Uncategorized

SALON SO BOOK 1 PAGE 21-22

 

????????????????????????????????????????            ???? SALON SO ????

????????????????????????????????????????

    BOOK ONE ????

Story & written by

Mommyn fareesa

   ????️21&22

“Ab’angaren su anty amarya kuwa”tasan tabbas aymaan ya aikata abinda akace”taji kuma haushi akan b’ata mata plane da yyi”domin adalilin

hakan daddy zaik’i bashi auren imaan nan gaba”sannan ayanzun haka tanaso tasaka yasmeen ta mata wani aiki”gameda mr Aliyu”boka yabata magani ta zuba a abinci ko abin sha”indai yaci to shima zai dawo sai yadda tayi dashi”wannan dalilan suka saka anty amarya tadinga rantse rantse akan aymaan be aikataba”gashi tsoronta guda ace yabar gidan”idan kuwa tagama da Aliyu magana ta k’are….Azaune anty amarya take gefen daddy”tanata kissa da kukan munafurci”

Ita adole sharri akayiwa aymaan”be aikata laifin ba”jinta kawai daddy keyi bece komaiba…

Daddy na k’ok’arin mgn mr Aliyu yashigo cikin parlourn”

Atake ya murtuke fuskarsa sbd ganin anty amarya”duk’awa yyi yace”.daddy barka da safiya!kasancewar sun gaisa d’azun da asuba”

yauwa my son! munyi mgn da DPO yanxun”za’a bada beling nasa kayi hak’uri umarni nabaka”

Kasa cewa komai mr Aliyu yyi sbd b’acin ran dayakeji”bazai tab’a musu da mahaifinsa ba”yasan duk makircin anty amarya ne”

    Amma zai nuna mata ikonsa agidan ubansa”

Anty amarya kuwa ta kud’urci niyar da burinta yacika akan mr Aliyu zata kori yasmeen dg gidan da company d’in….

Daddy babu komai Allah yashiryesa”amma maganar zaman sa anan gidan yak’are gsky daddy….

Baki bud’e anty amarya ke kallon mr Aliyu, tanajin kamar ta d’auki wuk’a ta dab’a masa”sbd yadda takejin zafinsa”babban bak’in cikinta yadda yake nuna mata halin ko in kula bbu ruwanshi da ita”sai ajima mgn bata had’asu ba”shima sai idan itace tamasa mgn…..babu damuwa Aliyu hakan bazai gagaraba”muryar daddy ta katsewa anty amarya tunani…..tamkar zatayi mgn”amma sbd wani mummunan tunani datayi yasaka tafasa”saima cewa tayi,babu komai alh saiya koma gidan mu da zama ai..  

Daddy dai bece komaiba”mr Aliyu yatashi tsaye yayiwa daddy sallama beko kalli position d’in da anty amarya takeba”

ransa ab’ace ya wuce sashensa ya shirya cikin suit bak’ak’e”sunyi mugun karb’an jikinsa”da haska farar fatarsa”saidai fuskarsa bbu annuri ko kad’an”sbd daddy zai saka afito da aymaan…

Fitowa yyi dg bed room d’in sa”yaci karo da yasmeen na k’ok’arin ta shiga”azatonta ma ko baya nan”

Cikin rashin sa’a suka had’a ido”wata uwar harara yabanko mata”

Tab’e baki tayi tana kauda kanta”aranta tace”. lallai yau a company za’a yi kora”

Kingama shiryawa kobaki gadamar gama shiryawaba?”bed room d’in ka zan gyara”kafin kagama break fast d’in na idar”

Tsaki yaja afusace yace”.meyasa wai kin rainani ne?

mamaki ita yasmeen ma yake bata”irin yadda yake mata iko da gadara k’oshi yayan tane sai haka”

Itama fuskarta bbu walwala tace”.niban raina kaba”katambayeni nabaka amsa shine rainin??”

Bansaniba! yafad’a yana fita dg cikin parlourn”afili tace”.kodai yanada aljannune”sbd ad’azun tagansa fuskarsa asake”yanzun kuma yanata had’e rai da cin magani….

Da wannan tunanin ta gyara masa bed room and toilet ta fito”

doguwar riga ce ta lace bubu brown&black! ajikinta ta yane kanta da mayafi brown.

Koda ta fito main parlour taga bayanan”imaan kuwa dama tun7:30am tatafi skul”

rufe k’ofar sashensa tayi”tafice dg main parlourn sbd masu aiki na gyarashi”

Fitowa tayi dg cikin gidan”taduba get” mani driver baya nan”

wayarta ta d’auka ta lalubo number d’in mr Aliyu”dukda dai basu tab’a yin wayaba”tadai ajiye number d’in ne tsaran lalura”

“sau biyar tana kira ba’a d’agawa”ganin tanada 300 a hand bag nata ta wuce waje ta hau adaidaita”

gabanta nata fad’uwa suka iso company d’in”bayan ta sallami me adaidaita d’in ta wuce ciki”

A first floor ta had’u da salim”yana ganin ta yasaki murmushi”

Ranki yadad’e dama zakizone?saida nayi zaton gsky baki zoba”

Aikuwa nazo salim”ina kwana?

