SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

anan ma kukan ya sake kufce mata cikin shessheka ta kuma cewa kuma kinsan Allah a duk sanda na ganku sai na ji kamar kuna tuno min da kaina ne da kuma halin da na shiga ciki a rayuwa adan wani lokaci…
Wannan abun shi yasa na kan sha wannan abun don na samu sauki arai na..
Ummah tace Allah sarki, sahura har akwai damuwar da tafi nawa kenan wanda har zai sa ki cutar da kanki ?
nifa a inda na fito wallhy shan kayan kwalba tamkar zunubi ne babba…
kiyi hakuri ki kwantar da hankalin ki komai na duniya mai wuce wa ne..
Baga shi yanzu kina zaman ki asiri a rufe ba
Anan ajiyan zuciya sahura tayi tace haka ne,
Don dai baki san wacece ni bane gambo, ko kina ganin akwai kwanciyar hankali ga wance ke zaune da tsinuwar iyayen ta ne?
Wani rasss ummah taji…sahura tace
Ni din na ma da kike gani daga kauye na fito, kuma ba wani karatu nayi ba,ina aji na uku a secndry aka min Auren dole bayan fyaden gangami da wasu yan shaye shaye suka min wajen tallar abinci da umma na ke daura min a tashan garin mu kowani yamma ..
Naki auren nan amma sam suka turje sai na aure shi, cewar su ai babban mutum ne ga shi da dukiya da rufin asiri.. yaya na harda min wa’azi akan na amince Ni dama Sam sam banyi karatun allon nan ba haka na amince da su..
“Gambo, nayi hakuri na zauna da miji na ..sabida ba yadda bai nuna amanan sa wa iyayen mu ba ,amma daga bisa ni kadai nasan azaban da na sha hannun sa…
Nan Ta bude ma ummah gadon Bayan ta wanda ke dauke da layi layi bakake da wasu patches suma sun dishe sunyi manyan tabo tace har yau bazan manta yadda mijina ke duka na ba, ya zage ni ya ci mutunci na,kuma yayi min gorin cewar sa ai ya sayi bakin iyaye na sun bada ni a banza…
Cikin tsananin mamaki da magiya ummah tace shine baki kai karar sa ba kin ga jikin ki kuwa sahura?
Cikin kuka tace,wani kara kuwa gambo? Ai gaskiyan shi ne basu ganin laifin sa don yana basu kudi yana musu alheri yana nuna musu ina zaman lpya da kishiyoyi na…
shiyasa kuma kullum idan na kai magana sabanin haka a gida ake ci min mutunci sosai wata rana ma har a korana ni da duka..haka nayi ta zaman kunci gashi yana da mata har biyu nice na uku
Ke Ban tashi ganin zan mutu a hannun sa ba sai da Allah ya bani ciki,miji na yayii bakin ciki sosai da na gaya maza, kuma nasha duka wajen sa har sai da na kasa tashi..
fitar sa yaje ya karbo min maganin zubda ciki ban ma san da ga ina ya samo ba kina gani kinsan ba mai kyau bane..ya jika a ruwa yace maza na shanye tasss a gaban sa ko ya kashe ni…
Wallhy baida imani gambo, haka na sha nayi ta ruwan jini anan kasa a daki na tsawon lokaci sai dai ya zo ya wuce ya barni rai na a hannun Allah,gashi matan sa basu isa su zo kusa dani ba ya hana kowa motsawa..
Washe gari Ban tashi ganin kaina ba sai akan gadon Asibiti kawata ce aminiya ta ita batayi aure ba ma itace ta kaini asibitin anan na kwana ana duba ni ..
“dana farfado da danyen jiki na na lallaba na taso na wuce gidan mu,Ko da naje da maganan nan mijina ya gama kulle nashi,kuma bayan sa suka bi sosai suka kuma tsane ni.
Ko magana ba abari nayi ba aka shiga min fada babu wanda yake so ya saurare ni ,kawu na har da min dan banzan duka cewar sa na tona musu asiri…
Duk na lura da su kowa na fadan ne da son zuciyan sa,su baba su kawu duk dan abunda suke ci ne a karkashin miji na na arziki basu so ya rabu da ni
Dana tabbatar da hakan Nima sai nayi zuciya nace bana son aure na tada bori na haukace har sai da na tunzira miji na ya sake ni a gaban kowa da kowa
Su ummah da su baba Haka Suka taru akaina suka ce na bada hakuri a sasan ta nace sam sam na kuma turje nayi zuciyan maza..
