HAUSA NOVELSAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Nan Ya dada fitowa da confidential card din sa ya mika mata yace wata rana idan kika waye sosai nasan zaki nemi ni ko fadima?
Allah ya bada yarmu lpya kaiwa nan ya juya ya tafi abun sa.

Ummah Duk bakin ciki ya ruda ta ta dube sa yana tafiya a sanyaye tace
Kaje nidai sakayya ta na wajen Allah.
Ta juya ta shige keke napep din,

Sai da sukayi dan nisa yake tambayar ta ena ne waje ..
Nan ne ta dawo daga duniyar ma ta bude ledar ta zaro dan takardan ta da shike duk tarkacen ta anan ya kuntsa mata ganin kudin ya sata ta sake sauke hawayen bakin ciki…

Amma wani shaidaniyar zuciya ya gaya mata meye amfanin badi babu rai ?cuta kam an riga an cuce ki, kada ki yarda kudin nan kiyi amfani da shi kawai in yaso daga yanzu kyasan yadda zakii sa rayuwar ki anan garin marasa imanin..

Anan umma har ta kawo bakin asibiti,

Idon ta sun bushe amma karya ka kalle ta baka dago tana cikin ha’ula in rayuwa ba..

Kai tsaye ta shigo tana neman likitan daya rubuta mata magani.

Lokacin Ana neman kiran magrib nam ya samu ya dube ta
Acikin kudin nan ta zare ta bashi 15 da yan kai..

Kwata kwata ya rage mata saura dubu hudu da dari biu..

Anan tayi tsayin daka ga jikin ta har yanzu ba wai ya sake ta bane don ko kimtsa kanta bata samu tayi ba,

Takaici ke dawainiya da ita tana zagaye abakin dakin aikin..

Anan aka shafi kusan awa uku ana kintsa ni..

Wannan saurayin da da chan aka hado umma da shi shi ya zo ya dauke ta suka koma gida bayan likita yayi bayanin cewa an kammala komai
Amma yace bazan tashi ba sai gobe zasu cigaba da bani magani..

Anan ne data iso gidan tayi wanka ta kintsa kanta ta biya sallolin ta ta dada kai kukan ta wajen Allah..duk dama zuciyan is full of hatred and bitterness

Sahura da dan aikan ta kuwa ba karamin Mamakin yadda umma ta samo kudi da wuri suka ji ba

Dan haka sahura ta qudiri niyyar sa ma umma ido ko zata san ya take yi jiya jiya ace ta zo kano ,kanon ma bayan gari amma har ta san yadda zatayi shige da fice ta samu kudi mai yawa..

Ranar Ummah ko bacci batayi ba Washe gari da safe
Ta mike ta shirya,
Sallama tayi ma sahura tace ni zanje asibiti..

Sahurah Tace ma ummah insha Allah zata zo itama taga jikin Nawa..
Duk dai ko zata gane wani abu game da ummah amma shiru

Nikuma tun misalim karfe 4 saura na bude ido na warau na ke jina sai dai kananan ciwon ciki da dan jini da nake yi ba sosai ba..

Koda ummah ta ganni a haka ba karamin kuka da godiyan Allah tayi azuciyan ta ba, amma sai ta kasa furta komai sai sannu sannnu take min..

Na dauka duk tausayi na ne amma gaba daya sai na soma gane cewa ummah na fama da wani bakin ciki ma musamman a yau din.

 

 

 

 

 

_Share_

 

 

*WATTPAD VOTE AND FOLLOW @SURAYYAHMS*

 

*OFFICIALCATTY????*
[2/23, 23:02] ‪+234 802 646 5734‬: *????BRILLlANT WRITERS ASSO????*
{ _pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers_ }
™jan2019
????????
*SAMARIN SHAHO*
????????
*#lovestory:#destiny@fault#purefic#thriller:#romance,any resembelance of life or story shud be considered as a coincedence i give no permission for copy or comparison#copycat*
_A true sensational story_
*VOTE STORY AND FOLLOW WATTPAD@ SURAYYAHMS*
????

_PAGE6_

Kallo na bi ummah da shi a nitse tsawon mintinu na 10 amma kamar bata ma sani ba
Duk ta bi tayi tagumi ta bata shiru cikin tunani…

Nace ummah,ummah,
A nan ta dago a dan fakaice tana goge siririn hawayen ta da ta dade tana boye wa bata iya cewa komai ba

Murya na na rawa Nace ummah lpya kuwa ?

