HAUSA NOVELRAYUWAR HUMAIRA Complete Hausa Novel

RAYUWAR HUMAIRA Complete Hausa Novel

 

[11/10 1:50 PM] Aishat muh’d: 89RAYUWAR HUMAIRAT
Abba shima yamike tsaye yacema islam bari naje nai magana da doc,yawuce yafita Ahanakali islam yajuyo da kanshi yana kallon humairat dan yanzu ancire mata oxygen din tana numfashi normal, yakura mata ido yanamai kara sonta, dayan hanunshi yakai yashafi gefen fuskanta, yace my sleeping beauty wake-up, kanshi ya daura kan kafadarta, yayinta hanunshi daya na rike da hanunta,lumshe ido yayi kaman yana bacci,yana tuna ranan dayafara mata kiss…..
Momy na kibarni na mutu kowa baya sona,i dont want to leave anymore…momyn humairat tashafa kanta, my baby go back lokacin mutuwanki baiyiba, kinsha wahala a duniya yanzu lokacin dazakiji dadi ne,my baby go back to ur world,Islam need u badly..humairat ta kankame mamanta but mumy nafiso nabiki, nafiso na dawwama ina mafarkin nan nidake muna tare…maman tace shiiii say no more, go! humairat go, bat humairat tadena mafarkin datake…….
motsin dayaji ne yasa yabude ido da sauri gani yayi humairat na girgiza kafa,idanunta na rawa sai chan kuma jikinta yahau rawa,…hanunta yarike yakai kan kirjinshi ahanakali yace humairat open ur eye, is me ur islam, ur yaya,wake-up plz my luv hawaye na zuba daga idonshi…ga mamakinshi yaga tabude ido tangarass tana kallonshi,ta tsura mai ido kaman tanason tuno wani abu……chan yaga ta daga hannu ta share mai hawayen dake gangara daga idonshi,ahanakali tace stop crying UNCLE KHALIL……
Maman shakur
[12/10 7:49 AM] Aishat muh’d: [11/10 6:19 PM] Aishat muh’d: 90RAYUWAR HUMAIRAT
Mamaki ne yakamashi, yace humairat am yaya islam baki ganeni bane?? Ta yamutse fuska chan kuma ta kwalalo ido laaa ka iya karya ko??uncle khalil sunanka…..badai humairat tayi loosing memory nata ba??but amma ai inhar mutum yay lossing memory komi yake mantawa maisa ta tuna sunan khalil?? Juyawa yayi zai fita ta kwalla ihu yadawo da sauri menene??tace karka fita tsoro nakeji, kallonta ya tsaya yanayi batare dayacemata komiba…yana zaune gefen gado yaji anbude kofa dad da doc ne suka shigo…humairat kwalla ihu tayi ta rirrike islam uncle khalil kace sufita,wlh kace sufita banason ganinsu, wayyo ni tsoro nakeji scorpion ta turosu su kasheni
ta rikeshi gam wanda hakan ya saukan mishi da kasala, Abba da doc kuwa sakin baki sukayi suna kallon ikon Allah meke faruwa??
Islam yace humairat kallenin, ta kalleshi Abba ne da doc bazasuyi miki komiba, doc zai dubakine kawai, tayi rau rau da ido tace are u sure uncle khalil?? yace yes am sure…doc da Abba suka karaso inda doc ya duddubata dubata duk tana rike da hanun islam dan acewarta karya gudu…bude kofa akayi khalil ne yafara shigowa sanan anty amarya…wani wawan ihu humairat tasaki tare da zabura ta sauka akan gado ta shige karkashin gado tana ihu scorpion scorpion wlh tazo zata kasheni zata aureni wayyo Allah my mumy save me, duk yan dakin sun rude Islam yafito da ita daga karkashin gadon yace humairat babu scorpion a dakin nan, tayi pointing anty amarya jikinta na rawa wlh itace baga uniform din prison ajikinta ba, kowa ya kalli anty amarya wanda lace ne ma ajikinta pink, sun tabbatar humairat ta haukace ….dama lokacin massage therapy dinta yayi nurse din dake mata tashigo humairat takara fasa ihu ta kankame islam uncle khalil kaga scorpion takara shigowa ko gatanan su biyu ..kace sufita sakin islam tayi ta waiga taga flask din ruwan zafi agefen ta dauko ta jefama nurse din wlh bazan bari ki kasheniba i will kill u first muguwa kawai,. Da gudu nurse tafita, tafara neman abunda zata jefama anty amarya, plate din abinci tagani ta dauka zata jefa mata da sauri islam ya karbe ya matseta a kirjinshi sanan yama doc signal ahanakali yatako yamata yamata aluran bacci take bacci ya kwasheta ya kwantar da ita kan gado…
Maman shakur
[11/10 6:46 PM] Aishat muh’d: 91RAYUWAR HUMAIRAT
Jikin kowa a dakin yay sanyi.. anty amarya kuka kawai take koma wacece scorpion dinan taci nasara danko ta haukatar mata da humairat…..Abba ne yay jarumtar tambayan doc wai meke damunta??tayi loosing memory ne doc??ko hauka takeyi?? Doc ya sauke ajiyar zuciya ya kallesu yace yarinyar nan is under going EMOTIONAL TRAUMA sakamakon wani abu daya firgitar da ita,ta tsorata matuka da abun,….khalil yace doc macece sunanta scorpion….doc yace no wonder tanata kiran scorpion,..yanzu dole ku kula da ita da kyau, tariga ta tsorata da scorpion so kowace mace tagani zata dinga ganin kamar scorpion dince….ba hauka takeba kuma batai loosing memory ba, kawai wahalan da scorpion din tabatane yasa brain dinta baya tuna komi sai scorpion din, but bayan kwana biyu zata dawo normal in sha Allah…..
Abba ya sauke ajiyar zuciya, doc yay murmushi yace alhji ka kwantar da hankalinka case din yarinyar kama da kyau…wata wanda muke dubawa kwananna hatsari akayi agabanta mummunan hatsari mutane sunyi daga daga agabanta saboda firgitan datayi ta tsorata taga abunda bata taba ganiba yasa yanzu ko kadan bata magana bata gane kowa inta bude baki saidai kuji tace corpses…Abba yace hakane kam alhamdulilah da Allah yakawo na humairat da sauki doc yamusu sallama yatafi…..
