SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

yace “Sha shashah kawai ashe baki da hankali gambo?
Allah wadar dake Mu sam bama bukatar irin ku anan garin bakar ashana kawai….
Sarki yace tabbasss , gambo kin nuna mana bamu isa dake ba kuma baza mu iya zama da tsagerun irin ki ba.
Tunda kuwa kin ce sarati bazata bada hakuri ba ai addini ya mana hukunci wanda suka aikata zina sabida haka ranka shi dade tunda saukin da ka musu bai mata ba
Ayi ma yarinyar nan hukuncin ta kawai kowa ya huta
Anan ma aka kusa aka kawo dorina
Aka shimfida ni da karfi da yaji aka kwaso sageer aka mana bulala 100 100 chifff chif
“ni kam Har Sumewa nayi tsaban kuka da azaban da nake ji ajiki na cahn da na kuma farfadowa ummma nagani a kaina tana kukan mai dauke da tashin zuciya…gaba daya ta sauya min kamannin ta kamar ba ita din ba
Worst part awajen in ka dubi fuska kusan kowa babu mai jin tausayin mu sai ma tsana da tirrr dake bayyane a fuskan su karara
Sarki yace toh ke kuma gambo
Daga yau na yanke miki hukuncin barin Garin nan ta kofar yammma, kar na sake ji ko nasake ganin Ki daga nan har yankuna biyar da garin nan
Na haramce ki da kasar nan kiyi nesa damu chan kuje bariki Bakin halin ku shi zai kashe ku..
Guda aka rangada aka shiga tafi ana shewa..
Sarki da mukaraban sa na barin waje aka ma na eeele ni da ummah aka sa mu agaba har hanyar kofar yammma bamu dauki komai namu ba haka muka fice daga garin kurwala.
Ga dare yayi ga bakin ciki ga yunwa ga radadin takaici gashi da kyar ummah ke ja na bulalan da aka min har yanzu na damu na ga danyen ciki ajiki na..
Tafiya kawai muke yi mu biyin mu babu hutawa.
tun muna kukan har muka dena kowa yana ji da abunda ke ransa..
Da kyar muka kai zauren wasu yan uwa fulani..
Matar gidan ita ta taimaka mana da ruwa ganin yadda muka galabaita anan ummah roka mana sarari muka zauna muka huta don kuwa akwai tafiya sosai agaban mu kafin mu kai wani gari….
“sai da na dan huta na dada jin yadda Ciki na ke min ciwo amma bana ma so na ji tsaban yanayin dana tsinci kaina na kuncin rayuwa…
Ummah kam tayi shiru kamar bata tuna komai…
Cahn Tace saratu? Inaga fa zan dan nemi kudi anan yankin saboda kinga yanayin ki baza mu iya jure tafiya da kafa ba gashi bansan ina zamuje ba..
Nace ummah kudi kuma ta yaya zaki samu anan?
Tace “Ke dai bari mana ki gani naga kamar akwai aiki wajen wancan bafulatanin tayi min nuni da shi wani manomi ne sosai ana kan hidiman masa dure a buhuhunan sa ..
Nace to ummah ..nima zan taya ki
Ta girgiza min kai alaman ah a na huta kawai nan ta mike tabisa wajen su..
Cikin hikima da dabara irin nata ta cire kasala da gajiya ta hau aikin ma bafulatnain nan kamar bakar jaka..
shikan sa sai da ya sha mamaki..
Buhuhu na 15 da rabi na sabon gyero umma ta samu ta dura masa kafin nan an aneman goma saura na dare sai layi da haki take idanun ta sunyi jajir dan wahala..
A hakan ma bata daddara ba duk da ma ummah na da saurin sabo amma anan ba wanda ya san meke faruwa da mu tace ma matar gidan insha Allahu washe gari zamu tafi idan aka biya ta..
Anan muka kwana bata mana rowan abinci ba kuwa,muka sauke gajiya cikin daren har da wanka….
Washe gari ban tashi ba tsaban yadda nake ji da tsamin tsamin duka ajiki na ga laulayin ciki da kananun ciwon mara.
Umma kam tuni ta bi layin karbo kudin aiki…
Dubu10 kacal ta samu
A haka ma ji tayi kamar an tsoma ta a Aljanna
Ta zo ta daga ni tace maza ki shirya yanzu zamu tafi kar azo agan mu anan yankin saura mana yanki 2 mubar kurwala….yi da jikin ki saratu..
Nace toh umma na mike adaddafe na shirya ..
Fura mai kyau ummah ta siya dukan mu uka sha harda matan gidan..