Lafiya qlau”amma gsky yau both kora kawai yakeyi bbu d’aga k’afa”

gaban yasmeen yafad’i”aranta tace”. nasan za’a rina”suna tafiya tace”. subahanallahi!!

Kedai bari kawai amma kisaka baki k’ila amayar dasu”

ni awa dazan saka baki?”tafad’a tana murmushi suna isowa alast floor”

ni wai hjy yasmeen banida ko number d’in ki,balle adin….shiru salim yyi sbd hango mr Aliyu yanufosu “yana jifar salim da wani irin mugun kallo”

Fuskarsa bbu annuri ko kad’an”yasmeen da kewa tayi,dukda ta tsorata” ta daure fuska taci gaba da tafowa”harta iso gab dash”

K“ biyoni a office!dato ta amsa”salim yyi k’asa da kansa”jikinsa na kirma”yana adduar Allah yasa kar akoresa”

Last warning dazan koma ganinka ka tsayar da mace a gurin nan ko wacece”

I’m sorry both!!banza yamasa ya wuce office d’in”

yasmeen na tsaye tana jiran yasauke mata kwandon masifa”

buga k’ofar yyi da k’arfi,bayan yaturo yashigo”kafin cikin fad’a yana kallon ta yace”.last warning nawa dake na k’arshe”karki koma tsayamun anan gurin kina firan banza”

Kije kiyi yadda Kika gadama”idan awajene be dameniba”aiki kikazo yi ba soyayya ba”

nifa yaya Aliyu ba saurayina bane”rufemun baki”kin ganni kin gimtse fuska”

Amma kinata washema wani banza baki ko?”

Amma yaya Aliyu nima ai idan kaganni had’e rai kakeyi ko?yanzun dai ba wannan ba”sannu da aiki”nagama d’azun nasamu kayi tafiyarka”

Kirik’e sannunki banaso!and last nan gurin ba dandalin fira bane”

zaki jamasa dake kanki wlh”yafad’a yana jan kujera yazauna”

Allah yabaka hak’uri”ga ruwa kasha dan Allah”tafad’a tana matsowa gun table d’in tafara k’ok’arin tsiyaya mishi ruwan”

banaso!bazan shaba kifice kibani waje kitafi gun salim tunda shine kikeyiwa aiki”

Ajiye cup d’in tayi batace komaiba”taje ta zauna kan wata kujera tayi tagumi”

kallonta yyi ta gefen ido”yaga tana kuka”

 zonan!! yafad’a cikin cool voice”

meye zanzo namaka tunda bakason ganina??”tak’arasa zancen tana sakin kuka”

meyasa kuka bemiki wahala ne?nabaki 3 minit ki goge fuskarki kizo nan”

batace komaiba ta goge hawayenta”ahankali ta taso tazo gaban kujerarsa ta duk’a”

meyasa kikayi kuka?”yanzun dan Allah yaya Aliyu meye laifina anan?”kanata mun fad’a akan abinda ban aikataba”nakuma baka hak’uri”nabaka ruwa kak’i sha kace nafita….yazanyi da raina?”

kansa yad’ago ya d’auki cup d’in ruwan yashanye”kafin ya ajiye cup d’in”

nasha shikenan?”turo baki tayi tace”.ai bakace ka hak’ura ba”

Eh”idan kin kiyaye anan gaba zan hak’ura”yanzun kitashi ki zauna”kinmayi break fast?

Eh nayi”tafad’a tana jan kujera ta zauna”loptop nasa yaturo mata”Kinga wa’annan bayanan?

Eh nagani”okay copy zakiyimun yanzun”anjima zamuje meeting gurin 12:00pm”

To shikenan Allah yakaimu”tafad’a tana jawo loptop d’in”

Amma kamar angyara office d’in nan ko? Eh cleaners sun gyara”yafad’a atak’aice yana  jingina jikinsa da kujerar ya lumshe ido….

Ajere suke tafiya gwanin burgewa da sha’awa”zaka d’auka masoyane”

yasmeen na d’auke da breaf case nasa”da hand bag nata”suka wuce d’akin meeting d’in”

Daddy da sauran jama’a duk suna zaune”sosai daddy keta kallonsu har mr Aliyu yazauna”

Bayan angabatar da kammala meeting d’in”yasmeen na zaune can k’arshe tanata tunanin duniya”kawai taji ankama hannunta guda”

Da sauri ta d’ago kanta suka had’a ido da mr Aliyu”taga bbu kowa ad’akin meeting d’in sai su”

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button