SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Rigijib ummah tayi agaba na duk da bana iya bude idanuna da kyau na tsinkayo bakar tashin hankalin dake tattare da ita “tace sannu saratu, sannu kinji ,bazaki mutu ba ina tare dake bari naje na tsaftace ki ko zaki ji dai dai..
Ta daga ni riki riki mukayi bayi..anan ta sullebeni ta shiga wanke ni tana matse min ruwan aciki na jinin nan kuwa kamar ana zazzago shi ne,
Ummah tuni ta fahimci cikin ne ya lalace amma bata tabbatar ba..
Haka ta min jinya da dabara irin na su na yan kauye tasss na dawo da dan gwabi sai jiri da rashin karfin jiki danake ji
Dan kwalin ta ta bani na daura da shike ya kaini gwiwa sai ta dan yage
mayafin ta tayi min nadi nasa tsakanin cinya na na tare jini..
Fes ta wanke kaya na ta shanya a haka ma bata dawo dakin ba sai da ta fita tayi yawon neman chemist ta siya min maganin ciwon ciki ibrufen da paracetamol ta hado da shayi mai dan yaji yaji hadin kasuwa da bredi daga wajen mai sai dawa ta zo da shi..
Sam na kasa hana kaina kuka sosai nake yi cikin tsumayi da tsananin bakin ciki..
gashi bana jin karfi sam sam ajiki na
Ummah ita kanta sai da tayi shiru ta zuba min ido..
tace “Wato ke saratu magana baya wucewa wajen ki ko? Kina gani dai baki da lpya
Har yaushe zaki cigaba sa damun kan ki akan abunda yanzu ya zama tarihi?
Ki ci abincin nan kawai bana son shashanci
“Nikam ina sai kukan kawai nake yi mai ban tausayi.
Abun ya ishe ta zata sake magana nace
Ummah…”wallhy ke nake tausayawa ke nake tunawa ummah kina shan wahala da hakkin da bana ki ba Allah zai saka miki ummah…
Nan itama ta taro hawayen ta sai yanzu ta gano ashe tausayin ta wai nake ji abun yana damu na…
Nan ma bata lallaba ni ta hau bambani
Ke saratu ni bana son Shasahan ci kici abinci kawai ki rabu da komai ai ya wuce …
Nikam ai mahaifiyar ki ne duk duniya babu abunda nake takama da shi in ba ke ba raina naki ne saratu akanki zan iya mutuwa ma ba wahala ba
kar kisa aranki wahala muke yi abunda ya kamata nayi miki kwanan nan..
Ko kina da wanda zai miki ne?
Cikin kuka na gyada kai alaman ah’a nan ne ta shiga lallabani har na samu naci abincin…
Ciki na yayi kauri ya dau dumin shayin sai muka kwanta bacciii
Chan dare yayi nisa na farka sakamakon tsanantawa da ciwon ciki na ya dawo
Umma na hange agafe tnaa bacci agajiye har gwarti ke deban ta..
Sai naji bazan iya tashin ta ba kawai na cigaba da dauriya na abu na gaba gaba
Kafin safiya na suma bana ko motsi
Da safen A wargaje ummah na ke tashi na amma shiru har matan gidan wato sahura ta karaso
Ganin halin da umma take ciki na tashin hankali gani a kwance cikin jini bana ko motsi ya sa ta tsorata ta soma mata masifa
Tace nifa ..Kawai ku fita ku bar min gida na ai dama Kwana kuka ce gashi Allah ya kawo mu safiya …
Maza maza kufice nikam ban isa ba da wannan fitinan ba..
“ummah tace emmm Baiwar Allah dan Allah kiyi hakuri ki dubi girman Allah ki barmu na same mafita ma yata nasan ciwon ta ne kawai ya tashi zan je nan na siyo magani zata farfado.
Tsoro yasa Sahura ta turje sam taji sauraron ummah har sai da ummah ta ce to ta ara mana dakin zata bata kudin na san wani lokaci.
Suka yi bargain akan dubu 7 da kyr ta yadda ta karbi dubu 5 ya rage mana saura dubu 1 dawani abu kacal a hannun mu
Nan Kafin ta kyale mu mukaji sarari ta tausaya bawai bata tausaya ba
Kuma ta lura umma na duk yadda akayi batayi karatun boko ba bare arabi
Ba abunda ta sani anan birni ita dai akwai wayo ne sosai
Ganin yadda umman ke jeka ka dawo daga chemist zuwa kai na ya sa ta je ma ummah..
Tace “Ai na fahimci matsalar yarki wato cikin tane fa ya zube ya kamata ki kaita asibiti a duba ta.
Umma ta ce toh”amma ina ne asibitin naku
Ko zamu iya zuwa adan duba min ita ..