Maman shakur
[11/10 8:26 PM] Aishat muh’d: 92RAYUWAR HUMAIRAT
Bayan fitan doc Abba yace dafa matsala wazai dunga kula da humairat?? Anty amarya tace saidai islam tunda shikadai take yarda dashi, khalil jiyayi kaman ya mutu saboda kishi idanunshi yay ja islam ko wani murna ne yacikashi yana kallon yanda Khalil yay kicin kicin darai yay dariya azuciyarshi yace ai sai kamutu tuntuni nagane take taken ka …
Karfe tara Abba yace oya sutafi khalil yafara kame kame saida yaga anty ta daure fuska sanan yataho suka tafi….
Bayan fitansu islam yakoma ya zauna kusa da humairat yana kare mata kallo yanamai addu’a Allah yasa inta warware zata yafe mishi.. amaida aurensu, danshi jiyake bazai iya rayuwa da wata maceba sama da humairat….tunane tunane yakeyi har bacci ya kasheshi..
Da safe bayan yadawo daga masallaci ya shigo kenan yatarar humairat na kuka sosai da sauri yakarasa yace menene humairat???ta rikemai hannu bakaine kafitaba kuma kasan in scorpion zatazo ko, yarungumeta yayi sorry my princess bazan kara ba..dagowa ta kalleshi ta kuramai ido murmushi yayi yace menene??tace uncle Khalil kaman wani yataba kirana princess but namanta ko wanene shiru yayi bai kara cemata komiba….yace muje kiyi brush da wanka, mikewa tayi yarike mata hannu ahanakali take tafiya harsukakai bayin,ya taimaka mata tai brush din sanan yace bari nafita najiraki kiyi wankan, kuka tasa mishi ta rike hanunshi wai karyaje ko ina scorpion zata kamata, bayanda zaiyi yajuya baya, ta cire kayan ta mika mishi rikemin, hannu yamika mata ya karba yaga doguwan riganta ne da pant abunma kunya yabashi haka ya tsaya hartagama wanka, sanan tace towel, da baya da baya yaje wajen yamika mata towel din…tambaya yayi kin gama??tace eh sanan yajuyo kallo daya yamata yadauke kai dan yasan inya cigaba da kallonta za’a samu matsala… yace jeki zauna bari na wanke miki kaya,ina zuwa.tace uh uh nidai zan jiraka anan. bai kara cemata komiba wanke kayan data ciren yayi tass sanan suka fito yadauko mata wasu kayan juyawa yakarayi sanan tasa kayan. hanunta yaja suka fito bayan dakinsu ya shanya kayan nata daya wanke mata suka dawo daki ya zaunar da ita kan gado yace yanzu saura salla alwala yamata sanan yakoya mata yanda ake sallan tai asuba kafin yahada mata tea tasha takara bacci …..
Sai wuraren 11 su Abba amma anty amarya tana gida sunako zuwa doc yabasu sallama suka tattara komi akakai cikin mota sai kuma tunanin fito da humairat suka fara…islam yace abarshi da aikin yanzu dai bari yatasota yana zuwa yatasheta ahanakali tabude idonta ta kalleshi da sauri ya kauda kai tashi mutafi, mikewa tayi yarike mata hannu suka fito amma suna fitowa bakin kofa ta hango nurse mace da gudu takoma daki tana ihu scorpion islam dayaga zata bata mishi lokacin daukanta yayi chak tana ihu tana kururuwa bai direta ko inaba sai cikin mota…khalil dai kishi ne ke cinshi
Maman shakur
[12/10 7:50 AM] Aishat muh’d: [12/10 7:20 AM] Aishat muh’d: 93RAYUWAR HUMAIRAT
Suna shiga gidan anty amarya tafito nan humairat tafara ihu tana scorpion uncle khalil save me,islam ya daka mata tsawa yace wanan ba scorpion bace kidena cemata scorpion she is ur momy,humairat tai rau rau da ido tace are u sure uncle khalil???yace mata yes ….takara cewa are u sure she will not hurt me??yace mata eh mana muje ma kigani tafiya take jikinta na rawa sosai yakaita har gaban anty amarya wanda kuka take sosai tsayawa tayi ta kura mata ido sai kuma taji bataji dadin yanda take kuka ba hanun ta dago yana rawa sosai jikinta ma rawa yake tasa akan fuskan anty amarya tace stop crying momy sanan ta rumgume anty amarya kowa awurin yay hamdala…anty amarya taja hanunta takaita daki tai mata wanka ta shiryata saida tai bacci sanan tafito…
Tasamu su Abba afalo tace alh bangane maisa take kiran islam khalil ba, alh yace nima abin naban mamaki amma nafi kawo cewa saboda khalil shine wanda yaje visiting dinta karshe yakuma bata good news cewa zata bar gidan yarin saisa sunanshi ya tsaya a kwakwalwanta..Anty tace hala…….shidai khalil bakin ciki yakeji inama yana dakin tafarka da yanzu dashi zata dinga yarda……
Abba yace in Allah yakaimu gobe islam zamu wuce da humairat kano, islam yay zuru zuru Abba nima zan biku ai,. yatashi yafita dan zaije yadau leave a office …
Da safe bayan anyi breakfast aka fara tunanin ya za’ayi a tafi da humairat har airport gashi mata a ko ina…islam yace Abba zan iya dauko helicopter din air force natukamu har kano……ahaka sukabar maganan…….
Sun isa kano Lpy ba’a bari humairat taga su Abu ba danko ihu zata farayi tana kiran scorpion……har daki Abba yaje yasamu dad yace usama yarka na gidanan kazo kadubata batada lpy…yace yaya ina ganin girmankafa, kadenamin maganan wanan yarinyar, tsaki yayi yawuce yaja motarshi sai prison inda kausar take yaje sukasha fira yafadanata humairat tadawo kano wai batada lpy. gani yayi kausar ta mike tace mishi sai anjima bata jira cewanshiba takoma ciki….
