Uncategorized

MATAR UBA 24

Ad

_____

💦💦💦💦💦💦💦     *MATAR UBA*

💦💦💦💦💦💦💦💦

Daga Alkalamin ✍️

      

       *Milly*

                   Fadilah Yakub

                 *(MILHAAT)*

*🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️*

                   *M. W. A*

 *Bismillahir Rahmanir Rahim*

Ad

 “`Not Edited

CHAPTER 24“`

Hashim da already yaji Labarin mutuwar Mahaifin Nasa yayi saurin dawowa gida daga gidan su faisal, shigowar sa Kenan yaji news din da take ji, Kan ya nufi ta harta yanke jiki ta fad’i.

💦💦💦💦💦💦💦💦

……….. Cikin muryar kuka yake Kiran sunan ta, ‘dagata yayi ya d’aura kanta akan cinyar sa yana “Fad’in Mummy!! Mummy!!! Dan Allah ki tashi Innalillahi wa Inna ilaihirraji’un” Talatu Yar aikin gidan najin ihun ta ta fito parlor da gudu a gigice take ambaton “Innalillahi na shiga uku” hannu ta d’aura akai ta durkusa a gaban su cikin kuka Tace “Dan Allah mu kaita asibiti” Bai ce komai ba ya d’aga yayi waje ita ko da gudun ta ta bud’e Masa sit na baya, Mai gadi na ganin halin da ake ciki yayi saurin bud’e katafaren gate na gidan, Kai tsaye sai FMC suka nufa a Emergency room aka Kai ta, Nan da Nan likitoci sukayi kanta, ba dad’e wa suka fito.

Likita nufu Hashim yayi dake ta safa da marwa kasa kuka ma yayi don shi Bai ma San kukan Rashin mahaifinsa zaiyi ba ko Kuma halin da mahaifiyar sai take ciki ba, ‘dan dafa shi yayi yace “Hashim” d’aga jajayen idanun sa yayi Yana kallon sa ba tare da yace komai ba ya d’aura da fad’in “kayi hakuri Hashim da Rashin da akayi maka, duk mai Rai mamacine” Murmushi yayi ganin irin kallon da Hashim ke masa, yace “mamaki kake yanda akayi na San ka ko?” Kai ya d’aga Masa alamun Eh, murmushin gefen Baki yayi yace “ka daina mamaki Hashim Ahmad shettima, familyn ku ai ba ‘boyayye bane a garin gombe” kirkirarren Murmushi yayi yace ” Hakane”

“Labarin rasuwar Mahaifin ka ya karad’a gari,lungu da sako babba da yaro, Ka kwantar da hankalin ka kayi musu addu’a”

A zabure ya mike yace “ban gane ba Dr? Kamarya na musu addu’a? Ban fahimce ka ba?”

“Am sorry ka kwantar da hankalin ka, mahaifiyar ka lafiyan ta kalau?”

“To meyasa ta yanke jiki ta fad’i?”

“Suma tayi ssbida firgice,sannan jinin ta ya hau Amma yanzu ya sauka don yanzu ma bacci take….” Kasa karasa Maganar da yake yi yayi jiyo murya kuka sukayi daga waje, hashim na juyowa ya hango Fadeelah na kuka jab’e jab’e kallon ta suka tsayi harta karaso inda suke Hashim kasa magana yayi dai hawaye wiwiwi, sai yaji tausayin ta ya kamashi ga tsohon ciki a tattare da ita haihuwa ko yau ko gobe, ganin Hashim na zub da hawaye Kai a langwab’e tace “Shikenan ita ma mutu ko?” Ganin ya kauda kansa ta Fara rera sabon kuka, Dr yace “Babu abinda ya same ta ki shiga d’aki tana ciki” yana Maganar Yana nuna Mata d’akin da take da yar yatsa.

Da saurin gaske ta nufi d’akin,wani Kara ta yi Mai uban sauti hannu tasa ta rike cikin ta, ihu ta Kuma yi a Karo na biyu Duk su biyun suka nufe ta da gudu,Dr ganin jini na sauka a kafarta ya Fara Kiran “Nurse!!! Nurse!!!” Da gudu nurses guda biyu suka nufu cikin murya Mai ‘dan Karfi yace “Je ki d’auko wheel chair” ‘dayar ta koma da gudu,Hashim kasa magana yayi,yayinda Fadeelah sai aikin Kuka take tana kukan cikin ta.

Labour room aka kaita, sanadiyar tsorata da tayi nakuda ta tashi Mata tun a gida Amma,zafin rashin Mahaifin ta ya hanata Jin zafin nakudan, Tasha wahala sosai Kan ta haihu,ta haifi d’anta Wanda yaci sunan Daddy Wanda ake Kira da Adnan,sun shiga jimami sosai mummy Kuma sai da tayi sati d’aya churr a kwance a gadon asibiti,da taimakon Allah da Hashim mummy da Fadeelah suka rungumi kaddara.

Tun daga wannan lokacin farin ciki da kwanciyar hankalin da ke gidan Alhj Ahmad shettima ya gushe, Fadeelah na gidan ta, mummy ce  kad’ai da Hashim a gidan sai Yan aikin gidan,tun daga lokacin da Badiyya da Hashim suka rabu a school Bai sake kulata ba ko sai d’aro zata Kira bazai d’aga hakan ne yasa yaki picking calls d’inta har sai yau da Allah yayi zai ga Masoyiyar sa wato Asiya.

CIGABAN LABARI

……..Wani irin kallo Badiyya takeyi wa Asiyah Wanda ita Kanta Bata San tanayi ba, (Niko nace Badiyya Kar a biye wa son zuciya dai,kishine ke cin ki).

Hashim na barin asibitin Kai tsaye gidan su faysal yayi, yasanar Masa da ya ga Asiyah,faysal yayi matukar farin ciki yace “Alhamdulillah Allah ba azzulumin bawan sa bane sai da Wanda ya zalunci kansa yau idan Safiyya taji cewar kaga Asiya ina ga mutuwa ce kawaii baza tayi ba”

Murmushi Hashim yayi yace “Idan ta ga dama ta had’i yi ranta I don’t care” Yana maganar had’e da d’aga kafad’a kana fuskar sa nanu Yana cikin tsananin farin ciki.

Baba Mai gadi yace “Dr mun gode sosai Allah ya saka da Alhairi”

Shiru Bata ce komai ba,alamun suna nuna hankalin ta Sam baya jikinta ta,Nana dake kusa da ita ne ta dafe kafad’ar ta Tace “Likita lafiya kuwa? Ana Miki magana Baki ji ba?”

A ‘dan razane Tace “Na’am Na’am”

Baba Mai gadi ya Kuma maimaita abinda yace kirkirarren Murmushi tayi tace “Kar ka dumu baba,ai Asiya Tamkar kanwa take a gareni,so kaga ai yi wa Kaine”

Murmushi yayi yace “Hakane Hakane”

Khamal yace (Baban Yesmin) “Dr yanzu ya samu sauki ko za a iya sallamar mu?”

“Eh za a iya bari na dubo likitar dake kula dashi” tana Kai Nan ta fice.

Ad

_____

1 2 3 4Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button