RAYUWAR MACE 9
“Menene haka Lion?”
“Me kika gani?” Yace yana zama a inda Asma’un ta tashi. “
“Baka ga me kayi ba?”
Tace cike da kulewa
” Me nayi?” Ya dage mata gira yana baje hannayen sa a saman kujerar
“Menene na wani riko ta kamar irin kayi missing din nan nata.”
“Missing? Ni nace miki haka? Warning kawai nake so nayi mata, baki tsaya kin ga komai ba amma har kin yanke hukunci.”
“, Shikenan.” Tace tana zama a kusa dashi, ta kwantar da kanta a kan kirjin sa, ya juyar da fuskar sa dayan side din sabon tunani na bijiro masa.
Dafe kirjin ta, tayi bayan ta shigo daki tayi gaggawr sakala key ta kulle sannan ta zauna tana maida numfashi, macen da ya shigo da ita ta dinga hasasowa a idon ta, lallai Adam ya shahara, tunda har zai iya kawo mace gidan auren sa, ba tare da fargaba ko dar ba. Bata damu ba, idan ma dari zai kawo matsalar sa ce, ba zata dai yadda kuma ta sake hada jiki dashi ba.
Saman taji sun hawo, suna kyalkyala dariya cikin yanayin da ta hasaso a ranta, dakin sa suka shiga gami da murzawa kofar key, shiru bata sake jin motsin su ba.. ishirwa taji tana ji, ta manta bata hawo da ruwan ba na saman ya kare, tashi tayi ta sallalaba ta fita xuwa kitchen din kasan, ta dauko ruwan kenan yana shigowa kitchen din, yi tayi kamar bata ganshi ta, tayi kokarin rab’awa ta gefe zata fita ya tare hanyar yana bin ta da kallo.
“Zan wuce!” Tace a dake
“Ba zaki wuce ba!” Yace yana matsowa
“Sauri nake please ka matsa.”
“Anki a matsa din, saboda Sis ta hure miki kunne shine har kike da bakin fad’a min magana, wai tsaya ma, baki san nayi tafiya ba? Baki san ki duba mutum yana nan ko baya nan ba, kin fiso ma idan bana nan ko?”
Wani banbarakwai taji maganar tasa, ta kalle shi a kaikace ta sake kokarin rabawa zata wuce ya kamata ya hada jikin sa da nata, ta fizge da karfin gaske, ruwan ya fadi kasa tayi ficewar ta, ta barshi tsaye cike da takaicin abinda tayi masa, lallai ma yarinyar nan, sai kuwa ya koya mata hankali dan yaga kamar ta manta waye Adam, ko dan taga kamar ya sakko yana mata magana a nutse, tsaki ya ja mayen kamshin turaren ta da ya cika kitchen din ya shigar masa har makoshi, sink ya nufa ya kuskure bakin sa sannan ya dau ruwan ya fito.