Maman shakur
[12/10 7:48 AM] Aishat muh’d: 94RAYUWAR HUMAIRAT
Tana shiga cell dinta tafara tunanin ya za’ayi tabar prison dinan yau,kaman mahaukaciya haka tadawo dis is d best time nakasheta, batada lpy dole nakasheki humairat…..tana cikin tunanin taga wata guard dinsu mai suna merry, tadan manyanta dama tanashan giya kowa yasani a wurin amma suna mamaki da gwamnati bata koretaba…kausar taga matan na layi ga dukkan alamu giyan tasha kausar tadinga binta abaya har matan tashiga dakinta kausarma tabita ciki, duk merry bata lura ana binta abaya ba,akwai wata jijiya a wuya da inhar wani ya dakeka akanta saika sume, kausar ta daga hanunta ta kaimata dukan akan jijiyan na wuyanta, take matan tafadi a wurin sumammiya….kausar tacire kayan guard din jikin matan tasa, tadau facing cap din tasa, tadau tabarau tasa, sanan ta makala id card din matan a gaban aljihun ta,sanan tadau bindigan matan tasa a wandonta,..taja matan takaita bayi ta kulle da makulli, sanan tafito direct gate tawuce ta nuna id card dinta, akabarta tafita batare da anyi wani tunani ba…gudu tafara sosai tazo saitin wani gida taga sunyi wanki kayan sun bushe daukan riga da zani da hijab tayi takoma wani lungu ta chanza kayan sanan, tahau gudu baji ba gani sada tai nisa da prison din tabar anguwan kwata kwata sanan ta tsaya tasai ruwa da egg roll …taga wani gida da ba’a gama ginawaba ta shiga ta zauna taci, sanan kwanta tana hutawa……. Bataga kowa yashigo gidanba tai murna tace xan iya kwana anan ..gobe naje nakashe humairat.
Washegari Abu tashigo yima anty amarya sallama babelo ta haihu wai zataje yimata wanka anty amarya tai mata fatan alheri tabata kyauta akaima jariri……anty dataga Abu batanan babu wata mace gidan sai ita, dama twins suna gidan grandma dinsu……saisa tace bari tafito da humairat tasha rana…takoma daki tafito da ita, garden ta kaita,aiko humairat sai murna take tana dariya taga lilo tajuyo tace momy nahau wanan anty amarya da murna ya kasheta humairat na walwala yau,tace eh hau humairat. aiko tahau tana dariya yanda abun ke wullata sama da kasa,juyowa tayi ta kalli anty amarya tace momy dan daukomin ice cream dina wanda uncle khalil yasiyomin jiya, anty amarya tace to bari naje na dauko miki ki jirani anan fa tace to…..
Ashe duk abun nan a idon kausar tun asuba ta shigo gidan a idonta su Abba suka tafi masallaci tare da mai gadi. shine ta shigo gidan ta labe abayan tankin gidan,har lokacin da Abu tatafi duk kausar tana ganinsu,lokacin da aka fito da humairat ne tai hamdala tace anty amarya kin ragemin wahala…..fitowa tayi daga maboyarta ahanakali take tafiya har takai inda humairat ke lilo,bindigarta taciro daga jikinta tai pointing kan humairat, wanda dama tabata baya tana lilo so bataga kausar ba….
Maman shakur
[12/10 1:26 PM] Aishat muh’d: [12/10 12:41 PM] Aishat muh’d: 95RAYUWAR HUMAIRAT
Shigowan khalil kenan gidan. harzai wuce ya hango ruwa nazuba a garden pipe din da ake watering flowers dindasu kaman baba mai gadi yamantane bai kasheba, ruwa sai zuba yake yace bari yaje yakashe, yana zuwa yakashe dogowan dazaiyi yahango wata mata wanda baisan ko wacece ba tayi pulling trigger zata harbi humairat…..wani fanfalakin gudu yayi ya wani doka uban tsalle ya tunkuda humairat akasa tass bullet din sai akafadanshi yafadi wajen warwas….
Firgigit islam ya farka daga baccin dayake shidai yasan ko amafarki yanajin karan bindiga yasani,mai yakawo bindiga harda harbi a gidanan??dama dagashi sai anty amarya ke gida Abba da dad sunfita….sakkowa yayi baima tsaya sa kayaba dagashi sai singlet da short yadau pistol(karamar bindiga)yafito….
Anty amaryama tanajin karan bindiga ice cream din humairat data rike a hannu tayar,tafito a dari tana fitowa tsakar gida taga Islam ma yafito tabude baki zatai magana yasa hannu akan lebenshi alamun tai shiru yana tafiya ahankali tana biye dashi abaya…..
