SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Ana cikin wannan yanayin matsin wata
Ranar da yamma bayan ummah ta fita nima mana abun sawa a baki, Sahura ne zaune akan dakalin kofar dakin ta tana gyaran farcen ta sai ga umman ta dawo
Fuska ba yabo ba fallasa Tace sannu da dawowa gambo,
Ummah ta sauke murmushin gajiya da tunani tace yawwa mutan gidan ne a tsakar gida
Nan Ta karaso ta dan zauna kusa da ita..
Murmushi suka maida ma juna as usual sahuran ta ce yau kuma me aka samo?
Tare da sauke ajiyan zuciya ummah tace ,hmmm bari kawai ni abun ma ya soma isana akwai wahala anan sannan har yanzu ba abunda na tara na azo agani…ace kai kenan sai dai ka samu na cin yau na gobe sai ka sake fita? Kai ni dai kullum ina fada rayuwar birni babu abun gani aciki sai tarin wahala..a gajiye take maganan kamar ba ita ba
Sahura Ta tabe tace ai ke ki kaga dama gambo, na sha gaya miki ki kyale yarinyar nan taje ta nema muku wani abun ko dan aikatau din na bazata rasa ba ,gata da kyaun fuska da kuruciya ba mai ki ya bata aiki,amma kina nan tsofe tsofe kin nace saam kin sa wahala ma kanki ga yarinya tana so ta taimake ki amma kinki…
Jin sahura ta fadi hakan yasa sai da taji wani iri aranta
‘Hmmmm ummah ta sauke ajiyan zuciya.. abubuwan dayawa ke dawo mata arai
Tace sahura kenan,duk abunda nake gujewa kenan amma baki gani,wallhy bazan taba yarda yata ta fice cikin gari nan ba kam sai dai nayi ta wahalan har duniya ta nade..
Allah ya kiyaye …uhm uhm
“Nan ran sahura ya dan soma baci she juzt wonder how adamant one can be bayan ga uban wahalar data ke sha,
Tace ni fa ban ma gane miki ba ne kwata kwata gambo,ke kince baki tare da mijin ki, to na yarkin fa? Ko shima baya tare da ita ne?…to wai mijin yarkin ne kike tsoron sa da baki so taje ta nemi na kanta ta rufa muku asiri ke ki dan huta,? Shi din ina yake da zai dau nauyi ba ya barki da wahala wai shin wani rin rabuwa suka yi ne? Wannan wani irin rayuwar wahal dakai ne kike yi ne gambo?
Ummah tayi shiru tana mamakin ta yadda anty sahura ta dau abun da zafi
bisa ga dukkan alamu Sun gaji ne da damuwa da yadda take wahalar dakantan ba dare ba rana ni kuma ina zaune a gidan bana komai..
Ummah ta dan murmusa tace haba haj sahura, miyayi zafi haka?
Ke dai ki bar wannan maganan ni na daukar ma kaina hakan kuma zan cigaba da nema har na dace,maganan yata kuma wannan ai rayuwar mu ce ke dai ki ci gaba da taya mu da addu’a kamar yadda aka saba..
A fusace sahura ta mike tsaye tace bazan taya ba, haba ke kuwa baiwar Allah
Ke yanzu a kwana biyun nan da muke zama daku wani irin yarda ne ban gwada miki ba? Ko ce miki akayi a irin halin da na tsince ku akwai wanda zai bari ku zauna masa agida ne baisan ku bai san asalin ku ba amma wai har ina baki shawara kina ki?
Toh wallhy in har irin wannan zaman da zakiyi dani kenan ki tattara ina ki inaki ki bar mani gida…
Anan hankalin ummah ya tashi don bata dauki abun yayi tsamari har haka ba ga sahura sai dada hawan diri take ta shake fuskan ta sosai..
Ummahh zatayi magana sahura tace, kinga baiwar Allah ki tafi kawai ni nafasa zama da ku kuje chan na fasa karban ko sisin ku ma na yafe kuje kawai ..
Ta juya a fusace zata bar wajen cikin rudani ummah ta riko ta ” haba sahura yanzu akan wanannan maganan shine zaki ce haka dan Allah ki rufa mana asiri kiyi hakuri sahura..wallhy na yarda kin mana mutunci kinyi mana adalci fiye da yadda nazo na tarar da garin nan
Nan mah ta dan fashe da kuka, tace bansan ya zanyi bane sahura bazan taba barin yata ta fita cikin irin wayannan mutanen ba ,basu da tarbiya basu da imani gwara ni ayi ta cutar da ni da na kai yata ga halaka,..Allah ya isa tsakani na da duk wanda ya cuce ni…ta dada fashe wa da kuka mai taba zuciya…
“Ni kuma ina chan daki Da shike ana dan taba sanyi Bacci nake yi sosai tun bayan dan hirar da na taya anty sahuran so bana jin komai daga abinda suke fada.