Umma ta bata hakura ta bata dari biyar daga kudin aikin ta.
Daga nan muka fece….
Tafiya muke, duk da haka ba Abun hawa
Ciwon ciki na sai dada tsanantawa yake ga waje da nisa gari biyu zamu wuce amma ko rabin daya bamuyi ba ..
Tun ina boye ma ummah abun da nake ji har na soma wash washhh…
Anan ta riko nj niki niki tana mun sannu sannu in mun danyi nisa sai mu zauna bakin inuwa mu huta
Idan naji dama dama sai mu wuce
Har muka fice gari na biyu muka shiga na karshe..
Ido na yayi ja sosai, tsaban azaban danake ji aciki na..umma tace ki daure saratu ba abun hawa ne da sai na daura ki kije tashan mass kki jira ni,
Amma babu kiyi hakuri kinji..?
Anan na dan soma zub da hawaye na sosai..nace babu komai ummah amma cikin nan ne sosai yake murda ni..
Cikin damuwa ummah tace kiyi hakuri saratu nasan dole zaki ji wahala bari muyi sauri mu samu mota sai ki huta…ko zaki ci wani abun ne yanzu?
Na ce mata ah”ah
Nana Ta cigaba da lallabani muka soma tafiya..
tausayin umma ya sanyaya min zuciya ta naga kamar tama mance da kanta a kuncin rayuwa da bakin cikin da aka cusa mata ni kawai take kulawa
Dalilin haka yasa Nima sai na tursasa zuciya na na dage duk da abunda nake ji har muka kai tasha muka shiga motar haya
wanda dama ya rage guda daya ne tall shine na zuwa kano..
Ba yadda muka iya anan din muka tsakuro
akan balance ma na zauna nikam don Ancika makil shine mota a yau din na karshe kuma ba halin jiran wani…
Dadin Abun dai an rage mana ana kudi ne dan adubu 2 da dari 2 aka kaimu har kano
Bamu da isa ba sai wajen karfe 8 saura na dare..
Kowa ya fita a motar amma nikam na ma kasa dago kaina tsaban ciwon Ciki ga dumin jini da yake yawo a cikin jikin na ta ciki ina ji…
Umma ne ta daddafe ta jawo ni a hankali na fito..
Ganin yadda jin ke bina yasa hankalin ta ya tashi sosai….
” a gurguje ta sama min waje ta ajiye ni kar mutane su fara lura da halin da muke ciki ga shi a kanon ma ta baya muke wani local govmnt ta cahn wajen kumbotso bamu ko shigo gari karara ba
Kuka nake yi a hankali ena wayo Allah wayyo Allah ciki na ..zan mutu…ummmah..uhmmm
Mmmm numfashi na ke sama sama , a duk lokacin dana motsa kuma jini ke fita daga jiki na.
Nan Nayi lugwi ina nishi Ban sake ganin umma ba sai da wata yar dattijuwa tace gata nan baiwar Allah wannan ne yata ce”
Ki taimaka min dan Allah bata da lpya ne
Kare min Kallo matar tayi taga inayi kamar mai shirin dauke numfashi na ina wssshhh ita kanta tasan bana jin dadi
A take Matar tace to muje mana..
Umma ta rike ni muka kama hanyar isa gidan matan wanda bai da wani nisa da tasha.
Sunan ta sahura bazaura ce wacce bazata wuce 35-37yrs ba
Anan gidan ta dakuna biyu ne amma babu komai aciki sai tabarma da katifa sai dan ghna na kayan sawa.
Umma ta shimfida ni akasa tana cewa nagode baiwar Allah ko kinsan inda zan hada murhu na sami ruwan zafi?
Wani irin kallo ta mana Tace “Ah a, malama nifa kawai taimaka miki nayi ku sami wajen kwana amma ba ruwa na da wani abun ki..
Umma ta marairaice tace kiyi hakuri nima tambaya kawai nayi yata zan dan kimtsa ki taimake ni..
Batace komai ba Tayi ma umma nuni da wani murhu wanda daga gani ankai kusan Shekaru biyi ba adaura komai akai ba..
nan umma ta je waje ta shiga tattaro karare da duk abunda zata samu ta hada min ruwan zafi wanda ya sa ta
Ta kai 2 hrs sannan ta kammala..
Anan kafin ta zo na sume ya kai sau hudu tsaban azaban lalurin ciwon cikin …
“Saratu? Saratu… sai naji kamar a mafarki ummah na kira acikin layi na bude idon kamar wance ke sjirin shekewa lahira na amsa da naaamm ummmah..ummah mutuwa zanyi ki taimake ni ummah ciki na ciki na ummah….