Uncategorized

RAYUWAR NAJWA COMPLETE

 *PAGE* *1*~*2*

*Garin* yayi duhu sosai kasancewar hadari ya had’u ga wani irin iska mai k’arfi da akeyi, wata kyakyawar yarinya na hango sai sauri ta keyi sai dai tana tafiya ne tana d’ingisawa, burin ta d’aya shine ta isa gida kafin ruwan sama ya sauko, cikin ikon Allah har ta isa gida ruwan bai sauko ba. tana shiga  sai ga *INNA* nan ina ta hau ta da masifa kamar zata cinye ta d’anye, wannan yarinyan sai kuka ta keyi kawai. 

Cikin kuka tace” Dan Allah kiyi hak’uri INNA wallahi yau banyi ciniki ba”

Cikin masifa Inna tace” Yau naga y’ar banza kina nufin yau ma kinyi min kwantai da Awara, to wallahi ba zai yiwu ba”

Nan Inna ta d’auko wani k’aton ice tayi kan yarinyan nan da shi, ganin haka yasa yarinyan ta ruga wani d’an d’aki da gudu tana d’ingisawa nan Inna ta bita ta fara dukan ta da wannan icen, Allah sarki yarinyan sai ihu ta keyi. dan kanta Inna ta gaji da dukan ta ta k’yale ta. 

Haka yarinyan nan mai suna *UMMI* tayi ta kuka dan duktaji ciwo a jikin ta, a haka har tayi barci.

Washegari da safe da missalin k’arfe shida Ummi na kwance tana barci sai ji tayi an watsa mata ruwa. a firgice ta tashi,Inna ta gani rik’e da bokiti tana cewa” Uban wa zaiyi miki aiki kin kwanta sai barci kike ni tashi kije ki d’ebo ruwa kuma kiyo icce yanzun nan”

Tana karkarwan sanyi ta tashi ta d’auki bokiti ta nufa rafi nan ta d’ebo ruwa sannan tayo icce,bayan nan tace ma Inna” na gama”

Inna dake gaban murhu tana suyan k’osai tace” to d’auki bokitin koko ki tafi talla”

Tsayawa tayi ba tare da ta d’auka ba nan Inna tace” mene ne kin wani tsaya min a kai?”

Cikin rawar baki tace” Dan Allah Inna yunwa nake ji”

Da masifa tace” to maya in ban baki ba cinye ni zakiyi” nan ta bata wani koko na jiya har yayi tsami, 

Da sauri Ummi ta karb’a hannun ta na rawa tsabar yunwa nan ta hau sha tana gama shanyewa sai amai dan rabon ta da abinci tun shekaran jiya. tana gamawa ta wanke bakin ta sannan ta d’auki tallan ta fita tana d’ingisawa.

Ba ita ta dawo ba sai wurin sha biyu na rana dan takan jima ba’a siya nata ba. tana shigowa Inna ta hau ta da masifa sannan ta bata alallen gwangwani guda d’aya taci. tana gamawa ta shiga d’akin da take kwana wanda ba komai sai buhun kayan ta dan ko siminti babu a d’akin sai k’asa, nan ta shirya cikin riga da wando da farin hijab na makaranta. 

Tana fitowa Inna tace” ke ke tsaya ba inda zaki sai kinyi wanke-wanke wato ke mai son karatu ko to wuce maza ki cire kayan”

Cikin hawaye tace” Inna kiyi hak’uri inje wallahi nayi lati kuma malamin zai min duka”

Wani rangwashi tayi mata a kai mai shegen zafi da sauri Ummi ta aje jakan buhun ta ta fara wanke-wanken.

Wani mutum ne ya fito daga d’akin shi yace” yau naga y’ar banza uban mai ya hana ki aikin tuntuni wai ke a dole mai son makaranta “

Inna tace” Ashe kana jina da ita?”

Yace” Eh ai ni wallahi yaya Auwalu ya cuce ni da ya tafiya bar min wannan abar”

Ita dai Ummi na jin su tayi shiru kawai.

Bayan kwana biyu Ummi na cikin yin tatan kamu sai ga wata yarinya wace ba zata wuce sa’ar Ummi ba. ta watsa mata wasu tsoman kaya tace” ke wanke min kaya na dan biki zani anjima saura kuma kar su fita da kyau haha yarinya zan lakad’a miki na jaki wallahi”

 “Uban wa zaiyi miki wanki?” wani saurayi ya fad’a haka yayin da ya shigo gidan.

Turo baki tayi wanda yaji jambaki har ya wuce bakin tace” *YUSUFA* kana takura min fa”

Da gudu ya bita nan ta shige d’akin Inna tana ihu ai da sauri ina ta dakatar da shi ta fito tsakar gida tana cewa” kai wani irin wawa ne har sai yaushe zaka bar goyon bayan yarinyan nan?”

Cikin zuciya yace” ba zan daina ba Inna dan ni banga abin da tayi muku ba da baku son ta”

Inna tace”Eh d’in ba mu son ta ka fita a ido na fa Yusufa karka manta da kai da *LANTANA* uwa d’aya uba d’aya kuke amma sai ka so wancan matsiyaciyar to ka kiyaye ni”

Cikin haushi ya kalla wanda aka kira Lantana yace” ni dai da ita da *UMMINA* na d’auke su k’anne nane ba wani banbanci”

Habawa ai nan ran Inna ya b’aci ta shiga massifa tana zagin Ummi shi dai Yusufa fita yayi a gidan. Ummi ba abin da take sai share hawaye.

