Rayuwar Mace

RAYUWAR MACE 6

     RM
          6

****Zuwan angwayen ya saka aka shiga gabatar da bikin gadan-gadan. Babu abinda take ji sai faduwar gaba a duk sanda ta tuna abinda yake tunkaro ta, suna nan zaune aka fara kiran amarya da ango su fito fili. Murmushi ya sakar mata ya miko mata hannu, ta kalle shi a tsorace, ya sake sakar mata murmushin sannan ya kama hannun nata ya mikar da ita, suka shiga takawa zuwa filin tamkar tsofaffin masoyan da suka jima da kaunar junan su.
   Sun jima a filin shi da abokan sa na ta tikar rawa, taji jiri kamar zai debe ta, ta daure kanta na k’asa amma tayi matukar gajiya, yana ankare da ita yana sane kuma suka cigaaba da abinda suke, sai da ta gama gajiya likis sannan suka koma suka zauna, ta  kalle bangaren da su Hidaya suke, suka hada ido ta marairace fuska, tasowa suka da Rauda suka zo wajen ta, suka zauna a side dinta sai taji kamar an yaye mata dukkan damuwar ta, hira suke mata k’asa k’asa, hakan ya sakata warewa har tana murmushi, nan fa su ya Hadiza ma suka taso suka hawo wajen, daukar hoto. Tasowar yan gidan su ya sakata mantawa da shi da existence din sa a wajen, ta sake sosai har sai da mc yace ya isa haka su koma sannan suka koma amma ban da Rauda da ta rikewa hannu kam ta hanata tashi, sai kawai ta cigaba da zama a gefenta da yake akwai spare kujera a wajen.
   An dau lokaci sosai har su Ya Hadiza suka fara deciding kawai su tafi, basa son barin ta ita kadai amma dare yana yi musu sosai hakan kuma ba sabon su bane, bayan haka dukkan su da mazajen su, gashi duk ba gidan umma zasu koma ba sai gobe zasu koma. Waya Hidaya ta kira Rauda daga wajen zaman su, ta daga amma bata jin ta, sai ta mata text tace zasu tafi, suna kallo ta radawa Asma’un, nan da nan idon ta ya ciko da kwalla zatayi kuka,

“Dan Allah karku tafi.” Ta rada mata tana sake riketa

“Dare yayi sosai, zamu dawo amma in sha Allah da wuri.”

Sakin hannun tayi ta sunkuyar da kanta, tana jin tana mata sallama ta daga mata kai kawai.
   Bayan tafiyar su sai da aka kara almost an hour sannan aka tashi, wajen karfe daya na dare, Nadeeya ce ta rik’e ta suka fito harabar wajen bikin, ya karaso wajen su yace

“Kuje kawai zan zo.”

“Ok, gidan Mama ko gidan ka?” Ta tanbaye shi ta sigar zolaya. Shafa kansa yayi yana kallon Asma’un da take kallon gefe yace

“Gidanta mana, me zakuyi wa Mama a tsohon daren nan, kawai sun hadu da safe.”

