Uncategorized

SALON SO BOOK 1 PAGE 13-14

 ????????????????????????????????????????            ???? SALON SO ????

????????????????????????????????????????

    BOOK ONE ????

Story & written by

Mommyn fareesa

   ????️13&14

“Ahankali ta turo k’ofar ta shiga da sallama”yana zaune kan kujera yana zare safar k’afarsa”bayan yagama k’arewa parlourn kallo”da nufin da dare yaduba CTV camera yaga kota masa bincike….yana wannan tunanin yasmeen ta shigo”had’e fuska yyi ya amsa sallamar ta adak’ile”duk’awa tayi tace”.sannu da zuwa!bana buk’ata!

      me yahana tunda nashigo gidan kimun sai yanzun kika gadama?kayi hak’uri insha Allah bazan koma yimaka sannu da zuwan ba”maimaita mun abinda kikace”yafad’a yana binta da wani irin kallo”tayi k’asa da kanta”ki wucemun dg nan”in bacin gulma meye abin kiwani kama biyoni”idan ban kiraniba karki koma zuwa min” dallah malama kikoma kicigaba da abinda kikeyi yafad’a atsawace….uffan yasmeen batace ba”saidai harga Allah tafara gajiya da wulak’anci mutumin nan”hawaye duk sun wanke mata fuska ta mik’e tsaye”K“kukqn munafurci zaki mun”salon baby tayi zaton namiki wani abu ko?zonan ki share hawayenki”banza yasmeen ta masa”da sauri ta yi bakin k’ofar…..

Ke kin isa ina tsayar dake kina tafiya”

yafad’a yana dira agabanta”batasan tasowar saba saidai taganshi”

Cikin shasshekar kuka tace”.nafasa yimaka aikin”sbd bazan iya jure cin fuska da wulakanci ba”zanmayar maka da kud’in ka”

neman halak nakeyi a k’ark’ashinka ba maula nazoba balle ka wulak’antani… tafad’a hawaye na wanke mata fuska”tajuya masa baya”

Kingama burgar??to bari kiji”yin aiki aguna dolene agareki dakiso dakarki so”idan kuwa kikak’i zuwa wlh gaba d’aya family naki kinjamusu”rufeku  zanyi gaba d’aya”(yamata k’arya sbd yatsoratar da ita)

Duk abinda zakamana Allah yafika”

Kiwuce muje ki wanke fuskarki kibarmun parlour”idan kuwa kink’i adole zanjaki natafi dake ki wanke fuskar”

Yafad’a yana tunkarota”atsorace ta d’ago kanta tana kallon sa taga meye zaiyi?

ganin yana nufota fuskarsa tamau babu annuri”saurin yin baya tayi”ido cikin ido tace”.dan Allah kayi hak’uri zanje na wanke fuskar….

Tsaki yaja,kafin yace”.marar kunyar k’arya”zaki wuce kishiga ki wanke ina jiranki ko kuwa?

ni ai gida zantafi kasaka amayar dani har 3ta wuce”

banza yamata yana k’ok’arin komawa yazauna”

badan tasoba ta wuce bed room d’in sa atsorace ta wanke fuskarta atoilet nasa ta fito”

Tana murd’a k’ofar da nufin ta fita”shikuma yana k’okarin shigowa”da sauri tayi wuf ta fito ,har jikinta na gugar nasa”

K!kalleni muga idanuwanki yafad’a cikin cool voice”

batare data kallesaba ta ware idanuwanta”

tab’e baki yyi kafin yace”gobe k’arfe nawa zakixo?”

Kamar yadda nazo ayau”last warning karki koma zuwa min anan kimun kuka”kinji kobaki jiba?

Atakure tace naji”bece komaiba ya wuce cikin bed room d’in”

Itakuma ta sake daidaita fuskarta ta fita dg parlourn”

Imaan na zaune tana kallo”yasmeen na murmushi tace”.sorry imaan”taho maza na Ida miki 3:12 pm”

Imaan dai nata kallon ta tanaso ta fahimci wani abu”

Amma sai yasmeen ta janyeta da fira”

Sharp sharp ta Ida mata sukayi sallama”

K’arfe 3:38 pm yasmeen tadawo gida”

Umma tashare d’akin ta gyara musu”Ahmed da asma’u nata salla da yunifoam ajikinsu na islamiya”

Umma tace”.harkin dawo to yaya aikin??”

Yasmeen na murmushi tace”. alhmdllh bbu damuwa komai yyi”

Masha Allah haka nakeson ji”Allah yataimaka yabada nassara”

Ameen yah Allah bara na watsa ruwa nasaka yuni foam karna makara”

ga abincinki bazaki ciba?ah ah umma ak’oshe nake naci abinci”

To madallah”yasmeen ta fice tazuba ruwa a bucket ta wuce bayi tayi wanka” 

shirin islamiya tayi bayan tagama salla ta tafi….

