Rayuwar Mace
RAYUWAR MACE 6
“Ki goge min kayan nan tas kafin naje na dawo, tunda baki da amfani kika kuma karya min lissafi baki isa ki kwana haka ba wallahi.”
Kaya ne masu yawa nasa jeans jeans da tshirts, su yake so ta goge da wannan uban daren,
“Ba zakiyi ba?” Yace yana zare mata ido, bata amsa ba. Ya matso sai jin saukar mari tayi da ya kusan sakata sakin fitsari a wajen.
“Wayyo Allah na!” Tace a karon farko tun shigowar ta gidan,sake matsowa ta ga yayi, da sauri ta hau kwasar kayan tana kuka
“Stupid, tunda baki da amfani sai dai kiyi min aiki.”
Ya juya yana tsaki, ya shiga dialing number Fido dan ba zai iya asarar daren ba!