HAUSA NOVELSAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Suna ta kiran sa har yanzu shiru gashi 10 ya wuce har ana neman sha daya da rabi na dare.

Shikuwa ko da ya taso ya dago motar sa zai je gida ya same sarah da maganan

Dan jingina kansa da yayi yana jiran trafic anan ya sume baya ko motsawa..

wani asibiti daban aka kaisa emrgency wayar sa is off ga security

Sai washe gari da safe da kyar aka samu expert ya bude sai ga sakon sarah ya shigo..

Anan kuma hajiya billy taga safiya yayi bata ji motsi daga wajen mahfud ba
jira take yace mata ya aikata hakan
Gashi saura 2hrs daga 18hrs din nan
ganin danta yana dab da barin duniya ta soma kawowa ko mahfud ya rudeta ne ya bar kasar da matar sa ..

anan kirar ta ya hana na sarah shiga ita ta soma jin labarin halin da yake ciki da inda aka ajiye..

a hujajn ta kama hanya saura awa biyu daga lokacin da likita yace yazeed zai mutu.

ko da aka fada ma sarahn halin da yake ciki ba jira itama ta haura kan hanya antyn ma bata sani ba sai da tayi nisa ta tura mata sakon da suna asibiti.. Ita dama ko bacci batayi ba anty warda ke hanata daga hanakli sosai da suga bai dawo jiyan ba.

Isar hajiya billy ke da wuya ta same sa maimakon ta kawo jimanim datake ji aranta ganin sa hakan sai ta fara rokon sa ya tashi ya sake sarahn kar danta ya mutu..

A birkice sarahn ta taho da nurse zasu dakin da mahfud yake amma jin muryan hajya bilky ya sa ta dakata

Yanzu kam Abun ya ishe ta,ya kai kuma kaita makura itama sai idanun ta gaba daya suka rufe ko karasawa batayi ba ta juya a zuciye ta bar asibiitin

ko lura da wulgawar alhaj nafiu batayi ba,amma shi ya ganta kuma ya gane ta sosai abun ya basa mamaki

da safen nan jirgin sa ya sauko sai yaje asibitin da yazeed yake anan ake sanar masa da cewa ai mahfud ma ya kwnta hjy billy tana wajen sa.

Sai yanzu anty warda taga sakon itama hankali tashe ta kama hanyar asibitin

Sarah kuwa taka kan motar tayo aguje zuwa dakin da aka ajiye yazeed ba wanda ya lura da yanayin da ta shigo..

rufe kofar tayi gam gashi dama observation room ne private

Wani irn wukkantacce kallo ta baisa da shi tace

da dai ka tozarta ni da uwata kace tayi karuwanci sabida ta tarbiyantar da yarta ta hanya mai kyau…

Yau sai gashi kaima kayi kwatance da ita ma duniya kuma akan son abunda ta tarbiyantar da karuwancin nata zaka mutu don bazaka taba samu ba

Yazeed Kayi asarar duniya …..domin kuwa ban taba ganin uwa muguwa marar imani,tabbabiya kamar naka ba….

Ashe Gwara mahaifiyar tayi sabin Allah amma tana da imani bata da mugun zuciya da rashin tsoron Allah kamar uwar ka.

Allah ya sawwake uwa irin naka Mai shegen son zuciya..

Sabida taji laifin nawa uwar har da kora ni bani da tarbiya ko?to yau ninan sarah bukar lingard zan koya mata ladabi da tarbiya kamar yadda take ji tana koyar da wasu..
Ta hanyar da harta mutu bazata mance ba.

“Hannu ta sa ta zare socket din wayar computer dake reading Eline dinsa ta watsar kasa

sai ta dawo kan oxygen pipe din ta kama shima ta zare tayi firo da su..

Hes critical so ko minti uku baiyi ba ya fara jan numfashin sa sama sama kamar yana cire ransa na karshe …it was hard for him to breath again da karfin iyawar sa yake tattalin nunfashin sa..

ta tsaya tana duban sa tace”ban taba burin na kashe mutum ba amma yau kai zaka fara mutuwa kafin uwar ka ta kashe min mijina.

idan bata da hankali nima bani da shi … inyaso a hada mu ni da ita akaimu gidan mahaukata tare..

aure na da mahfud yafi karfin sadaukarwa ma banza irin ka bare kuma rayuwar sa….

Nan Ta juya ta fice abun ta.

