai jira yaji abunda zatace ba yawuce….
Maman shakur
[02/10 10:49 AM] aishat muh’d: 39RAYUWAR HUMAIRAT
saida tagama sharan kitchen din tass, sanan tazuba musu indomie din a plate takai dining, tafito tana neman dakinshi sama tahau tana yaya yaya kana ina? nagamafa,wani daki tagani ta tura kofan ahankali tare da sallama taganshi zaune idonshi yay ja tashiga tazauna kusa da shi tace yaya nagama.ya kalleta yace to ganinan zuwa,tatashi tafita yabita da kallo yay ajiyar zuciya ya mike yafito tare sukaci sai fira takemai yana dariya yanajin dadin zama da ita ranan through out bai fita ko inaba suna tare har dare…yakaita daki saida tai addu’a agabanshi sanan yadauko maganin yabata tasha sanan yakulle mata dakin yafito yatafi dakinshi ya tarar wayarshi na ringing..katsewa yayi yasake kira
Islam:Hello sweetheart
Farida:dont sweetheart me, kana tare da amarya kamanta dani?ko kakira kacemin ka isa,
Islam: yace kiyakuri bahaka bane aiki gidan muketayi ne saisa bansamu daman kirankiba…
Farida:ni Allah islam nagaji nama fasa auren naka,shekara nawa muna tare ina jiranka sai yanzu kadawo ka auri yar uwarka nice tabiyu,dan rainin hankali wai kanada dalilin aurenta wlh bakomi nafasa ma
Islam:sweetheart jiyafa da daddare danazo munyi maganan nan ki yahakuri nasan banmiki adalciba amma ai zan aurekin ko saura watama biyu,dan kinga na auri humairat inada hujjata…
Farida;mai hujjar??
Islam:kiyaha kuri bazan taba fada miki ba ,bazan iya fadamiki ba sobada sirrin tane kaman yanda itama bazan taba iya fadamata sirrin kiba..
Farida;ka kyauta dan kaga inasonka kakemin hakako?
Islam;sweetheart dont get like dat,kinsan nima ina bala’in sonki haba baby na karkija wanan abun yabamu matsala mana mubar maganan plz..oya smile 4 me tai mai murmushi haka suka raba dare suna hiran soyayya abunsu…
Wacece farida???
Maman shakur
[04/10 12:28 PM] Aishat muh’d: [02/10 6:48 PM] aishat muh’d: 40RAYUWAR HUMAIRAT
Wacece Farida??
Itace yarinya tafari a gidansu tanada kannai 4 iyayenta talakawa ne sosai mal mati da goggo madina,ahaka suka lallaba aka sata a gov school harta gama secondary da sidin goshi iyayenta suka samu kudi akasata a jami’a buk..tunda farida ta taso ita yarinya mai son kudi da rayuwar hutu, akwai ta da karya, bata yarda takawo kawayenta gidansu saboda talaucinsu,gata da son money kaman me,ana haka Allah ya tadata tawata kawarta mai kudi tsigai sunanta haka suka kulla kawance tunda tsigai ta lura farida irin maiyar kudice ta dinga murna saboda tanada buri akan farida…
Akwai wata rana ta gayyaci Farida gidanta aiko jiki na rawa taje,da farida ta shiga gidan bude baki tayi yanzu wanan gidan kine tsigai??tai murmushi tace kema inkinaso zan iya taimakonki kisamu,tace wlh tsigai inaso,ko ta halin yaya ne nidai kawai nai kudi shine damuwata,zulai tace kinyi alkawari zakiyi tace eh,nan tsigai tace mata wani kungiyane amma inhar budurwa zata shiga to dole ta bada ubanta asha jininsa, kuma inhar budurwa ta shiga ba ita ba aure, inkuma ta dage saitai aure za’a barta amma dole zatakawo wani abu as sacrifice….farida tai wuri wuri ta ido tace tsigai yanzu babanki kika bada kafin kiyi kudinan?tace eh mana me aciki ?wani guba zasu baki kisa mai a abinci yaci shikenan sai kungiya ta zuke jininshiii…farida tace zanyi kudi sosai??tsigai tace harsai kudin sun ginsheki,da tsigai ta lura farida ta shiga cikin damuwa tace dalla ke banza ce ga kudi kin tsaya kina tunani banda abunki ma ai babanki ya riga yagama yawo yanzu babu abunda zai tsinana muku yariga ya tsufa saidai yabaku wahala yanzu inkin kasheshima sai dai yaji dadi dan kin rage mishi wahala ,farida tace kumafa hakane wlh inhar xanyi kudin dazan samu wanan gidan da mota da iPhone irin nako koma waye zan iya kashewa nasamu tsigai na shirya zan shiga kungiyar….
Maman shakur

Previous page 1 2 3 4 5 6Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button