Humairat jitayi tafadi ga wani wawan karan dataji yasa tasaki wani ihu tamike tajuyo. kausar tagani batai ihuba amma gani take kaman tasan fuskan a wani wuri, kantane yafara jujjuyawa gabaki daya taga duniyar na juyawa a idonta,chan idonta yafara baki bata ganin komi kawai tafadi kusada khalil asume….kausar takara pulling trigger tace just wot i needed tayi saitin humairat zata harbeta…….islam wanda yariga sun iso wurin amma suna tafiya ahankali, shammaceta yayi yasa hanunshi yadaki guiwan hanunta bindigar tafadi kasa,yayinda hanunta yace kasss dagajin karan kasan hanun ya karye. ya tsugunna yadau bingigar yafara dukanta tana ihu, yayin da anty amarya ta rude tama rasa abinyi kan humairat da khalil zatayi koko zataje takira alh ne?? Islam yace anty go and call d police kuma kikira su Abba…yacigaba da dukan kausar..dukan mugunta yake mata irin nasu na sojoji gabaki dayan joints dinta yake duka batada karfi koda na tafiyane sai ihu take tana yayaha kuri….gani yayi humairat na daga hannu alamun tatashi yasa yasaki kausar yaje kan humairat.. kausar na ganin haka da rarrafe tabar gidan tana fita waje taga zata iya mikewa tamike tanamai ihu tarike hanunta daya karye…..tafiya take da sauri taji ance za’a kira police yazatayi??ina zan boye??wani gidan mai tahango na total agabanta, daga gani irin abandon gidan mai dinanne wanda andena aiki dashi andena siyar da mai karasawa tayi..tana zuwa tashiga underground building din (Masu karatu nasan akwai wayanda basusan underground building ba shi ginine akeyi a kasan kasa…yawancin gidan mai nadasu saboda tawurin ake zuba mai din da ake siyarwa)
Tana shiga taga kujera tazauna tana sauke ajiyan zuciya..yanzu dai ranane zan bari sai dare zan fito daga wurinan natafi asibiti a gyaramin hanun dan dan iskan yaron nan ya karyamin.wlh kuma ban fasaba saina dawo na kashe humairat ta dandani azaban da uwarta tasani…takaici da bakin ciki yasa taji tanason ta zuki taba, dama tantiriya tariga takoya mata shan taba. tako ciro tabanta da store light ..ita a ganinta tunda andena siyar da mai ai babu wani petrol, so zata iya shan sigarinta aiko tana kunna store light din ta sa wutan ataban…jitayi bomm kakeji wurin yakama da wuta kausar tasaki taban akan wajen batare data kasheba aikuwa wuri yakama da wuta da gudu tayi hanyar fita, wani ikon Allah saitaga wutan hanyar fitama tafi ta cikin wurin yawa, kuka tafara tana Allah na tuba, Allah kayafemin abunda nayima ,atagafurullah, Allah kaceceni, nahakura bazanma humairat komiba, Allah karkasa wutanan yakonani,wlh Allah natuba abunda take fada kenan. amma inaa is too late 4 kausar dama fadin annabine Allah na karban tuban bawansa matukar bai kai gargaraba!!
Kausar ihu take tana help help wasu dasukazo wucewa anjita aka leka akaga wuta ne yakama aka kira birget amma koda sukazo suna zuba ruwa kaman kara ruru wutan suke wutan ci take kaman aci balbal……INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN wat a painful and miserable ending 4 kausar INDEED!!!
Maman shakur
[12/10 1:26 PM] Aishat muh’d: 96RAYUWAR HUMAIRAT
Islam ya rike hanun humairat yana wake-up wake-up, daidai lokacin Abba da dad sun shigo dama basuyi nisaaba sunje duba wani plot of land ne.. anty amarya kuma takira police amma basu riga sun isoba, anty amarya ne tafito daga daki tana islam lamban Abba ka baya zuwa saita gansu sun shigo, da sauri Abba yakarasa yana lpy na ganki arude tace muje garden suka bita abaya….har lokacin humairat bata farkaba amma hanunta ta daga tana let go off me scorpion karkimin komi stop stop, Abba yace bamuga tazamaba mukaisu asibiti juyoya yayi yacema dad baban humairat yatayashi sudau khalil amma saiyaga shima ya sulale akasa sumamme….duk suka kara rudewa wai meke faruwane yau?? Abba ya kalli islam kai tashi jekasa kaya mukaisu asibiti khalil na numfashi bai mutuba nan da nan anty amarya ta share hawayen ta tana alh da gaske??yace eh, islam yafito suka fara daukan khalil suka sashi amotan Abba,sanan sukadau humairat akasa a motan anty, sai kuma baban humairat dad akasa a motan islam,..Abba ya kalli anty amarya zaki iya driving kuwa?? tace eh kafinma su shiga mota police suka iso nan suka fadama inspecta ai kausar dinma tagudu.. yace musu tun jiya suka samu waya tagudu daga prison sunata nemanta, nan dai inspecta yashiga motan da humairat ke ciki yay driving gabaki daya suka rankaya sai hospital aminu kano…..
Direct theater aka wuce da khalil dan cire bullet din yayinda sauran likitoci suka dukafa kan dad da humairat…
Islam dai jikinshi duk yay sanyi
Ba a dadeba dad ya farfado yace yanason ganin yayanshi,nurse tafito tafada mishi aiko Abba anty amarya da islam suka shiga…yace yaya ina humairat???kowa a dakin yay mamaki dan ansan bayama tambayan humairat,yace wlh wani mugun mafarki nayi yanzunan wai inata wulakanta humairat, harda duka amma islam duk saiya taimaketa ya kwaceta a hannuna inatake humairat din yaya ban ganku tareba???Abba yay shiru yakalli anty amarya anty amarya ta kalleshi sukai murmushi..Abba yace alhamdulilah kanina yadawo hayyacinshi.. nan yafadama dad duk abunda yadingayi dad kuka yayi wiwi yanzu shine yay ma yarshi haka??y??duk saboda kausar takenan yadinga tsinema kausar yana Allah ya isa….inspecta ne ya shigo dakin yace alh dole kubiyoni yanzu munaso kuyi identifying wani body ….Abba yace anty amarya ta zauna,Abba islam da dad suka tafi har gidanmai…..dayake ankashe wutan wani abu suka gani kaman ball an rufe da farin kyalle inspecta ya bude musu salati sukayi dukansu kausar ne kanta kadai , Abba yace maiya faru???wanan ai kan kausar ne??nan inspecta yace wuta ne yakama ba’asan garinya ba, bayan wutan yamutu akaga wanan kan amma jikin yakone kurmus.. inspecta yace abunda yaban mamaki shine jikinta ya kone kurmus amma banda kanta…dad yay magana yace hakika wanan darasine amma kadai gamasu imani da tunani….matan nan taraba uba da yarabshi biyu takashemin da kabir,ta rabani da marainiya humairat,tarabani da yayana da kowa,takashemin matata ta farko……ya share hawayen yace Allah nagodema daka kubutar dani daga shairin kausar..yakara share hawayen idonshi yace kausar bazan taba yafemiki ba, kuma wlh bazan sallaci gawankiba, yajuya yatafi Abba na kiranshi amma ko juyowa baiyiba…