 ******   ******

*Asalin* Ummi, malam Auwalu shine sunan mahaifin ta daga shi sai k’anin shi iyyayen shi suka haifa tun tasowan su sun sama tarbiya mai kyau har zuwa lokacin da suka girma  inda su keyin noma kasancewar mahaifin su ba shi da hali sosai. sunan k’anin Auwal Rabi’u. 

Lokacin da suka kai munzalin aure, baban su yace su fito da mata nan Rabi’u ya had’u da wata yarinya sunan ta LARAI(Inna) nan akayi auren su sai dai Auwal bai sama wace yake so ba sai bayan shekara biyu lokacin har Larai matar Rabi’u ta haifa d’a namiji mai suna Yusuf, nan ne Auwal ya had’u da wata wace yake so acan wani k’auye. yarinyar kyakyawa sunan ta AISHA tun bayan auren Aisha Auwal yake d’an samun arzik’i da gonar shi dan shi Rabi’u yasa wasa bai damu da aiki ba a wannan lokacin ne mahaifin su ya rasu bayan wata uku mahaifiyar su ita ma ta rasu. a gaskiya sun ga tashin hankali dan mutuwar ya shige su.

Tun bayan auren Auwal da Aisha har yau Allah bai ba su haihuwa ba. sai dai suyi ta addu’a , rana d’aya kwatsam dai Aisha ta sama ciki habawa ai ba k’aramin farin ciki suka yi ba nan ta cigaba da rainon cikin ta.

Lokacin da Larai taji Aisha na da ciki tayi bak’in ciki sosai dan ta tsane ta ba kad’an ba.ga shi a wannan lokacin ne Rabi’u ya had’u da mugayen abokai nan suka sa mai son kud’in yayan shi tunda shi ba shi da shi. aiko haka yazo yana ma yayan na shi hassada dan ko gidan shi bai zuwa da yake gidan su ba d’aya ba, shi ko Auwal bai san meke faruwa ba.

Bayan wata tara Aisha ta haifa yarinyan ta kyakyawa inda akasa mata suna UMMI. tunda aka haifa Ummi yaron Rabi’u yake son ta haka Yusuf zai zo gidan ya zauna dan yana son Ummi sai dai iyyayen shi basa so amma ba yanda za suyi.

A wannan lokacin Larai ta haihu ta sama mace aka sa mata suna Lantana tsakanin ta da Ummi shekara d’aya ne.

Ummi na da shekara bakwai iyyayen ta suka rasu sakamakon gobara da ya kama a gidan ba’asan ta ina wutan ya fito ba cikin dare abin ya faru dayake ranar sun je har k’auyen su Aisha to Ummi tace ita sai ta zauna acan nan suka bar ta dan suna son yarinyan sosai.

Kasancewar yarinya ce Ummi ba ta da wayau nan akayi sadakan bakwai da iyyayen Aisha suka tashi tafiya da ita ai nan Rabi’u yace bai yarda ba shi zai rik’e yarinyan dan’uwan shi ba dan sun so ba suka bar ta sai dan ba yanda za suyi. haka Ummi ta fara rayuwa dasu Larai(Inna) da Rabi’u(Kawu) a hankali ta gano ba iyyayen ta har ta fahimci sun rasu dan wani zuwa da kakan ta tayi ta fad’a mata.

Kawu ya dawo gidan baban Ummi da zama duk ya gaje dukiyan shi dalilin da yasa yace sai anbar mai Ummi kenan.

Haka Ummi ta fara rayuwan k’unci da takura a wurin Inna lokacin tana da shekara goma Inna taje gurin boka tace tana son a kasara ma Ummi rayuwa domin yarinyan Allah yayi ta kyakyawa samari na son ta dan gaskiya tana da kyau kamar ita tayi kan ta wai dan tana

 k’arama ma kenan ina ga kuma ta girma. nan boka yace ma Inna mai take son ayi ma yarinyan tace kawai so take a nak’asa mata rayuwa domin yarinyan ta lantana bata da kyau kowa Ummi yake so.  nan boka yayi asiri ya turama Ummi aljanu suka rik’e k’afan wanda bata tafiya da kyau tana tafiya tana d’ingisawa ne. kowa yayi mamaki yarinya kyakyawa amma tana da nak’asa a k’afa. lokacin da kakan ta taji tazo dan ta d’auke ta sai dai Kawu da Inna sun hana dan sun san magani zatayi mata. haka nan ta hak’ura ta tafi tana kukan tausayin Ummi.

A yanzu shekaran Ummi goma shabiyar kyan ta sai fitowa fili yake duk da kasancewar ta mai kasara a k’afa ba k’aramin son ta Yusuf yake ba shiyasa yake kiran ta da *UMMI NA* wanda Inna na jin haushin sunan. suna gana mata azaba iri-iri dan ba ko da yaushe Yusuf ke gida ba dan son da iyyayen shi suka nuna mai ya b’ata shi dan yana bin masu shaye shayen nan tun bai sha har ya fara sha sai dai baya sata da neman mata sai dai yasha kwaya ya bugu yazo yana musu layi a gida sai ya kwana biyu baya gidan sai dai yana kula da Ummi dan wani lokacin saboda shi ake raga mata. tana zuwa

 makarantan boko da allo dan shi ya dage sai Kawu ya sata. ita kan ta Ummi tana son yayan nata Yusuf dan tana jin dad’in yanda yake kula da ita…

DOWNLOAD HERE

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button