Sahura ta kira wani yaron matashi shi ya kaini ni daa umma har sabitin gwamnati dake tsallekan anguwan..
Bayan wulakanci da muka sha da zagi wajen likitan su akan cewa ba akawo ni akan lokaci ba sai da abu yayi nisa anan aka bani gado aka shiga duba ni..
Bayan wasu lokuta kadan likita ya taho dakan sa ya same umma yaron nan na ne tare da Ita don sahura tace masa mu baki ne
Yace kece mahifiyar ta ko?.umma tace eh likita lpy dai ko?
Yace to lpyar kenan dai amma meyasa kukayi sakaci kuka barta tayi ta zubda jini haka?ba kisan zata iya mutuwa sanadiyar hakan bako?
ummah tace” ayi hakuri likita mu Baki ne agarin a taimaka mana tafada cikin magiya
Likita yace hmmm ku dai yi hankali nan gaba kar kisake irin wannan wasa da rayuwar mutum..
Yanzu dai sai kuyi hakuri ta rasa cikin dake tattare da ita, sannan tana bukatar wanke cikk da karin jini….
Sai ayi sauri a kawo mana ko kije chan ki biya kudin… ya mika mata list bill din dubu 15 har da yan kai…
Umma ta duba
Da kyau ta gani bata ma iya karantawa ba kuma bata ce komai ba ta juya asanyaye zata bar wajen
Likita yace malama”
zakuyi hanzari fa don rayuwar yarki na ciikin hatsari muna bukatar kayan aiki nan da 24hrs idan ba haka komai zai iya faruwa ta riga ta rasa jini da yawa…
Ummah tace to likita na ji za ‘a kawo
A lokacin kuka ne ke so ya kufce mata ga
Wani mutsumusan tashin hankali da ke yawo a zuciyan ta na jin halin da ake ce ina ciki
Tace wayyo ni fadima a ina zan samu kudin nan ”
Tafada tare da daure a hannu akai cikin tsananin Jimami..
Sosai yaron da ummah tazo da shi ya tausaya mata
Yace ya kamata muje ki duba ta tunda yanzu babu kowa a kanta
Umma tace haka ne muje..
Suka zo dakin da aka ajiye ni har ta zo ban farfado ba an dai samin ruwa ina kwance kamar mutacciya..
Hakan Ya dada karya zuciyan ummah kukan ta zage tayi mai cike da dumbin bakin ciki agaba na..
yaron nan ke bata baki har ya samu Suka fito waje…
Anan ummah ta shige neman mafita…
Tace “Ummm kana ganin ta ina ne zan fi samun aikin gaggawa wanda zai kawo min kudi ko min kankantan sa Zan iya kar kadamu..
Yaron yace “Ah a gaskiya nikam ban sani ba.
anan kuma ai kafin ki samu aiki akwai wahala gaskiya bazan boye miki ba zai yi wuya sai dai kiyi kadan kadan ana baki dai dai gwargwado rayuwan nan birni fa kamar na wani wajen bane..
Ummah tayi ajiyan zuciya bataa dadddara ba tace amma ina dai zan samu ?.
yace Eh insha Allah, kiyi nan hanyar akwai masu siyar da abinci dayawa a bakin hanya kije bazaki rasa abunyi ba ko da 500 kike samu ai arage wani aBun
Ummah tace toh angama
Sai ka rukuta min sunan nan wajen saboda kar na bata kasan da bakunta ..
Yace haka ne nan ya nemo aron takarda ya rubuta ma ummah..
Nan Ta shiga yawo cikin kasuwa neman kudin aiki kafin nan da 24hrs din ya cika..
Acikin kasuwar Tun karfe 9 saura take naman inda zasu taimake ta ma shiru saima korata da ake
wasu ma sam basu yarda da ita ba duba da yanzu ana tsoron maganan Boko haram
Sosai taga wulaknci da cin zarafi..har mari saida ta karba wajen wata kabilar igala mai siyar da tuwo sabida nacin ko zata samu abun yi amma ina..
Tun daga nan umma ke kuka tana zagaye da kafafun ta ko jin tagaji batayi ba har aka kira sallahr la’asar
Anan wajen alwala ta samu ta sa ruwan sanyi a kanta ta dada Watsekawa
Ta cigaba da tafiya” weeee wew hawaye na bin kunci ta tashin hankaliln ta bai wuce ko naira biyar bata rike a hannun ta ba gashi lokaci na dada tafiya
Tace “Ashe haka birni yake? Ashe babu masu imani a birni Shikena yanzu Sai na bar saratu ta mutu?… wayyyo Allah na na shiga ukku..in ta runtse ido ba abunda take kallo in ba ni acikin jini ina nishi ina kiran suna ta cikin wahaka ba…