Maman shakur
[13/10 3:06 PM] Aishat muh’d: [13/10 8:59 AM] Aishat muh’d: 97RAYUWAR HUMAIRAT
Bayan fitansu Abba ba dadewa humairat ta farka lokacin anty amarya na kusada ita amma tadan kishingida tana bacci…humairat ta kalli anty amarya ta kalli dakin datake ciki ahanakali tace mamanan,da sauri anty amarya tabude ido, da sauri ta matso kusa da humairat din tace humairat kin tashi??ta girgiza kai alamun eh, anty ta rumgumeta sai kuma humairat tahau kuka sosai, anty amarya ta dagota humairat menene??mesa kike kuka??humairat tana shesheka tace mamana maiya kawoni nan??nidai nasan ina prison scorpion ta kaini dakinta…anty amarya tace yauwa me scorpion dinan tamikii??nan humairat tana kuka tafadanma anty amarya komi anty amarya tace wlh dole sai anbimiki hakkin ki abunda scorpion tamiki…nan dai suka cigaba da fira humairat ta tambayi anty amarya kowa, amma banda islam.anty amarya duk tana lura da ita…anty amarya ta kaita bayi tai wanka sanan tahada mata abinci taci. Lokacin doc ya shigo yacema anty d operation was successful yama tashi zaku iya zuwa kuganshi…humairat tace mamana waye akaima operation???anty amarya tace khalil ne,humairat ta rude tafara kuka maiya sameshi?? anty amarya tafadi mata komi…humairat tamike suka tafi dakinshi…yana kwance yaga humairat ta shigo baice mata komiba sai kallonta dayakeyi…anty amarya tafara magana ya jikinka??ahanakali yace da sauki..tace bari nahadoma tea,ya kurama humairat ido, jawo kujera tayi ta zauna abakin gadon takama kunenta tai rau rau da ido am sorry uncle khalil, saboda ni aka harbeka da yanzu nine za’a harba,mamaki ne yagama dashi humairat taji sauki ne?kome??murmushi tayi tace uncle khalil ai naji sauki…lokacin da anty takawo tea din humairat ta karba da sauri mamana bari na bashi, har cikin ran anty batasoba amma dai ta kyaleta humairat ta dago gadon sama yanda zaiji dadin shan tea din….kadan kadan take bashi tunda yake baitabajin tea mai dadi da gardi irin wanan ba, kodan humairat ce kebashi oho, yanasha yana kallonta itako sai murmushi takemai…..tana cikin bashi su Abba suka shigo da sallamansu, islam mamaki ne da kishi sukai mishi katutu a wuya, humairat na ganin Abba ta ruga da gudu ta rumgumeshi tahau kukan shagwaba da kyar ya lallasheta tai shiru, tare da cewa yanzu komi yawuce insha Allah,ko kallon islam batayiba tajuya zata koma tacigaba dabama khalil tea ne, anty amarya ta daka mata tsawa bakiga yayanki bane?? atsorce tace ina wuni yaya, bata jira amsan shiba takoma tacigaba da bama khalil tea din yanasha ahanakali.. islam gani yayi bazai iya jura ganinsu hakaba yajuya yabar dakin….
Maman shakur
[13/10 9:48 AM] Aishat muh’d: 98RAYUWAR HUMAIRAT
Sai wurin karfe 8 aka sallami humairat, kuka tadingayi tana cema Abba ita abarta zata kula da khalil,tunda sanadiyyantane aka harbeshi,Abba yace kintaba ganin inda mace takula da namiji??anty amarya tace humairat zan zanekifa wuce mutafi gida baga Abokinshi sadiq yazoba,zai kwana anan, haka suka jata suka shiga mota, Abba da anty amarya agaba,sai ita da islam abaya ko kallon islam bataiba tanata kukanta ahanakali, shikuma babu abunda ya tsana aduniya kaman kukan humairat jiyake kaman ya janyota jikinshi ya rungumeta,…tana ganin sunyi hanyar gidansu na kano tafara ihu sosai tsabagen rudewa yasa tama kankame islam ta shige jikinshi yaya plz karku kaini gidanan, anty da dady zasu dinga dukana plz yaya saida taba kowa tausayi amotan,…islam ko wani nishadi da kwanciyan hankali yaji lokacin dayaji humairat a jikinshi shafata yafarayi princess is ok karki tsorata su dad bazasu kara dukankiba kinjiko, dukda haka bata daina kukan ba kuma tana jikinshi ta kankameshi…..suna shiga suka parking da kyar tafito takara rike islam. dago kanta dazatayi taga dad na zuwa wani ihu tayi ta shige jikin islam tana yaya dad zai daken….i bata karasa maganan ba tasume…dad ko kuka yafara yanzu yarinyar daya haifa ne haka takejin tsoronshi duk saboda shairin kausar….hawaye ya cika idonshi tap…islam ya dauketa chak yakaita dakinta cikin part din anty amarya, ya kwantar da ita kan gado sanan aka shafa mata ruwa afuska, tana bude ido taga dad kusa da ita takara ihu tarufe idonta gam tana yaya plz zoka rikeni,wlh kacema dad na dena fitsarin kwance karyasani akan kada, islam zama yazo yayi kusa da ita yace humairat open ur eye ahanakali tabude idon look at me takalleshi…dad dinki ne bazai miki komiba ki tsaya ki saurari abunda zaice, zamu tsaya abakin kofa kinji rikeshi tayi tana girgixa kai uhm uhm nidai a’a karka fita…dad da hawaye yasoma zuba daga idonshi yafara magana humairat kiyafemin dan Allah abunda namiki nasan nai kuskure babba amma kiyafemin yata ,humairat jikinta yay sanyi ahanakali murya narawa dan tsoron dad yariga ya shigeta tace dad ni wlh nayafema tuntuni rugumeta yayi yana Nagode humairat Allah yamiki albarka.. itadai tarike hanun islam gam dan haryanzu gani take kaman zai iya dukanta.. kowa adakin saida dad yabashi tausayi…dad yace namiki alkwari zan baki kulawan da duk uba yakema yarshi kinji humairat ta??ta girgiza kai alamun eh…sanan yace kiyi barci kinji yatashi suka fita tare dasu Abba… Akabar daga islam sai humairat,tana ganin dad yafita ta fincike hanunta daga hannu islam tana turo baki,mamaki da dariya tabashi yarinyar da dazunan tagama runrungumeshi dayike taga abun tsoro amma yanzu jibeta…magana tamai nidai yaya kafita bacci zanyi tana murgudamai baki,…matsowa yayi dap da ita, da sauri ta koma baya ya daure fuska mekikace???nan da nan ta birkice to ai ai dama ni bacci nakeji abunda nace kenan,…murmushi yayi yakara daure fuska yace duk randa nakara kamaki kinje kusada khalil ko kika bashi wani abu abaki saina zaneki ranan,,,,bata cemai komiba, tafara kokarin cire rigan jikinta, dan tasaba dan zaman datai a prison haka zaka cire riga gaban kowa….islam kuma yaki fita kaman gunki…juyamai baya tayi tacire rigan yarage daga ita sai short iya guiwa, baya ganin gabanta sai baya tafiya tayi saida ta shiga bayi sanan ta leko da kanta ta jefamai doguwan rigan data cire tareda cewa look look taimai gwalo.. tajuwa tarufe kofan bayin tana dariya, shima dariya abun yabashi ya manna rigan a kirjinshi sanan yamike da kyar dan tagama dagulamai lissafi yawuce dakinshi…..