Dariya Nadeeya ta saka, ta budewa Asma’un mota ta shiga, ya rankwafo kanta yace

“Get ready for me.” Yayi mata shu’umin murmushi sannan ya juya zuwa wajen da friends dinsa ke tsaye suna jiran sa, da kallo ta bi bayan sa, tana kisisiisma iya abinda yake tanadawa a ransa,tasan babu batun sassauci a tattare dashi, ita kuma tayi alkawarin rik’e mutuncin ta har sai ta tabbatar da wanne irin aure akayi mata.
   Tafiya motar ta soma yi, tana cigaba da hangen sa tsaye suna ta magana da shewa, baka jiyo me suke cewa amma tabbas ko ma menene suna cikin nishadin sa, sanda motar ta fita daga harabar event centre din a lokacin ta lunshe idon ta, wasu zafafan hawaye masu dumi suka zubo mata, sai kawai ta kwantar da kanta ta rufe idon ruf tana jin duk hirar da suke a tsakanin su, wanda duk maganar yadda dinner ta kasance musu ne.
    Tafiyar da sukayi ba me yawa bace kasancewar dare ne babu cinkoson ababen hawa, tana jin motar ta tsaya tayi saurin bud’e idon ta, ta kalli gidan da yake amsa sunan gidan ta, gidan da zata zauna a ciki tayi rayuwa wadda bata san iya adadin ta ba,watakila ma sai dai a fidda gawar ta, ji tayi kamar an sake bubbuge mata kafafunta, taji kamar ta juya ta shiga gari watakila ta samu wadanda zasu fuskanci halin da take ciki, sai dai bata duk wannan damar, tana jin kuma saboda kasantuwar ta mace ce, watakila da itan namiji ce da hakan ba zata taba faruwa ba.
   Bin su ta dinga yi tamkar rakumi da akala har zuwa tsakiyar falon gidan, wanda yake fidda shihirtaccen kamshi, amma halin da take ciki ya hanata fahimtar haka, hasalima baki take ganin gidan, basu tsaya da ita ba sai da suka dangana da bedroom din ta, suka zaunar da ita a gefen gadon sannan suka zauna suma suna dan bata baki, hakan ya sakata sakin kuka wanda a da tayi alkawarin ba zatayi ba, sai a sannan ta karyata duk dauriyar ta, domin ba karamin abu bane rabuwa da iyaye ko da kuwa auren soyayya ne balle ita nata da bata ma san a wanne bigire zata ajiye shi ba. Tana jin su suka cigaba da bata baki, suna kokarin ganin ta kwantar da hankalin ta, bata daina kukan ba amma tayi k’asa da muryar ta har suka yi zaton ta riga ta daina, sukayi mata sallama suka tafi. Daga nan gidan yayi tsit babu motsin komai, tsoro ne ya soma shigar ta, ta duba wayar ta taga daya da rabi ta wuce, da sauri ta zame a wajen dan dama bata sallah, ta kudundune jikinta waje daya.  Bayan kamar minti talatin da tafiyar su, taji motsi kad’an kad’an alamun tafiya, sai kuma magana da ta kasa tantance ta waye sai da aka matso kusa sannan ta fuskanci shine yake waya, diri-diri tayi ta rasa me zatayi kuma, ta kalli kanta sai kuma ta kalli kofar, ta tashi da azama zata rufe sai dai kafin ta kai ga rufewar ya danno ya shigo, yana sakale da wayar a kunnensa cikin shigar boxer da wata riga armless, saurin ja da baya tayi ya kalle ta yayi murmushi yace

“Baby kina da matsala, na fad’a miki I’m all yours, babu ruwan aurena da alakar mu, you can see me whenever you want,kamar dai ko yaushe.”

Dariya yayi yana sake makale wayar, ya shiga ciki sosai ya zauna akan bedside yana cigaba da wayar, komawa tayi ta zauna a gefe a k’asa, har ya gama sannan taji ya taso ya nufo ta, kafin ya karaso ta mike da sauri, ya tsaya a gabanta yana kallon ta.

“Wannan kayan baki chanja su ba, nifa bana son kazanta fa.” Ya fad’a a wulakance ya kai hannu gefen wuyanta ya shafo ya kalli hannun

“Duk kin yi gumi baki san miji zai zo wajenki ki dan watsa ruwa ki saka sexy night wears ba, bansan duhun kai fa.”

Shiru tayi masa shi kansa dama ya san shirun zata masa, kuma dama ya san a hakan zai tarar da ita dan abokin sa yace haka matan hausawa suke, wai kunya sai a kawo amarya da wasu kaya masu uban nauyi ta yi ta wani nuku-nuku a ciki, shi sam baya son ire-iren wadannan al’adun malam bahaushen wanda suke cike da kauyanci da gidadanci.
   Cigaba da bin ta da kallo yayi, zai sake magana aka kuma kiran sa, ya kalli wayar kamar zai daga sai kawai ya fasa ya kashe ta gaba daya ya cillar da ita a saman gadon, sannan ya fizgota zuwa jikinsa ya matse ta.

“Me kika zo dashi?” Ya rada mata a kunne yana zame dankwalin kanta.

“Ina fatan dai sun shirya ki sosai da sosai, bana son matsala ko kad’an, kin gane me nake nufi.”

Bata gane abinda yake nufi ba dan duk a kidime take, yana ta jujjuya hannun sa a jikinta ya na zagaye da ita, har ya kai bakin gadon, ya hankada ta baya sannan ya bita yayi mata rumfa, da sauri tace

“Bana sallah.”

Kamar be ji ba, sai kuma ya tsaya chak yana kallon ta, kallon neman karin bayani, da girgiza masa kai alamar eh da gaske take, wani irin mikewa yayi da sauri yana ja baya, kamar yaga abun kyankyami, ya fice daga dakin, mikewa tayi ta dauki mayafin ta, ta yafa a tsorace kamar wadda tayi gudu saboda yadda ta rude.
   Be jima da fita ba sai gashi ya dawo, rik’e da wasu kaya masu yawa, ya watsa mata a fuskar sa sannan yace

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button