..wannan kuskukern ya sa uwata da ubana suka yi Allah ya tsine dani ..
Nayi nadama gambo amma raina ne ya baci ina ji ina gani da kuruciya ta amma zuciya ta ta soma kangare wa da rashin imani…
nasan idan na koma aure na miji na kashe ni zaiyi kuma bazai dame su ba don ba su san wani hali nake ciki ba.
tun daga ranar kowa ni abu marar kyau ya same shi sai ya laka min alhaki
Bakar Tsangwama da mummunan tsana daga iyaye da dangi ya sa na bi shawaran zuciya na na fito duniya har kika ganni anan…
Yau shekara na kusan 15 kenan Da barin gida kuma nasan ba mai sake karba na ko da na koma
Wani bin nakan nemi labarin su amma su ban taba ji ance sun nemi ni ba, ta cigaba ba kukan tana cewa to me zanyi gambo?a duk lokacin da na tuno da ni wacece sai na ji na shiga wani hali, dole na soma shan wayannan abubuwan don su sani bacci kar wata rana na mutu da bugun zuciya..
Ummah Itama Tun tuni ta ke sharben hawaye, tabbas wasu iyayeen haka suke ba ruwan su da halin da yarsu zata shiga ciki ko take ciki musamman idan miji ya zo yana musu sallah sallah ace yana da kudi kuma yana dan kyautata wa
To fah yar su bata da baki kuma ko wani laifi ko ganganci na ta ne ita kadai.
Hakuri ummah ta shiga bata da dada dan kalamai kamar wanda ta san wani abu game da addini sosai..
lafazi take na masu imani tana tausasa zuciyan sahura har ta dena kuka
Ta kuma duban ummah tace”yau zan tambaye ki tambaya na karshe gambo,
Dukkan mu bayara bane shiyasa bazan sake takura ki ki gaya min labarin ku ba,
amma na roke ki ki saukaka ma kanki da yarki ku nemi duk wani hanyar da zai taimake ki ko ma ya take don zaman birni ya sha bambam da duk kauyen da kuka fito…
Ummah tace haka ne ai na gani da kaina..sai dai labari nan ne babu dadin ji sahura kuma tsoro nake ji.
Anan itama ta baje ta bada sahura labarin mu kaf ko tunanin sahura zata iya mata karya batayi ba tsakani da Allah ta gaya mata har ranta duk abunda muka fuskan ta..
Da ita ma abunda ta furkan ta na wulakanci da tozarci awajen mutane wanda basu sani ba..
Sai dai har ila yau babu abunda yafi shiga ran ummah kamar fyaden da ssa danjuma yayi mata akan kudin jinya na..she feels really miserable about it.
“jikin sahura yayi sanyi Sosai da sosai ta ke hawaye suka sauko mata har muryan ta nakin fitowa yau ta soma jin ina ma da ba haka ta karbe mu ba tun farko,
Suka taru sukayi ta jimami da kuka suka kuma rarrashi kansu, don da ita da umma kusan sao’in juna ne shekarun su bazai wuce 35 -37 ba..
Anan ummah tace,ni fa da kike gani na sahura yanzu babu abunda yake raina illah na sami abun yi na taimaka ma kaina da yata saratu, ina burin saratu tayi makaranta ta taimaka ma rayuwan ta ko da bana raye bana burin saratu ta kare a hakan jikin jahilci rashin wayewa da wahala, kuma in Allah ya yarda sai na cimma wannan burin nawa..
Sahura tace ni kuma zan baki dukkan goyon baya gambo,
Kar ki damu da wanda zai cuce ki ko ya kece miki mutuncin ki rayuwar nan dama cude ni in cude ka ne ,saboda babu wadda zaki iya masa …
Ummah tace haka ne
Tace”gambo Idan kika tsaya zaki yi na mutunci da gaskiya har duniya ta nade bazaki kai inda kike so ba kuma zaki wahala sosai sai dai ma ince wani wahalan shi zai kashe ki…
Ummah ta kuma cewa haka ne kuwa aini na gane ma idanu na sahura akwana biyun nan da zan gaya muku bakar wulakancin da nake sha da bazaku sake bari na na fita neman kudi ba
Sahura ta dan jinjina,
Tace yawwa gambo na fara wani tunani amma bansan ko ya zaki dauek sa ba,
ummah tace ina jinki…
ta dube ummah tace Tun da kince wannan ma cucin marar imani ya baki lambar sa yakamata mu san abun yi akan sa.. Ni inaga ma Ta kan sa zamu fara