Ummah dan Allah kar kisa komai a ranki ki dena zubar min da wannan hawayen naki
..duk da duniya ya juya mana baya bazan rusuna wajen ganin farin ciki a fuskan ki ba..

Ummah nayi alkawari kuma na dauki alwashi duk inda halak yake zan nemo shi don na sa ki farin ciki a duniya
…ummah dan Allah ki dena kuka
Anan nima kukan ya kufce min na kife kai na ina yi…..

Musamman gani danayi maganan dana ke yana dada sa ummah na shiga wani irin halin tsumayi da rudewar tunani….

Ita kam dai tana shiru
A hakan ta daure ta shiga share hawayen ta a hankali ta dawo daf da ni ta kamo hannu na…
Tace”Saratu, kiyi hakuri saratu ki yafe ni…bawai na daga hankali na bane akan rayuwa abubuwan duniya ne kawai suke bani mamaki,rayuwa da ciwo sarahtu .sai dai duk da haka insha Allahu bazan dena kula da ke ba… duka duka ke kadai nake da shi a duniyan nan, kece abun alfahari na…nan tayi ajiyan zuciya tace
Allah ya baki lpya saratu
Kar ki damu dani kinji? Duk zan warware

Cikin sheshheka na dago zan yi magana ta sake min wani murmushi mai tarin nauyin zuciya tace in har farin ciki zaki bani ki daure ki cire komai aran ki saratu, ki dauka wannnan ba yin mu bane ba son ran mu bane,qaddar mu ne. Amma tunda yanzu mun samu kan mu tunanin abunda zamu yi mu tada rayuwar mu kawai zamuyi nan gaba.kinji?

Ba yadda na iya haka Na gyada kai da kyar ina kuka mai dauke da tarin takaici ,shiru ne ya ratsa wajen ummah ta shiga shafa ni gently tana bani karfin gwiwa batare da tace komai ba..

Haka nayi kwana anan gadon asibiti sai da na dan warke sarai sannan aka sallame mu

Ba laifi dukan mu muka soma sawa ranmu ruwan sanyi musamman fannin kau da nadama da koke koke duk muka bada hankali wajen nema makan mu mafita arayuwa ,ummah bata so na kawo wani magana game da komai sai na warke amma kowa da nashi a zuciyan sa kullum sai na saka na warware.

Cikin kwanakin anty sahura ita kadai take zuwa dakin mu wani bin tare da yaron nan daya taimaka ma ummah na.

kamar dai dukan su tausayin mu suke ji sosai duk dama ita bata wani nuna mana akan fuskan ta ..

Har aka sallame mu muka dawo gidan
Anan ne zamantake wa tsakanin mu da anty sahura ya dan fara samun fahimta..

don yanzu har akan gaisa a mutunce wani bin har abinci takan kawo min tace naci
Gashi ta bani rifa da skirt ummah na ta bata zani ya zamto muna sa wanda zamu na sauyawa

Hakan muke zaman mu a bariki zaman fadi tashi, Sai dai yanzu ummah na ke bada matsala

kullum sai naga ta bace shiruuu ta zurma kanta cikin wani irin yanayin kunci da tunani amma ko da na tambaye ta sai tace babu komai…tana lissafin rayuwar mu ne kawai..

Bayan wata guda lokacin har na mike tarwal jiki na ya dada bayyana wani sirrin girma kadan sabida abubuwan da suka faru dani har nonowa da kugu na suka dan taso sosai ba yabo ba fallasa ban rame ba..
Hasken fata na ne kawai ya rago.

Babban damuwa ko ince baban matsalar mu baki daya da ni da anty sahura shine ummah..

don kuwa sosai abun umman ta keyin gaba gaba shiru shirun umma ya soma daga mana hankali..

Gashi kullum a buga buga take neman kudi bata zama amma ko da ta tafi a kullum in banda zallan wulakanci da takaici babu abunda take karba wajen mutane

Munyi fama da Rashin sa’a kamar wanda aka mana mumumman baki Cikin kwanaki da abubuwa suka tsanan ta har anty sahura ta yafe mana biyan kudin dakin da muke ciki”
Tace kawai mu zauna anan din batare da wani fargaba ba sai dai dakin namu babu ko wutar lantarki,dama daga tabarma ne sai dan tsumman kayan mu da baifi kala biyu ba

Ni kaina da na fara tunanin ko tsaban yadda ummah take cin karo da mummuman rashin sa’a da takaicin mutanen birni ya ke sa ta wani yanayi amma sam abun yaki zama sosai araina..

Nasan Dole akwai babban abunda ke cinta a rai amma taki sam ta fada mana daga ni har anty sahura..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button