 

*Nasan bazan samu daman gode ma kowa da kowa ta hanyar kiran suna ba,idan baku mance ba labarin littafin true life ne kuma gashi mun kawo kusa da shafi na Karshe,so i wanna use this medium to thnk alll e grops in media da suke karantawa suke coments wasu ma ina cikin su basu sani ba,Nagode nagode sosai i cannot repay ur kindness so jazakklhu khairan peeps,u can folow and vote my acct both instagram and wattpd@surayyahms*

 

????
[2/24, 14:40] SURAYYAHMS????: *????RILLlANT WRITERS ASSO????*
{ _pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers_ }
™jan2019
????????
*SAMARIN SHAHO*
_The scorned_
????????
*#lovestory:#destiny@fault#purefic#thriller:#romance,any resembelance of life or story shud be considered as a coincedence i give no permission for copy or comparison#copycat*
_A true sensational story_
*VOTE STORY AND FOLLOW WATTPAD@ SURAYYAHMS*

 

_52 LAST PAGE_

Mahfud bai ko motsa ba haka itama hajiya billy bata dena jijijjga sa tana fade faden ya tashi ya aiwatar da abunda ta sa shi ba..
har alhj nafiu ya shigo bata sani ba sai zuba take agaban mahfud tana tona makanta asiri

Shock ya hana sa motsawa ji yake kamar an shafe masa kwalkwawa da jin wannan kalaman ta nata…
Ohh ashe shiyasa yaga sarah dazun kenan mahfud ne ya auri sarah? Amma meyasa zata ce ya sake matar sa sabida yazeed kar ya mutu shin me hadin yazeed da sarah again?
Sai da ya gama kawo wannan in quick flsh sannan yayi gyaran murya tare da cewa bilkisu?

A birkice ta dago tana ganin sa ta mike tsaye tare da kara sautin kukan ta tace Alhj?
Alhmdullhi gwara da ka shigo alhj kace ma mahfud ya tashi ya sake sarah idan ba haka ba dan mu kwallli daya a duniy zai mutu..

Abubuwa da yawa sun daure masaa kai cikin dauriya irin na namiji ya dago ta yace ta fada masa duk abunda yake faruwa dan ya fahimci me ake ciki?

Alhaki da kamuwar Allah ya sa ta zazzage bit by bit na bakar shimfidar su da suka shirya ita da danta komai sai data warware

Wanda tamkar agaban anty warda akayi shi sabida tana dab da su a bayan alhaj tana ji.

Nan kuma alhj nafiu ya riga ya tafi duniyar tsananin mamaki da zaucewar tunani shin bilkisu ta haukace ne?
Ya tambaye kansa

Itako ta riga ta rude sai dada cusa maganan take tana cewa dan Allah kayi wani abu bana son yazed ya mutu ..shi kadai muka mallaka a duniya.
Sunkuyar da kai anty warda tayi a duk rayuwar ta batayu tsammanin zatayi fushi kamar ydda yanzu take jin abun aranta ba

Out of shock alhj ya bude baki yace bilkisu duk ke kikayi wannan abubuwan?hannun sa na rawa..

Nan ta dawo hankalin ta amma gani take ai shima bazai so ace sabida wani na daban su rasa dansu kwalli daya ba

Zata bude baki tayi magana sai tasssss ya wanka mata mari mai gigitarwa”
Cike da tsawa yace am disapointed in you bilkisu wannan wani irin banzan zuciya ne dake haka?

A hargitse tace eh banzan zuciya bakin zuciya mummunam zuciya duk ka kirani da shi amma dole ne yazeed ya tashi bazai taba mutuwa ba sabida wasu..

Hannu ya sake dagawa zai kai mata mari anty warda ta rike sa..
Sai yanzu suka san da zuwan ta..
Tace barta haka alhaj..
Alhj nafiu Bai iya cewa
Cos He was stranded in mysery jikin sa sai ya hau rawa ya juya ya kalle mahfud cikin yanayin tausayi… take zuciyan sa ya fara masa zugi a sulale ya koma akan kujera ya zauna ya dafe zuciyan sa”
Blaming kansa yake da yasan haka na faruwa da tuni ya br duk abunda yake yi ya taho… iya zaman sa da bilkisu baisan ta da haka ba..amma sai gashi yau tayi wanda ya kure masa tunani”

Gaba da gaba suka taho da anty warda she is quiet sure itace maman sa na germany sabida sunsha ganin juna a video callz.

tana shiru tana kallon anty warda wacce haushi ke cinta amma sai ta rike sa ta soma magana in stern amd disguistful mood.
Tace sannu hajiya,mun gode da kulawar ki ashe maganganun danake ji akan zamn ku da mahfud gaskiya ne?
Nan hjya billy ta dago azuciye zata maida martani anty warda ta dakatar da ita da cewa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button