Maman shakur
[13/10 10:20 AM] Aishat muh’d: 99RAYUWAR HUMAIRAT
Bayan tafito daga wanka ta tsinci kanta tana mai tunanin yaya islam komaiyasa oho??maisa duk abunda yamin nakasa tsananshi??wata zuciyan tace saboda shi jininkine,dan uwanki,kuma yayanki,….da tunanin islam tai bacci….bangaren islam ma hakane bai iyayin bacciba saida ya rungume doguwan rigan data jefamai yana tuna yanda ta turo harshe tanamai gwalo….bangaren khalil shima da tunanin humairat ya kwana yanamai tuna yanda tai rau rau da ido ta rike kunne tacemai sorry arayuwanshi yana bala’in son mace mai shagwaba…….bangaren anty ita kwata kwata bata runtsaba duk ta lura da take taken yaran,suna neman su kawo wani al’amari da itane zasusa a tsakiya,inhar tunanin datake na cewa kaninta khalil nason humairat yazatayi???inhar tunanin datake humairat nason islam haryanzu amma dai itane bata ganeba yazatayi???inhar tunanin datake nacewa islam nason humairat haryanzu kuma zaice zai komar da ita yazatayi???banason nai sonkai,banason kanina yaga kaman nafison dan mijina kanshi,banason humairat tai tunanin ban riketa amatsayin yata dagaskiyaba,banason islam yamin kallon mai sonkai inhar na yarda humairat ta auri khalil……dahaka barci ya kwasheta..
Washegari humairat ta tashi tai wanka tasa wani riga da sket na atampha kore yay mata kyau sosai gashi sun matseta tafiti falo ta zauna gani tayi dad yashigo da sallamanshi a tsorace tamike jikinta na rawa tace dad ina kwana yace humairat harkin tashi muje dakin Abba kowa nachan muna breakfast hanunta yaja suka shiga falon tagaida kowa banda..islam daketa kallonta kaman ya cinyeta,dad da kanshi yadinga ba humairat abinci abaki tanaci Allah sarki uba da ya kowa murna yake babu wanda yataba tunanin rana irin tayau zatazo,bayan angamaci humairat tafara kwashe kayan tana kaiwa kitchen shima islam ya kwashi sauran ya rutsata a kitchen batacemai komiba tazo zata fita yaja hanunta,tadaure fuska mai haka??yace wanene look look??tace toni ai badakai nakeba…matseta yay a bango yaushe za’a maida aurenmu.??..wani kallo tai mishi tace ni bazan kara aurekaba yaya. banasonka wanda nakeso Zan jira ya warke muyi au….re,wani wawan mari yamata dayasa tafashe da kuka sosai, i’i’na dinshi yafara yace wlh duk randa kika karamin maganan wani namiji saina bata miki rai yawuce yatafi yabarta awurin tana kuka rike da kuncinta….
Maman shakur
[13/10 3:06 PM] Aishat muh’d: [13/10 11:03 AM] Aishat muh’d: 100RAYUWAR HUMAIRAT
Tundaga ranan da islam ya mari humairat bata karabari sun haduba,koya aika akirata bata zuwa,dazaran taji yashigo dakin anty amarya zata tashi dasauri ta shiga dakinta ta kulle,islam duk ya susuce koba komi ganin fuskan humairat makes him happy,but kullum tana zuwa duba khalil,yay confessing mata yana sonta,batai watawataba ta karbi soyayyanshi ,.soyayya suke mai tsafta babu wanan soyayyan shan mintin……zaman da anty amarya tai da humairat ta lura humairat batasan komi game da aureba,taje tasamu Abba da maganan….da daddare Abba yakira islam yake tambayan shi wani abu na aurataiyya yataba shiga tsakaninka da humairat???akunyace yace a’a Abba….Abba yace mishi ai shikenan yarinya na samun miji wlh aure zan mata, indai ba ita tace zata koma gidan kaba, tashi kabani wuri mutumin banza kawai, islam yatashi jikinshi a asanyaye yana addu’a insha Allah batada miji saishi…..adaren ya tattara inashi inashi dan hutun daya dauka yakare dole yakoma bakin aikinshi…..daya gama hada kaya lokacin karfe 9 yace bari yaje yafadi ma anty gobe zai koma..daidai bakin kofanta yaji muryar humairat na cewa mamana wlh yanzu mutum daya nakeson nagani…anty tace wacece???humairat tace anty sunanta aishat muhammad,a prison muka hadu tana sona sosai tana kula dani,lokacin da scorpion ta fasamin kai bangama fita hayyacinaba naga aishat ta shigo dakin tana kuka ta rufemin jikina da towel…sauke ajiyan zuciya tayi tace anty wlh kullum addu’a na Allah yasa tafito innuna mata so,in gode mata,inmata karamci sanan inhar zan kara ganinta tafito daga wajenan, wlh mamana zanso nahadata aure da dady na, takarasa maganan tana kuka anty amarya tace ki dunga addu’a Allah ya kaddara saduwarku da kyar tai shiru….shiko islam juyawa yayi yakoma daki dole yafito da aishat Muhammad daga prison inhar hakan zaisa humairat farin ciki kuma wlh scorpion saitasan ta wahalar mai da mata….washe gari da sassafe yayma kowa sallama dukson dayayi yaga humairat abun baiyuwu ba…
Yau kimanin wata 3 da tafiyan islam kenan,soyayya tai karfi tsakanin khalil da humairat dan kowa yasani a gidan…Abba ko tuni yacema khalil yaturo magabatanshi. kaman ansashi a aljanna yaturo iyayensu akasa biki wata 1 kacal… zuciyar mutane biyune basuson wanan auren..anty amarya dan harga Allah tasan islam nason humairat, sanan dad din humairat shiko bayason auren ne dan aganinshi inda badan islam ba dahar yanzu humairat na cikin rayuwar kunci, kullum tanashan dukanshi dana matarshi kausar….yasan cewa Khalil shima yataimaketa tabbas, amma islam dabanne lokacin dakowa kejin kyamanta baijiba,ya tausaya mata,yabata abinshi,ya aureta,yasata makaranta,yay mata gatan uwa da uba,sakin nan daya mata kaddarane wanda Allah yariga yarubuta tuntuni zai faru,dad yace ina! dole nasan abinyi, yatace,nasan duk randa islam zai dawo yaji ansama humairat rana bazai tabajin dadiba….islam mai son yatane akullum akuma koda yaushe acikin kowani hali dakowani yanayi…..
