SALONSO 35-36

????????????????????????????????????????
???? SALON SO ????
????????????????????????????????????????
BOOK ONE ????
Story & written by
Mommyn fareesa
????️35&36
tamkar imaan tafad’i matsayin yasmeen agidan”amma sanin halin jidda na zata iya gayawa yasmeen bak’ar magana kota goranta mata….hakan yasa kata cewa”girl friend d’in sace”kuma itace sakatariyarsa a office…. tab’e baki jidda tayi ranta ab’ace tace”.shine zai mareni akanta?”wlh bazai yuyuba”tana fad’in hakan tajuya da sauri tabar parlourn”
kaitsaye sashen daddy jidda ta wuce”kasancewar week end ne shima yana gida”
yana zaune a parlourn sa suna fira da anty amarya jidda ta shigo parlourn tana kuka”
Tamkar anty amarya tarufeta da duka taji”sbd tatsani duk wani dangin Alh yarab’i gidan”
daddy nabinta da kallon mamaki yace”.lafiya jidda meke faruwa ne??”
wai daddy zuwana kenan gun yaya Aliyu nasamesa da wata mace suna kissing juna”shine nace masa hakan bbu kyau”
Kawai yadinga gayamun bak’ar magana yamareni”sannan yakoreni”
Hmmm ! Alh gashidai kaji da kunnan ka ko?”amma anyiwa aymaan sharri”ance yayi k’ok’arin haike mata”
cewar anty amarya tana hura hanci”
Cikin fushi daddy yace”.ya isheki haka samira!mekike nufi ne?”nasan irin tarbiyyar dana bawa d’ana”ke kuma jidda tashi kibani waje zan je nabin cika”idan nagano kin mun k’arya abinda zai biyo baya bazakiji da dad’i ba”
Cikin kissa anty amarya tace”. Allah yabaka hak’uri alh”amma ai bani nace ba fad’a akayi ko?”
Uffan daddy bekoma cewa ba”jidda ta tashi ta fice gabanta nata fad’uwa”sbd makircin data had’a be yuyuba”
Tana fitowa tayi waje da nufin taje ta zugo mahaifiyarta”
Daddy kuwa tashi yyi yawuce bed room d’in sa da nufin yakira mr Aliyu ta waya”
Anty amarya tace”ayanzun yaka mata k’udurina yacika akanka Aliyu”mussammun sbd wannan mgn da jidda tayi”idan be yuyuba yanzun nan gaba kad’an zai yuyu….tana fad’in hakan itama tabar parlourn…..
yasmeen naganin jidda ta fita”fuskarta bbu walwala tace”.wacece wannan yarinyar??”
meyasa kike son sani?”bazaka fad’amun ba?”Eh”
bata koma cewa komai ba tabar gurin”
Parlourn tafara k’ok’arin gyarawa”yyinda mr Aliyu tunaninsa yakasu kashi2″b’angare guda na umartarsa da yaje yasanar wa yasmeen matsayin jidda kada yasmeen tayi fushi”
gefe guda na zuciyarsa na sanar masa yashareta itad’in me?wacece ita da takai matsayin tamaka irin wannan tambayar?”
barin dining area d’in yyi bece komaiba yafice dg parlourn”
yasmeen tana gama gyara parlourn takoma bed room d’in sa”
D’akin imaan yanufa sbd jikinsa yabashi anan jidda zataje taji labarin wacece yasmeen??”
Tun kafin imaan tamasa mgn fuskarsa bbu walwala yace”.amsar me kika bawa jidda akan yasmeen??”
Kasancewar imaan bata iya k’aryaba tasanar masa”yana k’okarin mgn wayarsa tayi ringing”yana dubawa yaga daddy ne”
Cike da girmama yad’auka”daddy yace”.yasameshi a parlourn sa”
yana kashe wayar yafice dg d’akin imaan”
ya wuce sashen daddy yana tunanin me jidda taje tasanar masa?”
Daddy na zaune a parlourn sa”mr Aliyu yashigo yasamu guri yazauna”
Daddy yasanar masa abinda jidda tafad’a”mr Aliyu beyi mamakiba”bbu alamar nuna razana yace”.daddy k’arya takeyi”yasmeen yarinya ce me tarbiya data dace da mahaifiya ta gari”
banida burin b’ata rayuwar wata”nima inada k’anwa mace”bazan so hakan yafaru da itaba”kasan irin tarbiyyar daka bani daddy”
Hakane kam Aliyu”nikaina nasan k’arya jidda keyi”nasan kishi taji tunda tana sonka”amma maganar gsky yakamata kafito da mata kayi aure”nikaina nafiso ka auri bare ba auren zumunci ba”
Insha Allah daddy nima banida ra’ayinsa”
Anty amarya dake lab’e tana sauraron komai azuciyar ta tace”.tabbas ayau zan k’aryata manufarka Alh akan d’anka…..