Sahura na shiru tana jin kukan da ummah ta gurfana tana yi, a hankali ta dago ta tace haba wa gambo na san akwai
Dalilin da ya sa kike haka, nifa kika zo kika samu anan garin kuma ma abariki gidan shege da shegiya, ki dube ni da kyau nafi ki sanin halin rayuwa anan
Sai dai ban sha mamaki don kin ki ki gaya min asalin damuwar ki ba dama chan zaman duhu muke kin kasa gaya min komai akanki bare yarki. toh shikenan rike abun ki, gani gaki anan kowa zai gane ma idanun sa..sai dai ki sani duk randa tayi tsami dole zanji,kaiwa nan ta kama hanya ta shige dakin ta.
Anan ummah ta zauna tana jan hawaye,
Tana tuno da yadda cikin kwana kalilan sahura ta karbe su hannu bibbiyu cikin aminci da sauyawar hali,….
amma sam bata da burin tona sirin ta ma wani bare gane take bata yarda da kowa ba yanzun..
kuma gani take kamar in ta tada za’a tsangeme ni ko makamancin haka
Amma ganin yanayin Sahura dazin ya sa tayi tunani” wai shin meyasa ta damu dani haka ? Wai daman akwai masu tausayin mutum har haka ne anan?
Ko dan ni ma mace ce kamar ta ummah tayi tunani cikin nazari mai zurfi..
Bayan nan ta tashi ta shige daki, ta daga ni as usual labarin daya ne babu abunda ya sauya dan abunda ta kalato muka samu muka ci.
Bayan sallahr ishai muna dan hira sa ita mama sai na lura ummah bata cikin hankalin ta kawai jina take ina ta faman surutu, har sai wajen goma saura na kishingide kan tabarma nayi bacci na..
Bayan nan Ummah Waje ta fito,tasan tunda har yanzu akwai haske a dakin sahura to batayi bacci ba kenan tare da sauke ajiyan zuciya ta kama hanyar dakin sahurar….
Wajen shiru sai takun ta tunanin hukuncin data dauka aranta take yi anya abun da zanyi dai dai ne ?wani zuciyan sai yace mata muddin kina so ki cigaba da rayuwar ki dana yarki dole sai kin fuskanci kalubalen ki kin kuma sa wa ranki zaki iya da komai don cimma burin ki ..
Anan ta yi salam bakin kofa kusan minti 2 sannan sahura tace shigo daga ciki….
“Baki bude ummah ke binta da ido ganin yanayin Da ta same ta, bata iya daurewa ba tace
Sahurah? Me nake gani haka? dama kema kina shan wayannan abubuwan ne, tayi nuni da kwalaben codine da totulin akasa an sha guda da alaman zata bude dayan ne..
Sahura na shiru kuma bata sake hada ido da ummah ba, har sai da umma ta zo ta gaban ta suka fuskan ci juna ”
kafin umma tace zatayi mata magana kuka ne ya dan subuce ma sahura mai sanyi da ban mamaki…
Cikin rashin fahimta da rudani ummah ,ta zaunar da ita ta shiga rarrashin ta hade da mata wa’azin a nitse cewar bata taba tsammanin Tana shan kayan kwalba ba?
Meye damuwar ta?
Sahura dake jimami ta dau lokaci tana jan shessheka kamar wata sabuwar amarya
,hankalin umma duk ya bi ya tashi ta cigaba da lallabata tana tambayar ta..anan sahura ta dube ummah tace babu komai kawai na tuno da duniya ne….
Cikin damuwa ummah tace habawa sahura, yanzu abunda zaki ce kenan ko dan nima abunda nake fada kenan zaki rama?
Ta ce ko kadan, kawai abubuwan ne dole wata rana zaka ga wasu wayanda zasu tuna maka da naka rayuwar kuma zai maka zafi..
Ummah tace haka ne shiyass nima na zo nan
Dan nagaya miki wacece ni, na yarda da amincin ki sahura kuma na yadda cewa bazan taba iya komai da kaina ba gani ba ilimi ga kauyanci babu kuma wanda na sani anan mai hali nagari na tausayi in ba ke ba
Sahura ta dago a sanyaye ta dube ummah tace ai ciwon ya mace na ya mace ne gambo,kar ki ga wai farkon zuwan ku ban sake muku ba.amma ni tun da na ganki jiki na ya bani kina cikin wani hali bazan boye miki ba ina tausaya miki sosai ,,,