Musamman yau anty amarya ta shirya taje gidansu dan magana da khalil tako sameshi yananan zaune adaki….gaisheta yayi a girmame, tace khalil inason magana dakai,yace inajinki anty…tace khalil maisa kakeson shiga tsakanin soyayyan da’aka gina tutuni??tun humairat batasan wacece itaba,tun humairat batasan menene aureba??khalil nasanka yarone mai tausayi,kanada amana,gajinakai,kana ganin duk randa islam zai dawo yaji ansa muku rana zaiji dadi???shiru yayi saida yabari tagama magana yadago da jajayen idonshi yace anty farin cikin islam kike gani bana dan uwankiba,islam yaron mijinkine nikuma kaninki saisa kikafi sonshi kanniko??anty inason humairat sosai yakikeso nayi?? yana maganan hawaye nazuba daga idonshi…mikewa anty tayi tace kayahakuri khalil kadena kuka,ina sonka ,inason islam kuma inason humairat dukanku nawane Allah baku zaman lapiya ta tattara tabar gidan…tabar khalil da tunani…
Maman shakur
[13/10 11:23 AM] Aishat muh’d: 101RAYUWAR HUMAIRAT
Yau yarage bikin humairat saura sati biyu…anty ajiye komi tayi agefe tana gyran amarya abunta..ta lura humairat tama manta da batun wani islam…itadai anty tasan daurewa kawai takeyi amma harga Allah batason auren humairat da khalil, dukdako tasan khalil na bala’in son humairat amma ita aganinta farincikin humairat natare da islam……
Karfe 9 nadare islam ya shigo garin tare da babban bakuwa,masu karatu kunason kusan wacece bakuwar???anki anfada din:roll: ….koda suka shiga dakin anty amarya, da yayma anty amarya bayanin bakuwar tai matukar murna anty amarya ta wadatata da abubuwan tande baki….bakuwar ta tambaya ina humairat? anty amarya tace tana barci amma bari na tasota bakuwar tace mamanmu kibarta gobe dasafe taganni as surprise…….islam yawuce dakinshi dan yay wanka, bayan yay wanka yaje yagaida Abba anan ne yasamu zancen dayafi dagamai hankali kan komi aduniyar nan, yace Abba yanzu humairat aure zatayi???Abba yace da kai zata jira bakai kasaketaba,yace islam nahoreka da yawan fushi,yanke hukunci cikin fushi abune wanda bai da kyau, yanasa nadama daga baya sosai..gashinan wa gari tawaya kai…tashi kabarmin daki, mikewa yayi haryana kume kai da bango.. Abba yace ka kashe kankama inkaga dama,auredai ba fashi…inka sake auren wata matan ka saketa itama inkai fushi, sha sha sha kawai….
Ranan islam baiyi bacci ba zuciyarshi kuna takemai kaman garwashi dayaga ba sarki sai Allah yaje yayo alwala yadinga salla sai bayan sallan asuba bacci yay gaba dashi…
Maman shakur
[13/10 11:41 AM] Aishat muh’d: 102 RAYUWAR HUMAIRAT
Da safe bayan humairat tabude ido taga wata kakkyawan fuska fara tana mata murmushi,mikewa tsaye tayi ta share idonta gani take kaman a mafarki, falo taje tasami anty amarya tace mamana wacece a dakina kaman aishat…anty amarya tace tunda ita kika gani ai ita dince ko….komawa tayi dakin taga tanamata murmushi, sai chan tabude mata hannu tafada kirjinta dagudu suka rumgume juna suna kuka…aishat ce tafara dagowa tace beauty i missed u alot,bayan ankaiki asibiti nadena walwala kullum tunanin ki nake…sai 3 month ago yayanki islam yazo yanemi ganina muka gaisa yaban labarin ki..sanan yasa nafada mishi labarina abunda yakaini prison yasamomin lawyer aka fara fafata case harsaida yacironi jiya muka zo kano…ta share hawayen idonta tace humairat yayanki nada kirki sosai wlh…humairat har cikin ranta taji dadi abunda islam yayi amma mamaki take ya akayi yAsan tanason aishat har yacirota daga prison….tashi tayi tai wanka suka tafi dakin Abba yin breakfast….kowa murna yake anata ma aishat sannu da zuwa dad ne yace wai ina islam???Abba yace oho…dad ya mike yaje dakin islam ya tarar dashi zaune yadafe kanshi idanunshi sunyi jaa sosai dad yakarasa ciki da sauri islam maiya sameka??hawaye ne ya gangaro daga idonshi sharewa yayi yamike yace bakomi,dad yakamoshi nasan kaji komi kan zancen auren humairat kayaha kuri islam….kalleni nan badai nine baban humairat ba..to amatsayina na babbanta nabaka auren humairat,amma kai shiru ni inada plan karka fadanma kowa jekayi wanka muna jiranka yace to…….