Da dare suna zaune ad’akin umma itadasu Ahmed suna fira”

yaro yyi sallama yace” ance yasmeen tazo inji mani driver”

yasmeen ta kalli umma tasanar mata mani driver shine yake kawota gida yamaidota”kafin tasaka hijab ta fice”

mani driver na tsaye yasmeen tamasa sallama ta gaishesa”

Ledoji manya ne guda 2 yamik’a mata”gashi inji y’allabai”yace”.akwai waya aciki da sim card”

Sosai yasmeen ke mamakin meye mr Aliyu kenufi da kawo kayan”

Amsa kawai tayi tamasa godiya ta koma gida.

Arebi’at gownt ne kala 7 da mayafansu masu kyau da tsada”

sai takalmi da hand bag kala3″

Umma nabin kayan da kallo kafin tace”.meye ma’anar kawo wa’annan kayan??

Umma dama munyi mgn dashi yace”. ba’a son saka kayanmu irinsu atamfa sai irin wa’annan a company nasu”

sainace masa banidasu ai”shine ya aikomun”

Amma gsky umma zan mayar masa da wayarsa”yacanzamun nokia”itace daidai dani”amma inani ina rik’e iphone!

wannan gsky ne yasmeen Allah yakaimu gobe d’in saiki sanar masa d’in”

Dato yasmeen ta amsa tana kwashe kayan tasaka acikin akwatinta “tayi shirin kwanciya bacci”

       washe gari 

Tun 7:45 am yasmeen tagama shirinta”tsab acikin gownt maroon colour”tayi rolling da mayafin “tasaka cover shoe’s ta rataye hand bag nata”bayan tasaka kwalin wayar da key d’in d’akin sa aciki”

dg umma har su asma’u bin yasmeen da kallo sukeyi”sbd kyawun datayi da canzawar da kayan suka saka tayi”

Umma acikin zuciyarta tana cewa ikon Allah arzik’i me b’oye muni”talauci me b’oye kyawu”

yasmeen na k’ok’arin mgn mani driver ya aiko tazo”

Sallama ta musu ta fita”

suna isowa yasmeen ta fito dg motar”hakan yyi daidai da karasowar aymaan da alama wani waje zaije”

Sosai yaketa kallon yasmeen”kafin yad’an matso bayanta yana cewa y’an mata jira pls”

Juyowa tayi suka had’a ido yana binta da wani mayen kallo”murya can k’asa yace”.kece nagani jiya da safe? Eh nice”kokece mai aikin yaya Aliyu? Eh nice”tana fad’in hakan tayi gaba bata tsaya jin mezai koma cewa ba”

Ab’angaren mr Aliyu ko nace MAI NASSARA!

Bayan tafiyar yasmeen ya kunna TV ta saitin CTV camera yaga tun farkon fara aikinta har zuwa fitarta da kallon da aymaan yadinga binta dashi”

be mata wata mummunar fahimtaba zaidai k’ara bincikarta”sbd  bazai yi saurin yadda da itaba farar d’aya”

da dare da kansa yaje yyi shopping yabawa mani driver yace”.yakaimata”

yana tsaye gaban dressing mirror yana taje suman kansa”yaji motsinta a parlour”

yasmeen kuwa fara k’okarin gyara parlourn tayi”aranta tana yaba kirkin daddy”sbd yanzun taganshi a parlour tare da anty amarya ta gaishesu”

daddy ya amsa cike da kulawa”anty tasanar masa matsayin yasmeen agidan”tana kallon yasmeen da mamakin kayan jikin ta”bacin jiya ba haka tazoba”

Sosai yasmeen jikinta yabata anty amarya munafukace”

k’amshin turarensa data shak’a yatabbatar mata da cewa yashigo cikin parlourn”

da sauri ta rusuna har k’asa”cikin sanyin murya tace”.ina kwana?”

Idanuwansa akanta yana kallon dress d’in ta yace”.lfy! atak’aice yana nufar dining area”

Hand bag nata ta d’auka ta ciro kwalin wayar ta nufi dining area d’in”

gabanta nata fad’uwa sbd batasan wane kalar rashin mutunci zai mataba idan ta mayar masa da wayarsa”

Tun kafin ta k’araso yace”.ke zoki had’amun tea”

Dato ta amsa ta janye kujera ta tsaya tafara k’ok’arin had’a masa tea d’in”

yad’an fi rabin cup tea d’in, sbd gudun masifarsa kar yace beyiba”

Ke inbacin k’auyan ci irin naki meye abin kiwani had’amun da yawa haka”

batace komaiba ta turo gabansa”

batare daya kalletaba yace”.sauran kayan breakfast d’in kina jiran sainace kiyi serving nawa?

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *


The reCAPTCHA verification period has expired. Please reload the page.

Back to top button