Rayuwar Mace

RAYUWAR MACE 7

“Alfarma nake nema asma’u, ga yayanki nan Adam, dan Allah asma’u ki taimaka min, Adam ya dawo cikin nutsuwar sa, kiyi kokari wajen jawo Adam jikin ki, dan Allah ki yi kokari wajen ganin ya bar dukkan abubuwan da suke mara kyau, Adam yana son ki zaki iya amfani da soyayyar da yake miki ki dawo dashi kan gaskiya, babu me iya yi min wannan alfarmar sai ki, kiyi hakuri ki danne duk abinda zai biyo baya, a karshe zamu ci riba, kinji? Dan Allah.

A duk maganganun Mama babu daya da ya tsaya mata a rai wanda dama bata sani ba face wai Adam yana son ta, wai Adam yana son ta. Ta tabbata a kaf duniyar nan babu wacca Adam ya tsana sama da ita, da za’a bashi bindiga ace ya harbe mutum daya ta tabbata ita ce, haka take itama a wajenta, tana jin tsanar sa sosai a zuciyar ta, tsanar da bata taba yiwa wani mahaluki ba, bata son ganin ko da fuskar sa ce, dan ta gama tabbatar da rashin imanin sa, bashi da kirki lamba daya, ta yaya ake tunanin zata iya gyara shi, bayan shi a ganin sa babu wani abu da yake mara kyau? Bayan ba dauke ta a matsayin mutum me daraja ba? Tana ji Maman ta cigaba da magiya, ta amsa mata da kai dan bata san kuma me zata ce mata ba, ba zata taba fahimtar ta ba, tunda ta riga ta saka son kai a cikin al’amarin auren masu, wanda ta tabbata tayi hakan ne saboda personal interest dinta, ba wai dan alakar ta da abban su ba, ba kuma wai dan soyayyar da take ikirarin Adam din nayi mata ba.
Fitowa sukayi in da suka bar su, ta koma kusa da su Nadeeya ta rabe tana jin hirar da suke, kiran sallar magriba ya tashe su daga wajen, ta bi bayan su Nadeeya zuwa daki, sukayi sallah tana zaune a gefen gado suka idar, sai suka cigaba da zama a dakin suna hirar karatu. Mama ce ta aiko ta zo, ta fito ta ganshi a tsaye ya jingina da bangon falon.

“Bishi kuje asma’u, zaa aiko muku da abinci wai Ashe tun da ya fita be koma gidan ba.”

Murmushin yake tayi, gabanta ya hau dukan uku uku, yayi mata alamar su je yana nuna mata hanya, ta shiga gaban sa ya take mata baya yana murmushin mugunta.

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button