Shigowa yayi dakin Abba da sallama aka amsa yagaida kowa aishat tagaidashi amutunce,humairat tace ina kwana yaya dago kai yayi ya kalleta gani yayi takara kyau takara fresh da cika…ciki ciki ya amsa mata lpy… Saida suka gamacin abinci Abba yay gyaran murya yace aishat munaso kibamu labarinki….
Maman shakur
[13/10 10:56 PM] Aishat muh’d: [13/10 11:59 AM] Aishat muh’d: 103RAYUWAR HUMAIRAT
Aishat tafara tace,nidai sunanan aishat Muhammad am 25 years old..iyayenmu ba hausawa bane mu nufawa ne, mubiyu suka haifa nida kanwata mai suna habiba yanzu tana 17 years….muntaso tare da iyayenmu basuda kudi talakawanemu sosai, bamuda kudi.. tafiya takama iyayenmu suka barmu suka tafi.. bayan sati daya aka kawomana labari cewa iyayenmu sun rasu.. …nashiga tashin hankali saboda lokacin habiba batada wayo.. yanzu ina zamu?? bamusan kowaba.. Bamusan yan uwan iyayenmuba …kuma gidan damuke haya suka koremu..wani makwabcinmune yace zai iya taimakon mu yakaimu gidan marayu shima bazai iya rikemuba…haka aka kaimu munajin dadin rayuwa awajen saida mukai shekara 5 sanan nafara lura kullum mutane nabata, daya daya abun yadamen,daga karshe nagano ai matar dake kula da gidan marayun saida yara takeyi batare da kowa yasaniba,batare da gwamnati tasaniba, hankalina yatashi banda wayo sosai lokacin nafadama wata mata a gidan marayun ashe kawar hajiyarce. aikuwa tunda suka lura nasan sirrinsu shine suka lakamin shairin wai nabatar da yara 10.. gwamnati takamani akakaini gidan yari tundaga lokacin ban kara ganin habiba ba haryau..hala yanzu itama sun saidata….humairat ta rumgumeta tana tayata kuka…Abba yay gyran murya yace tunda yanzu angano gaskiya ankama hajiyar da kawar tata zamuje gidan marayun muduba inhar habiba na nan zamuyi adopting dinta, aikuwa aishat tadinga godiya….humairat tace Abba inada magana, Abba yace munajinki dawowa tayi kusa da dad tace dad dan Allah inaso ka auri anty Aishat,kunya ne yakama anty Aishat tafita da sauri tana boye fuskan,humairat tabita tana anty kidawo…bayan fitansu Abba yace usama bazan kyaleka kaki aureba,ga aishat nan tanada hankali mun yarda da ita, ta taimakama yarka agidan yari so ka aureta…anty amarya tace nima inasonka da ita,islam yace nima inasonka da ita dad…yay murmushi yace yaya wlh tunda na ganta naji tamin zan aureta islam yay hamdala yace amma gaskiya dad baza’a dauki lokaci ba nanda jumma’a inhar ta yarda za’ayi bikin….
Maman shakur
[13/10 12:25 PM] Aishat muh’d: 104RAYUWAR HUMAIRAT
Humairat tabita daki tafashe mata da kuka yanzu anty Aishat bakison dady na??bakison ki aureshi ki kula dashi???wlh koki yarda konaita miki kuka anan..tako fara kuka sosai aishat tace beauty rigima,beauty shagwaba,tom naji na yarda zan auri dad dinki.humairat tayi wani ihu ta rumgumeta tana thank u anty…tafita da gudu islam tafara gani ta rumgumeshi tace yaya tayarda…tasakeshi takara arcewa da gudu ta rumgume anty amarya tace mamana ta yarda..tawuce dagudu ta rumgume Abba tace Abba ta yarda sanan taje ta dane jikin dad tace dad ta yarda dad ma sai murmushi yake shiko yaya tunda ta rumgume shi tadagamai hankali…..khalil yazo humairat tabashi labarin aishat,aishat tafito suka gaisa da khalil…bata cema humairat komiba amma dan zaman datai agidan talura islam nason humairat to maiya faru??maisa aka hana humairat islam akaba khalil?? bari humairat ta shigo akwai magana….karfe 12 Abba yace oya kowa ya shirya azo atafi minna niger state dauko habiba……
Humairat tura anty Aishat tayi motar dad ..sanan Abba da anty amarya a mota daya sai humairat , twins,khalil da islam amota daya..yayinda islam ke driving khalil agefenshi,humairat da twins kuma abaya…motan su dad ne agaba har garin minna….
Sun isa gidan marayun cikin ikon Allah sukaga habiba zaune gindin wata bishiya…Aishat takarasa wurin tace habiba!!dago dara daran idonta tayi taga yayarta data dade tana kuka kanta…zuwa tayi da gudu suka rumgume juna suna kuka….khalil wani zuface ta keto mishi wanan ba yarinyar daya taba gani bane lokacin dayataba rako dad dinsu garin nan …yaganta tana kuka wai ankai yayarta gidan yari.. yakaita yasai mata abinci yabata naira dubu 1…tundaga lokacin yake tunaninta….yana yawan dawowa minna yazo inda yataba ganinta kozai kara ganinta amma bai kara ganin taba ………aishat kaita tayi tagaida su Abba amma tana kaiwa kan khalil tace khalil yace naam habiba…kowa yazaro ido:oops::oops: kunsan junane???tace anty kin tuna randa aka tafi dake inata kuka yaganni yasaimin abinci yabani kudi..saisa na sanshi daga nan suka dunguma office sukai adopting dinta aka kama hanyar dawowa gida…tuni habiba tazama kawar humairat yayinda aishat da dad sun daidaita kansu..Islam da khalil ko kowannensu da abunda ke ranshi….
Maman shakur

Previous page 1 2 3 4 5 6Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button