sosai mr Aliyu suka tattauna da daddy sannan yabaro parlourn”duk wani tunaninsa nakan yasmeen”
sashensu ya wuce yasamesu itada imaan zaune suna kitso”
yasmeen na ganinsa ta had’e rai”wanda ita kanta tarasa meyasata yin hakan”
zama yyi akan kujera yana satar kallon ta”
rasa mezaice mata yyi”
can yace”.nan da awa nawa zaku gama kitson?”tamkar yasmeen tamasa banza tadai daure bayan yacire rai dajin maganarta tace”.awa d’aya!
okay yafad’a yana kallon imaan dake rintse idanuwanta”baby da zafine? bud’e idanuwanta imaan tayi tace”ah ah yaya”
tashi tsaye yyi ya wuce bed room d’in sa yakwanta bacci”
Sai 2:15 pm yatashi”da sauri ya wuce toilet yyi alwalla sbd ganin har azahar tayi tana neman ta wuce ma”
2:30 pm daidai yashigo parlourn”dining area ya wuce”yabud’e warmer’s”
Tuwon semonvita ne da miyar kuka” taji daddawa da kifi anda gargajesa aciki”
yabud’e wata warmer yaga soyayyan naman rago ga zob’o drink”
Rufe komai yyi yabar parlourn”sbd yasan wayayi girkin”yasandai imaan bata tab’a masa tuwoba”
Imaan ce kawai a cikin parlourn tana chats sai smiling take ita d’aya”
Baby ina yasmeen?waye yyi girkin can?”
Anty yasmeen ce tayisa”tana bed room d’ina bacci takeyi”
taci abinci?”ah ah”jeki tasomun ita”
Dato imaan ta amsa ta tashi ta wuce bed room d’in ta”
babu jumawa imaan tadawo tana dariya tace”.wlh yaya tak’i tashi balle tazo”
nagama kamar fushi takeyi dakai ai”becewa imaan komai ba yatashi ya wuce bed room d’in”
yasmeen na kwance agefen damarta”ta rufe jikinta da hijab”baby face nata kawai ake gani”
motsin murd’o k’ofar taji”azatonta imaan ce”tak’i bud’e idanuwanta”
gefen bed d’in yamatsa yad’auki robar ruwan dake kan bed side drower”
yarfo mata ruwan yyi afuskarta”imaan wai meye haka?”kije kice masa nace bazan zoba”yasmeen ta fad’a tana bud’e idanuwanta……tsab acikin na mr Aliyu”murmushi yasakar mata wanda yafito masa da kyawunsa da kwarjininsa”
d’auke kanta tayi tana turo baki”cikin gunguni tace”.ni ina ruwana dakai ne?kaje gurin jiddan mana”
menene kikace?”yafad’a yana tsareta da fararen idanuwansa”
Kinga kitashi muje muyi lunch”kin mun tuwo”abinda bana ci”sbd haka dole kicinyesa duka yarinya”oya tashi muje kona d’aukekine??”
zaro ido tayi tana saurin tashi zaune”nidai kaje ganinan zuwa”
Kingama fushin ne?” Hmmm namefa?” naganin jidda”
Kamar yadda ka hanani kula kowa idan muna tare”kaima ai adalcine kak’i kula mace idan muna tare”
Tamkar yace”.amatsayinki nawa?”amma sai yashare”kinga kitashi muje inajin yunwa ne”
batace komaiba ta sauka dg kan bed d’in yana tsaye yana kallon tulin uban gashin kanta”dayake zargin attached ne”
ke wai attached kike sakawa kome??”Allah yakiyayemun”nikadaina kallemun gashi”
gashi ko attached?”bant d’in dake kan ta tacire ta girgiza kanta “atake gashinta yasauka agadon bayanta….
da ido kawai mr Aliyu kebinta”yana mamakin dama anasamun hausawa da irin wannan gashin?”ka yarda nawane?”tafad’a tana maida bant nata”kafin tayafa mayafin”
yaushe zamuje amiki gyaran gashin to?”nafasa ai”meyasa?ga jidda can kaje ka kaita”
yasmeen kin rainani ko?idan Kika koma yimun zancen ta wlh zanb’ata miki rai”yana fad’in hakan yajuya yafice”
Tab’e baki tayi tabiyosa”imaan dai nazaune tana kallonsa yazo yawuce parlourn sa,har yasmeen itama tazo ta wuce”
Afili tace”., Allah yasa yaya kuzama miji da mata kaida anty yasmeen”kilama soyayya sukeyi nice banganeba”tafad’a ita kad’ai tana murmushi”